Sashe 51
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaf yan gidanmu suma sun yi bajinta matan da Mazan. Alhajimmu ya saka aka yanka mata tinkiya cikin dabobbinsa na ƙauye Baba Aminu ya taho da ita tare da kaji da zabbi shi ya sa Yallaɓai bai siya komai ba yana gefe iyayenta sun gama mata komai. Ranar saukar lahadi ce tun tara muna haraban tahfezz ɗin su Jidda. Kaf ɗin su Ya Aina sun taho Rahila ce kaɗai ba ta zo ba laulayi, Kawu Abba shi da Marwa da tsohon ciki Gimbiya tare da su Khalipa da Naja, su Maman farko da Hajiya Iya. Su Munnira da Hauwa hatta Mimisco ta zo ita da Anty Bahijja da Anty Maimuna. Kaf din su Musbahu da Adnan Muttaƙa da su Suwaiba suna wajen taro sosai Jidda ta gani sai hamdala. Yallabai na da ganawa da wasu mutanen sai daga baya yazo lokacin ma Jidda aka kira tana karatu.
Sai da na yi ƙwalla da Jidda ke karatu, y'an uwanta na ta ɗaukan ta Video cikin burgewa. Bayan sun gama karatu aka kaddamar da su sha huɗu masu sauka aka ba su allon sauka. Mun yi hotuna tun da Adnan ya kira mai hoto, ta samu kyattuka, wajen malamai Kawu a envilop ya saka mata sabbin yan 1k A wajen a matsayin shi na Uba ta rumgume shi tana masa godiya. Duk mun zo da abinci da lemuka da ruwa da abun rabo. Tantin da muka zauna ba fariya ba sai muka zama abun kallo Jidda haka ta yi ta rabon jaka da Memo da abinci ruwa da maltina haka suke rabo. Baby kaf yan ajinsu ta gayyato suka ci suka sha, daga makaranta muka dawo gida muka ya da zango muka cigaba da walimar a gida. Mazan daman daga makarantan muka rabu da su.
Mimisco har gida ta biyo ni ta ci abinci sannan ta tafi. Su Anty Bahijja sai la'asar suka tafi har Gimbiya ranar sai dare. Na aika da abincin walimar da naman da kayan Snacks da abin rabo na aika da shi Gwammaja da Ɗorayi suma su shaida. Sauran kuma duk wanda zai fita jakan sa cike da kayan walima. Rahila ma na ba da saƙo akai mata Halima ce ba ta zo ba a cewar Gimbiya ba ta da lafiya ne, amma ni ban damu ba ta kanta na ke yi ba. Ranar gidana cike da jama'a har dare ranar ba gidana Yallaɓai yake yi ba sai washegari ya dawo gidan, sannan ya ga kayattukan da Jidda ta samu sai da ya shafa kanta kafin ya ce.
"Good girl. Am so proud of you Daughter."
Ga waya ga laptop, shi Yallaɓai Tab ya siya mata sabuwa, tsohuwar ya ce ta bar ma Baby, da take ta tura baki ita ba a siya mata komai ba ya ce ta ƙara ƙoƙari itama za a siya mata. Hotuna sun yi kyau na yi ta carbi a status mutane nata saka albarka bayan kwana biyu na saka ta , ta shirya ta je Gwammaja ta kai ma Nene allon saukar ta, daga can ta wuce Ɗorayi ta kai ma su Alhajinmu suka gani suka saka albarka.
Kuɗin da Jidda ta samu na tattara su na siya mata ɗan kunnen gold na ba ta ta maƙala a kunnen ta. Sai da na yi shawara da Yallaɓai shi kuma ya ce kudi na Jidda ne in ta amince sai na siya mata. Da na tambayeta tace mini tana so shi ne muka je tare kasuwa na siya mata. Amma na cire 30k a ciki na ƙara jarin hijabai da na ce ma na ara sai ta ce ba aro ba na baki Umma, na yi ta saka mata albarka. Adanan ya kai ta ta yi register ɗin layi tun da ta yi waya. Ta sha dokoki wajen Yallaɓai ban da shige shige WhatsApp kawai ta buɗe lambobi daga na mu sai na kawunta sai na yan ajinsu sai na y'anuwanta su kenan a cikin wayar. Ganin za ta fara zaman gidan kafin cuku cukun makaranta sai ta ce mini tana son ta koyi kayan su Snack haka sannan tana son koyon kwalliya na aminta da shawaranta sai na yi ma Yallaɓai magana shima sai ya yi na'am da mganar ya ce ta nemi in da ake yi sai ya ba ta kudi ta shiga..
Gimbiya na yi ma mgana saboda na ga ita duk ta iya su, ni kuma ba su dame ni ba, ita ta yi ma wata da ta sani mai yin snack sosai ta buɗe online class aka saka Jidda sannan ta na yin na gida sau biyu a sati alhamis da jummaa wata uku 20k Yallaɓai ya biya mata ta fara zuwa. Sannan na kwalliya ni kuma da na ke yi followimg ɗin su a I.G na yi ma wata Zahrajj magana da bayanin kuma ita a sharaɗa take amma tana da shago a nan zoo road wajen kamfanin Yallaɓai. Da na yi ma Jidda rigister ita sau uku ne a sati jumma da asabar da lahadi da safe. Shi kuma na Snack daman da yamma ne.
