Sashe 91
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Muna gidan Halima za ta zo ba ta shiga shashen Gimbiya ba ta yini a bangaren Rabi'atu ba abin da ba ta bata in dai ta gani ta ce tana so za ta ce ta ɗauka. Ni dai ta so ta sake shigowa jikina na ce nahi. Ai kin ci taliyar ƙarshe amma dai muna gaisawa sannan in ta zo gidan tana shigowa mu gaisa ni ce ba na sakar mata. Da baffan Rabi'atu ya je makka shi da Antyn ta, Har Nene da su Maman farko sun samu tsaraba Yallaɓai Jallabiya da Darduma da casbaha da dabino da ruwan zam+zam. Ni kaina an siyo mini abaya yara ma kowa da na shi har Jidda dake makaranta Gimbiya ma ta samu abaya. Ni kaina wayon yarinya na ba ni mamaki sumu sumu da ita ashe ta san abin da take yi.
Su Anty Bahijja ko duk an bi su da dabino da ruwan zam-zam suna ta taɗin suna jin daɗi. Ni dai ban damu ba da duk abin da take yi ba lokacin ta ne ta yi wata rana ba za ta yi ba mu kan mu ai duk mun yi wannan bin a farko muka gaji muka haƙura Gimbiya ce ke damuna kuma na faɗa mata ta yi haƙuri amma fa ba ta da yadda ta iya da Rabi'atu. Wacce ko zazzaɓi Nene ta yi kaf yan gidan su sun zo duba ta. Na cen maiduguri su kira waya me ya sa Yallaɓai ba zo so ta ba?
Nan da ya samu hatsari Allah dai ya tsare buguwa ya yi a hannu sai gocewa a ƙafa haka suke tururuwan zuwa duba shi danginta na nan Kano na can ko suna ta kiran waya. Kamar ta goya Yallaɓai haka take ki da shi, biyayya take yi masa ko abi za ta ba shi sai ta rusuna ni fa ina gefe ne amma ni kaina na san yarinyar nan bariki kawai take gwada mana. Ni kaina zuciyata na motsawa ballanta Gimbiya? Ga shi kaumar yaran mu take yi kamar ita ta haife su an ce mai ɗa wawa. Har ta su Khalipa yanzu in dai tana gida suna bangarenta ita kenan ba su abubuwa suna ciye-ciye an ce mai ɗa wawa Yallabai gani ya ke yi a kan Rabi'atu xai iya faɗa da kowa. In Jidda za ta koma makaranta ba ta zaune ba ta tsaye sai ta ga ta koma ita ce kawo mata wancan ta ya ta wancan kuma duk ya gani kuma wallahi hakan yana tasiri. Baby ko daman ta zam yar ɗakin ta ko gidansu muka je wani abu ya faru ita da danginta kamar si goya mu. Itama in ta shiga damu dangin haka za ta daraja su. Maganar gaskiya sai dai ƙin gaskiya amma Rabi'atu tana da hallaya mai kyau. Ta bakin Gimbiya ta kan ce an yi ma Yallaɓai surkullrn yan maiduguri ya ruɗe kan yarinya na kan yi dariya na ce ba surkulle sannu ciwon kai ne kawai.
Mun yi babbar salla Rabi'atu ba lafiya ashe ciki ne. Yallaɓai kamar bai taɓa haihuwa ba Gimbiya baƙuwa a harkan mu ai mun zama yan gari. Haka yake kiran waya yana faɗa ma mutane Rabi'atu na da ciki. Tarewa gabada ya yi a bamgarenta yana kula da ita tun da laulayi take yi mai zafi, Ni ko duk abin da yake so a yi masa ni zai kira itama in tana son wani Umma kaza Umma kaza, na roƙi Allah ya cire mini kishin nan na hauka shi ya sa da ni ake renon cikin Gimbiya ko sai dai kuka a ɓoye in ta yi magana cibi ya zama ƙari lokacin da ya tare a bangaren ta yi magana da cewa ai muna gida ɗaya ba sai ya tare a wajemta ne zai kula da ita ba buɗe bakin Yallaɓai sei cewa ya yi ya tare ɗin sai ta hana shi ganin ya harzuƙa ya sa na shiga tsakani na lallaɓa shi ita kuma Gimbiya na ce mata ta yi bamza da shi duk abin shi dai ba zai dauwama a wajen ta ba.
Gimbiya faɗa mini take yi ba za ta iya jarumta na ba. Ba za ta iya juran ganin Yallaɓai na rawan jiki akan wata na da ciki ba. Na ce gwara ma ta saba domin yanzu aka fara. Wataƙila bayan Rabi'atu ma ya ƙaro wata itama ta zo tana gasar haihuwar to ya za ka yi in ba ka yi haƙuri ba?
