← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 103

Sashe 29

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mun kai har wajen misalin biyun dare ina ba ma Ma'u baki a ɗakina mu ka kwana ni da ita saboda na ga ba ta ma cikin natsuwarta. Tana fashin salla ai da na saka ta mun yi tsayuwar dare a kan Alhaji Mustapha amma ni sai da na yi raka'a biyu sannan na kwanta. Duk da nauyin cikina amma ina ƙoƙarin yin salololin dare tun da na riga na saba. Ina da tabbacin Ma'u ba ta samu barci a daren ba duk lokacin da zan farka idanuwanta biyu. Baiwar Allah ta ba ni tausayi ni ma ai na shiga haka a baya kuma na san yadda mutun ke ji a zuciyarsa. Na so na zauna nima ban yi barci ba na ta ya ta jimami da ban baki amma ina barci ɓarawo sai da ya sace ni sai asuba na farka har ma mun kusa makara. Ina idar da salla na fita zuwa ɗakin su Jidda ganin Ma'u ta samu barci can na je muka yi azkar da karatun Qur'ani sai bakwai saura na baro ɗakin na bar su su ɗan ƙara runtsawa tun da ba zuwa makaranta yanzu mun kan kai sha ɗaya ma ba mu tashi ba in ba Yallabai na gidan ba ne in zai fita da wuri.

Falo na dawo na cire waya ta a chaji ta daÉ—e da cika tun jiya amma na manta ban cire ba. Yallabai na kira sai da ta shiga ma na ga kamar ya yi safe da yawa ina ma wannan tunanin na ji ya É—aga wayar a muryansa na fahimci kamar ya na barci ne na tashe shi.

"Sadiya me ya faru?

Ya faÉ—a da sauri Allah sarki bawan Allah shi ma hankalin shi ya tashi ganin kirana a wannan lokacin. Ina da ciki fargabansa kar ya zo wani abu ne ya faru mara daÉ—i.

"Ka kwantar da hankalin ka bakomai."

Na faÉ—a cikin kwantar da murya ina jin ajiyar zuciyarsa.

"To ina kwana? Wallahi na tsorata da na ga kiran ki, "

Saboda ya san ni ba mai damun sa da waya ba ne in har ya na can gidan, in kuma ya ga na kira to ba lafiya.

"Kai kaÉ—ai ne a in da kake?

Na tambaye shi sai ya ce shi kaÉ—ai Gimbiya ta can É—akin yara.

"Me ya faru ne?

Ya sake tambaya kamar bai yarda da cewa wani abu bai faru ba."

"Jiya ne bayan fitan ka sai ga Ma'u ta zo mini cikin kuka Alhaji Mustapha ya sake ta."

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un wani irin saki kuma?

"To ai har da marin ta ma ya yi Yallaɓai"

"Mari?

Ya maimaita cikin sigan tambaya.

"Ƙwarai kuma ya ce ta bar masa gidan sa a daran"

"Subhanallah me ya faru a tsakanin su haka?

"Ka taho gida in ba damuwa yanzu sai mu yi mganar."

Nan da nan ya ce min gashi nan zuwa. Bayan mun kashe wayar na zauna kawai ina tunani rayuwa kenan
Yau wai ni ce Ma'u ta zo mini da matsalanta, yau ina su Ya Murja ina su Anty Bahijjan ina su Shema'u? Yau duk ba za su yi mata amfani ba dole dolenta dai jininta ne zai yi mata wani anfanin da a da take ganin ni ban isa ba, kuma yadda ta zo ta faɗa mini wallahi sai Alhaji Mustapha ya roƙi gafaran Ma'u a kan wannan cin zarafin da ya yi mata. Zuciya ta sai ta fara zafi ina cin wani raɗadi daga ƙasan zuciyata kamar ni a ka yi mawa, na yadda akwai jinin Ma'u a jinina shi ya sa yake motsawa a kan ta in wani abu ya same ta.

Ina nan zaune a falon su Jidda sama da mintina arba'in har Yallaɓai ya shigo gidan. Shima dai ya nuna damuwarsa a saman fuskarsa na zauna na zayyana masa duk abin da ya faru na ƙarishe da faɗin" Tun jiya da ta zo ta ke kuka. Ta ce ba za ta koma ba tun da ya tozarta ta, ba ta yi barci sai da safen nan ba ka ganta ba gwanin ban tausayi."

"Gaskiya bai kyauta ba. Haba da hankalin shi me ya sa zai yi haka?

Yallaɓai ya faɗa kai tsaye, shi ma ai ya san gaskiya kowa kuma ya ji wannan mganar sai ya ce bai kyauta ba.

"Kuma a kan gaskiyanta ta yi mgana. A kan gadon ta fa ya je yana yin waya shi ne ta yi mgana ya yi mata wannan wulaƙanci."

Na faÉ—a cikin bayyana jin haushina.

"Shi ya sa na ce miki bai kyauta ba. Ya kuma nuna ko auren ya yi ba zai yi adalci ba. In ba wawanci ba me ya sa za ka zo cikin gida kan gadon ku na sunna kana waya da wata macen da ba ka riga ka aura ba, kenan itama ka nuna mata matar ka ba ta da daraja a wajen ka in ta shigo gidan za ta iya taka ta yadda ta ga dama tun da kai ka ba ta damar haka.'

