← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 103

Sashe 35

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gida ya kacame da ayuuka. Da yake za su yi waina sai sinasir da aikatau muka kai sannam za su yi alale da shinkafa jalop mai kaza. tun da akwai naman miya da Yallaɓai ya aiko da shi. Raguna kuma uku Yallaɓai zai yan ka ma Rukayy suma ragunan su Suwaiba na faɗa mini su Anty Bahijja suna ta surutu ni a bakin ta ma nake jin raguna biyu Ya Usman ya siya masa ɗayan kuma Mimisco ce kuma ya ce tun da da sunan Rukayya a ka ba da su to duka za a yanka mata su. Sannan nima na ba da a yi mini tsire sannan na saka mai yin ledojin kayana na hijabai ya buga mini na suna da jakar nan mai ɗauke da sunan Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna) name on 17 November 2020.
Cut-ceey: Hauwa'u Yusuf Muhammad(Jidda) and Maimunatu Yusuf Muhammad(Baby)
Lemuka da ruwan roba katan katan Yallaɓai ya saka a ka sauke mini sanman ni kuma za mu yi zoɓo da kunin aya duk za mu saka a robobin ma su ɗauke da sunan Rukayyatu.
Wanda a ledan za a saka mutum da jalof ɗin shinkafa mai kaza sai tsire da zoɓo wannan na in zai tafi gida ne. Da yamma kwandon tumatir da solon tattasai da attarugu mai yawa Musbahu ya zo da shi tare da gyararrun kaji guda ashirin a buhu, lokacin su Anty Bahijja da su Gimbiya duk suna gidan ba aikin da suke yi sun kame a gefe suna tsegumi tare da taɓe baki ni ko kallo ba su ishe ni ba, da suka ga an kawo wannan kayan nan kamar su mutu sun ɗauka Yallaɓai ne ke ta kashe mini kuɗi tun da nima yar matsiyata ne ba ni da kuɗi. Ya Hamza da Ya Auwal sai suka suka haɗa mini 150k na kuɗi saboda na ce musu zan yi suna kuma Yallaɓai ba shi da kuɗi, abin da ya ba ni ba za su ishe ni ba, Shi ya sa suka tura mini kuɗi har Datti sai da ya tura mini 30k ya ce na ƙara. Kawu Abba 50k ya tura mini bayan Marwa ta zo mini da atamfofi masu tsada guda uuku da kayan jarirai. Amina ma turamen ta kawo mini da kayan jarirai Farida ita ma turminta huɗu da kayan jarirai sama da guda biyar, tun kafin goben ta yi gefen gadona ya fara cika da kaya sannan wasu ma hidiman  su Munnira ke yi ba sa faɗa mini. Suma ita da Hauwa turame uku suka yi min da su pampers da kayan sanyi sannan sun ba da an yi mini yajin jego mai yawa mai daddawa.

Ina can cikin ɗaki ban sani ba Hauwa ta zo tana faɗa mini wai ashe sai da Anty Bahijja ta kira Musbahu tana tambayan shi ko Tafida ne ya ba da saƙo ya kawo? Shi kuma ya ce ni na tura masa kuɗi ba Yallaɓai ba ni tana faɗa minibsai da na bushe da dariya. Matar nan ba za ta bar ni na huta ba na yi alƙwarin in ta sake magana a gabana sai na mayar mata da martani ana cikin gida a na aiki su kuma suna zaunes sai ji da jiyarwa.

Bayan mangariba mai ɗinkin mu ya kawo mini sauran nawa  da na yara sai na Farida da Amina. Ni na fita har haraban gida na karɓa muka yi maganar ƙarishen kuɗin ɗinki na dawo kenan falon Baby ta tare ni tana faɗin wai Anty Gimbiya ba ta zo da su Khalipa ba. Kayan ɗinkin da ke hannuna na miƙa ma Amina da ta zo ta tare ni da mgana na ce ta bari in zo.
Ina sanye da doguwar riga tsaraban makka ne cikin tsaraban Yallaɓai., rigar ba takai mini har ƙasa  sosai ba tana da mayafinta shi ne ma jiki na, na yi kyau ɓulɓul da ni domin ga ruwan zafi daman sannan kuma na saka Aisha lame ta kawo mini mai da shower gel, kuma ina kula da jikina ina cin mai kyau ina shan mai kyau ni kaina na san na yi kyau da haihuwan Yumna sannan cikina ya fara komawa jikina ya yi cif sai na zama wata yar dumduma gwanin sha'awa kowa ya zo ya ganni sai ya ce mini na ƙara kyau da na haihu mene ne sirrin? Na ce Yallaɓai ne sirrina muna ta dariya.

A tsakiyar falon Yallaɓai na tsaya tun da nan suke zaune har da su Halima. Anty Maimuna ba ta zo ba itama Anty Bahijja gulma ne ya kawo ta. Yau ga shi Anty Bahijja na zaune amma bayan gaisuwa ba abin da ya ƙara haɗa su da Ma'u duniya juyi juyi. Gimbiya ta ƙura mini ido tana kallona ita kuma Naja da gayya take ce  mini" Ka ga uwar gida a gidan Uncle Tafida"
Na yi mata fari ina faɗin" Faɗi ki ƙara Uwargida mai babban muƙami a wajen megida "

Sai ta yi shuru ai ba zan bari ta saƙa mini magana ba Gimbiya na kalla ina faɗin" Baby ta kawo min ƙaran ki."
Sai ta yi wani luu da ido kafin ta ce" Ni fa? Me ta ce miki na yi?
"Ta ce ba ki zo da Khalipa ba"
Anwar ma da za ta zo da shi ya na wajen Halima.
"Ayya ai Khalipa na Rano Anty Marliya da ta zo ya saka rigima sai ya bita sai kawai na ce su ta fi dashi."
Sai na jinjina kai kafin na ce" Amma ai da kin ce su zo da shi saboda suna ko?
Kawai karaf  Halima ta saka bakinta.