Jidda tana da naciya da dakiya in dai ta sa kanta za ta yi abu. Ko sati biyu ba ta yi da fara zuwa ba ta fara iyawa. In ta dawo gida sai ta gwada Yallaɓai kuma ya ɗaure mata kugu ya sa aka kawo mata fulawa da siga sauran kayan kuma ya ba ta kuɗi ta siya kwalliya kuma Tariq ya aiko mata da babban kit na ƙwalliya, Baby ta yi jin haushi ta ce an fi son Jidda a kanta in ta yi mata dariya. Maganar gaskiya Jidda na da farinjinin jama'a sosai saboda yanayinta na sanyi da rashin hayaniya.
A tsukin Marwa ta haihu an samu mace ta ci sunan Innayi ana kiran ta Afiya muka tafi Rano suna har Gimbiya ta je, itama cikinta har ya turo gaba. Kwana uku muka yi a gidan Marwa ni da Munnira da Hauwa da su Ma'u da Rahila sai Ya Balki. Su Anty Bahijja sun zo suna amma ba su ko kwana ba, dangin Baban Marwa ma sun zo amma washe-gari suka koma mu kaɗai aka bari muka yi soye muka natsa. Ana gobe za mu koma gida ne muka yawata garin mun je gidan su Kawu gidan su Nene kenan daga nan muka je gidan su Hauwa. Na karshe shi ne gidan su Gimbiya. Hajiyar Tafida na nan da ƙannen Gimbiya da suka zo gida.
Ƙiri-ƙiri suka yi mana wulaƙanci ita dai Hajiyar ta karbe mu faram faram amma ƙannen Gimbiya saboda ni a wulakance suka amsa gaisuwar mu. Shashen Mamansu Sameena me kawai aka karrama mu. Bayan mun fito daga gidan Munnira na ta kumduma zagi ni da Hauwa muna yi mata dariya. Na ɗan ji haushi amma ban damu ba daga baya na watsar da abin. Washegari muka koma gida Kano kuma ko a labari ban taba faɗa ma Yallaɓai ba.
*****
Yallaɓai tuni ya zagaye filin shi an saka get har an fara gini gadan-gadan domin yanzu Yallaɓai kuɗi yake samu mahaukata. Kwangiloli sama da biyar yake yi a lokaci ɗaya.
Ba zato ba tsammani ban ma saka rai ba Yallaɓai ya siya mini mota a watan November ranar goma ga wata ranar da Yunma ta cika shekara ɗaya. Har na shirya mata party a gida Jidda ta yi mata cake tun da yanzu ta ƙware, sai ga Yallabai da maƙullin mota ya siya mini vibe fara, amma ba sabuwa ba ce sai dai ba ta sha miya ba. Na daka tsalle na ruƙumƙume Yallaɓai ina faman ihu da murna ni da yara shima farinciki yake yi ganin yadda gabaɗaya na rikice saboda murna.
"Mota ka siya mini Yallaɓai? Innalillahi."
Na ke faÉ—a na ma kasa mgana saboda murna da farimciki.
"Mu je ki ganta tana haraba. Ita na tuƙo, tawa na ce Musbahu ya taho mini da ita daga baya."
Ai sai gani ni da yara muna rige-rigen fita har da Yumna dake tafiya itama har ana neman ture ta Yallaɓai ya sunkuto ta ya biyo bayana.
Da na ga motata sai na dafa ta kawai na fashe da kuka.
"Yallaɓai wannan mota ta ce?
Shi da yara suna ta mini dariya ganin ina kuka sai ya ƙariso ya rumgumeni shi da Yumna yana bubbuga bayana lokaci ɗaya yana faɗin" Kin yi mota saura ki je ki sauke farali My Sady."
"Yallaɓai har saudiya za ka biya mini?
"In sha Allahu Sadiya ta."
Ai sai na ƙara fashewa da kuka na rumgume Yallaɓai na ƙamƙame shi ina ɗaga murya cikin kuka amma na kasa magana.
"Shii. Bar kuka yau ranar farimciki ne ok?
Ya faÉ—a yana É—ago fuskata ya fara share mini hawaye. Yumna na ta ya shi.
"Kin ga har Yumna ma ba ta son ganin Umman ta na kuka."
"Yallaɓai kukan farinciki ne"
Na faÉ—a wasu hawaye, na gangaro mini na farinciki.
"To za ki karar da hawayen na ki ne a yau? Ki adana su saboda ba ki ga komai ba. Tun da Ubangiji ya wadata ni ni kuma zan yi ta saka ki farinciki har ƙarshen rayuwar mu Sadiya ta."
A gaban yara na yi ɗage na sumbaci bakin Yallaɓai sannan na sake shi ina kallon shi kafin na ce.
"Na gode Yallaɓai. Ubangiji ya yi ma dukiyarka albarka. Na gode."
Na faɗa ina ƙara gocewa da kuka Yunma ma sai ta fara. Baby da Jidda na can suna santin mota, ko ta kan mu ba su bi ba,
"Bar kuka nan kin ga Yunma ta fara."
Ya faÉ—a yana bubbuga bayana. Amma na kasa tsaida hawayena. Sai da ya share mini sannan ya saka ni na shiga motar na yi bismilla da addu'a..
"Allah ya tsare Hanya Madam me"
Yallabai ya faÉ—a yana lekowa ta window
Yunma ta ya fito ni, na karɓeta ina fadin" Amin Sadaukina "
Babby har ta kame a gaba Jidda dai baya ta buÉ—e ta shiga tana faÉ—in.
"Umma tubuli Allah ya sa ki kashe ta lafiya."
"Amin Amin Jidda. Yallaɓai saura Jidda ka siya mata ta ta motar"
"Da a ce nan garin za ta yi makaranta da na siya mata amma tun da zariya ne sai dai in ta gama in sha Allahu."
"Allah ya amimce Yallaɓai na."