"Gaskiyan mgana kenan"

Na faɗa ina kallon Yallaɓai ina mirmishi. Shi ya sa na ke son Yallaɓai ta wanni fanni akwai shi da faɗin gaskiya komai ɗacin ta.

"Ita kuma rashin kyautawarta ɗaya ne me ya sa ta fasa masa waya? Da ta yi masa magana bai ji ba da ta ƙyale shi ta bar masa ɗaki in ta yi haƙuri zai wuce har kuma wata rana ya dawo ya na jin kunya. "

Duk abin da Yallaɓai ya faɗa gaskiya ne, nan na zauna ina faɗa masa wasu abubuwan da suka faru a baya ya jinjina kai yana faɗin" Duk laifin shi ne a matsayin shi na magidanci bai zama adali ba, ai ba a ce in za ka ƙara aure ka tozarta matarka ta gida ba. Ita kuma in ta nuna damuwarta ba ta yi laifi ba mijinta ne zai ƙara aure kuma tana dai-dai da ta nuna kishinta afili sai dai kuskurenta ɗaya me ya sa ba ta yi kishin cikin ilimi ba? Ta yi kishin da ta ta yar ma da mijinta hankalinshi kuma ganin tana kishin ne ya sa ya ke yi duk abin da ya yi, in da a ce ta yi masa kamar ba ta san yana yi ba da tuni ba ta kai su ga haka ba. Ta yi koyi da ke mana? Na san kina kishi na amma kishin mummuƙe kika yi mini sai da na dawo ina jin kuyar ki cikin ruwan sanyi kika saka na gane ba ni da wayau"

Ya ƙarishe faɗa yana kallona yadda na ga bai yi dariya ba ne na ga ne ba wasa yake yi ba. Sai da na harare shi sannan ya yi mini mirmishi yana faɗin ai gaskiya ne kishin mata masu Aji kenan a gasa namiji ta ruwan sanyi da zai zo ya na ba da haƙuri da kan shi, shuru na yi ban yi magana ba domin ni kaina ai ya gasa min aya a hannu kawai dai ana kauda kai ne a zamantakewa.
Mun tattauna dashi sosai daga karshe ya ce mu karya sai mu tafi tare da shi har da Ma'un nan kuma take ya kira Alhajin Mutspha ya ce za mu taho gidan Ma'u nan ba daɗewa ba ko kunya ya na faɗa ma Yallabai sun samu matsala jiya ba ta kwana a gidan ba Yallaɓai ya ce ya sani gidan sa ta kwana tare ma za mu taho ya ce yana gidan Hajiya Zainab amma zai taho nan gidan Ma'u yanzu.

"Ka ji min munafuki wato saboda ita Hajiyar ta san Ma'u ba ta nan shi ya sa ya je can ya kwana."

Na fada cikin jin haushi tun da duk na ji wayar na su a speaker ya saka wayar lokacin da ya kira shi.

"To mi ye laifin shi? Matan ahi biyu bai kamata ya yi kwanan gauro ba."

Wata uwar harara na jefi Yallaɓai dashi sai ya fara mini dariya ya na faɗin" Daga magana? Yi hakuri ba ni na kai zomin ba rataya kawai a ka ba ni."
Saboda haushi ban tanka shi ba yanzu yanzu ya na maganar kamar zai yi gaskiya a lamarin shin amma kuma yanzu ya na so ya yi son kai a lamarin shi.

Tare da shi muka dafa ruwan zafi shi ya ma soya ƙwai, ba buredi sai ya fita ya siyo, kafin ya dawo Ma'u ta tashi na saka ma ruwan a hiter ya yi zafi na ce ta yi wanka mu karya Yallaɓai ya zo za mu tafi can gidan na ta gabaɗaya.
Sai da ta yi wanka nima na yi, kaya na bata ta saka nima na zurma doguwar rigata mai kama da buhu ta bakin Yallaɓai bujun bujun ga cikina gaba ina tafiya a tale, Yallaɓai na falo can na je na same shi muka karya ita Ma'u ciki na kai mata na ta saboda ta samu sakewa. Sai da za mu tafi na ta da su Jidda suna ta barci na ce mata za mu fita ta yi musu wani abu su karya dashi ita da Baby in kuma za su sha Tea ne dai ga su ga gidan nan mu mun fita zuwa gidan Umman su Ma'u.

Yallaɓai ya ɗauke mu a motar shi, sai da muka ɗau hanya ne suka ƙara gaisawa da Ma'u ya na ba ta haƙuri sai ta fashe da kuka ta na faɗin" Baban su Jidda sakina fa ya yi a kan wata macen?

"Ki yi haƙuri ya yi kuskure kuma zan faɗa masa."

"Kuma wallahi sai ya biya ta marin ta da ya yi."

Na faÉ—a a fusace, sai Yallabai ya kalleni kafin ya ce"To ya biya ta, ko rama marin na ta za ta yi?

"In ta kama ba"

Sai Yallaɓai ya girgiza kai hankalin shi na wajen tuƙi ya ce" Ma'u kar ki biye ma wannan ƴar'uwan ta ki, a kusa ta ke kin dai gane"
"Ba wani a kusa na ke sai gaskiya ai ba zai mari banza ba."
"To na ji bai mari banza ba, daman ai ya san bai kyauta ba kuma ina da tabbacin yanzu haka ya yi nadama."

"Daga baya kenan an yi sadaka da bazawara."
Chapter 29 · 0% Book details