*Janafty*
*TKG320B*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Rawan jiki da ɓare-ɓare kam Yallaɓai na yin shi a kan cikin Rabi'atu ga shi cikin na ta ya zo da laulayi ga shi ba ta son cin abinci in ku ka ga yadda Yallaɓai ke lalacewa a gaban yarinyar sai kun yi mamaki. Ni kuma duk abin da ta ce tana so haka zai marairace yana roƙo na domin na samar mata, ni kuma tausayi take ba ni ko bakomai nima uwa ce, wani lokacin kuma Baby yake sawa dafe-dafe nan Gimbiya dai ya san ko giwan wake ya sha ba zai tunkareta ba domin ba ma yi za ta yi ba iyakarta da Rabi'atu sannu Allah ya ƙara lafiya.
Kwanciyarta asibiti biyu sannan ta ɗan samu kanta sai da ta koma gida ta yi satuttuka. Antynta ta ɗauke ta ganin wahalan da take sha, Yallaɓai ya so ya hana na dakatar da shi da cewa ya barta a gidansu a kula da ita. Ya bari ɗin amma fa can yake tarewa in ya dawo daga aiki sannan ya dawo gida ya zaunar da ni yana bani labarin in na ga Rabi'atu sai na yi mata kuka ta rame kaza kaza, ni har gajiya na ke yi kamar a kanta aka fara samun ciki su 'ƴaƴan gidan ba a gaban sa aka samu cikinsu ba daga sama ya gan su, duk dauriyata sai da ya riƙa motsa mini zuciya. Tana gidansu sau biyu yana sakani muna zuwa duba ta ni da yara Gimbiya dai an tashi zuwa sai ta ce ba ta da lafiya duk da ya san ƙaryanta ne ba ya matsa mata sai ni. Ni dai na yi sakacin da gabaɗaya Yallaɓai ya gama raina ni in dai akan lamarin matansa ne ko abu ne ba zai tunkari Gimbiya ba sai ni. Saboda ina yi masa kara shi kuma hakan sai ya bashi damar ya rika cin ko wata kasuwa a saman kaina , yanzu kuma lokaci ya kure mini na yi sakacin da ba zan gyara komai ba tun farko da ban bashi fuska zan iya ɗauka ba da wataƙila nima zai shakkar tunkarata da sha'anin matarsa kamar yadda ya ke jin shakkar tunkaran Gimbiya.
Ba ni kaɗai ba dangin shi ma sun ta sintirin zuwa duba ta zuwan mu na ƙarshe can na ga Halima ta yi baje-baje kamar a falon Nene ban yi mamaki tun fa yanzu ai Rabi'atu uwar ɗakin ta ce. Gimbiya ta ɗauka bayan ita ba wata macen da Yallaɓai da dangin sa za su yi ma rawan jiki saboda samun ciki sai ta ga ma suna abin da ya fi wanda suka yi mata a baya. Sai ta sha mamaki domin tun cikin na ƙaramin sa Yallaɓai ya gama tsara in mace ne ga sunan da zai saka Aisha in namiji ne kuma Alhajinmu zai yi ma takwara zai yi zai yi kaza har na haddace su a kaina.
Gimbiya ta yi ta ƙunci in an yi wani abu da ya bata haushi ta same ni da mganar na gani ko? Na ce na gani mana amma ban nuna na ji ko na gani ba itama in ta yi haka sai ta zauna lafiya. Amma ba ta ji shawarata ba kafin Rabi'atu ta dawo gida sai da suka yi tsiya akan ranar girkinta yana kai wa dare a can. Ta ga fa nima har ranar da yake ɗakina abin da yake yi kenan amma ta na gani ban ma na nuna na gane abin da yake yi ba, amma ita da shegen kishi ta yi masa mgana har tana saka ni a ciki wai na faɗa masa gaskiya ba ya adalci tunda yana jin mgana ta.
"Tana gidan nan ma rashin adalci yake yi mana Maman Jidda. Ba ta gidan ma ba zai daina ba."
Ina zaman zamana a bangarena ta kira ni a waya sha É—aya saura na dare. Na ji dawowarsa ba daÉ—ewa ni na ma É—auka wani abu ne ya same shi amma sai na iske shi zaune fuskar nan kamar hadari ya É—ora kafa É—aya kan É—aya a saman kujera yana karkaÉ—awa alamun yau fa akwai masifa in Gimbiya ta cigaba da zungurin sa.
Kallonta na yi, Baiwar Allah ta yi masa kwalliya da fa zafi ka zauna jiran miji har sai ka siƙe sannan zai dawo. Amma yanzu in na ce bai kyauta ba daga ni har ita zai iya cewa mu bar masa a gidansa a yadda dai yake zaman taƙama nan yana kaɗa kafa ji yake yi yana daidai da koma wacece.
"Fisabillahi yana kyautawa? Sai ya je ya shantake? Tun ƙarfe nawa na gama shirina ina jiran shi? Ni ban hana shi zuwa ba amma sai ya yi abin na shi da tunani a ciki.'
"Ok wato kina so ki ce ba ni da tunani ko Saudatu?
Ya faÉ—a yana daga zaune, a É—an kuma fusace domin ni fa na daÉ—e ban ji yana kiran ta da Daughter da ya saba ba itama tuni Daddy ya kama kan shi Babansu Jidda ne ko Abban Khalipa.