"Don dai suna me ya sa zai dawo? Suna dai ba biki ba fisabilillahi."

"To nima shi na gani."

In ji Naja.

Anty Bahijja dai ba ta yi mgana ba, ni ko sai na juya ina kallon Halima kafin na ce" Aa. fa ba suna kawai ba wannan sunan ya sha bambam da sunan da kika saba zuwa ko gani Halima. Suna ne garurumin da baki taɓa ganin irin shi ba."

"Allah ko?

Ta faɗa cikin mamaki ni kuma sai na gyaɗa mata kai, muna cikin haka ne sai ga su baby da murna da akwati Laaila ta iso mutanen Abuja. Muka rumgume juna ina yi mata maraba ta gaggaisa da su Anty Bahijja. Yara wajen ɗaukan wata leda suka yagata kayan ciki ya zube kayan fulawa ne ta yo mini cincin da donot sai cake, ina ta faɗa sai ta ce ai namu ne ta zo mini da shi saboda gobe. Ta ce mini ma ta saka ƙanwarta ta yi mini meatpie gobe za ta kawo. Su Amina duk sun taho falon da suka ji tahowar Laila.

Munnira ta daddage ta rangaÉ—a guÉ—a Amina na ta ya ta. Ina ta dariyan farinciki na ce"Na gode Anty Laila."
"Ba komai an zama É—aya. Kin ga yadda yayanki ya ruÉ—e. Ki yi ki gama aikin nan ki tafi kayan fulawan nan ma duk tare da shi muka shiga kasuwa muka siyo komai ina cewa ya bari na siya da kuÉ—ina ya hana shi dai faÉ—i yake Sadiya ce ta haihu ta yi ma Mama takwara saboda haka muma za mu yi ma wannan haihuwan na ta kara."

A gaban su Anty Bahijja ta fiddo mini kayan suna. Atamfa biyu leshi ɗaya sai kayan jaririya guda bakwai bayan su pampers da mayuka da rigunan sanyi. Har su Aina sun ƙariso suna ta ɗaga kaya suna gani da farinciki. Amina ta ranguɗa guɗa tana faɗin" wannan yarinya ta ga gata. Ta shaida ita ɗin yar dangi ce gaba da baya."

"Tabbas yar dangi ce. Ya Hamza ya nuna bajintarsa ga Ya Auwal ma ya nuna na shi Ubangiji Allah ya bar zumumci."

Aka amsa da Amin gabaɗaya  da gayya ba na ce" Kuma duk sun tura mini kuɗi duk da su na yi wasu hidiman."
Mu mun man ta da su Gimbiya a falon ma ballanta su ce da gayya mu ke yi sai da daga baya ne da muka haÉ—a ido da Gimbiyar sannan na ce bari nima na É—an É—ana.

"Na daɗe da sanin ni yar dangi ce amma na ƙara ganin kara a haihuwan Rukayyatu. Na ga karamci a wajen ku yan uwana na gode. Alhajin mu ma buhun shinkafa cir shanshera ya ba ni saboda Rukayya"
Su Rahila har da kabbara
Ni kuma na cigaba da faɗin "Mijina ya yi mini dukkan gata na gode masa. Sannan ƙawayena da ku dangina gabaɗaya kun rufa mini asiri kuma ina mai gode maku uUbangiji ya ruɓanya muku."

Munnira da Amina sun fi kowa zaƙin murya wajen amsawa da Amin
Munnira har ta na faɗin wani abun ma sai gobe. Ta ba ni hannu muka tafa ni da ita. Gabaɗaya su Gimbiya sun gama muzanta Anty Bahijja ma ba san tafiyarta ba na ji daɗin haka saboda ta fahimci ba Yallaɓai kaɗai ya yi mini hidima ba, Gimbiyar ma sai wajen tara na dare suka fita tare da Naja da Halima sai bayan tafiyar su ne da muka zauna da Sameena nake jin wasu manganganu. Ni da ita ba mu taɓa zama mun yi maganar zama na da Gimbiya ba sai ranar. Kusan raba dare muka yi muna hira na faɗa mata wasu rigingimun da suka faru tsakanina da Gimbiya. Itama tana ba ni wasu labaran da ban san da su ba.

Ashe Gimbiya kishi take yi da ni da tana da iko da tuni ta koreni. A bakin Sameena nake jin ko maganar haihuwan ta ce Tafida sai rawam jiki yake yi a kaina kuɗin shi duk a kaina da yayana ya ke ƙarewa to daɗin abin ma dai ban yi irin haihuwanta ba mace na haifa. Haka ƙannenta suke ta faɗa da masu goya mata baya. Kuma wai a haihuwan nan da na yi sai da ta nemi ya ranta mata kuɗi ta biya kuɗin shipping, amma ya ce mata ba shi da kuɗi aamma ni ga shi nan ya ba ni kuɗi ina ta wadaƙa har suna na shirya mai kama da biki. Har cewa ta yi yadda Yallaɓai ke jin maganata ko Nene albarka.
Chapter 35 · 0% Book details