Sashe 89
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nunawan ba shi da amfani in har ka bari wasu daga waje suma fahimta. Amma ina nunawa a yanayin da Allah ya hallice ni, mun sha yin faɗa ba adadi ni da Yallaɓai. Amma sirrina shi ne haƙuri gaskiya na saka haƙuri a kan komai ko na ji wani abu ya motsa mini sai na kira sunan Allah na danni zuciyata na yi haƙuri. In abu ya dsme ni Ubangijina na ke zama ina faɗa mawa ina, shi na kuma roƙa ya cire mini mugun kishi a zuciya na ce ya saka mini salama domin na samun zaman lafiya."
Gimbiya ta buɗe baki ta rufe kafin ta ce" Ikon Allah. Ni fa sai nake ganin duk wanda ya ce na yi haƙuri kamar ba ya sona ne."
Ta faÉ—a har tana yin tagumi.
"Haka za ki ji da farko. Amma in kika yi haƙurin wata rana ke ce da riba. Sai dai riban ya kan ɗau lokaci kafin a cinmma riban amma watan wata rana mai hakuri dai shine ke da riba."
"Haka ne."
Gimbiya ta faÉ—a cikin sanyin jiki, ni kuma ina ta mata dariya ta ce wai ko ba ni da zuciya ne bana kishin su.
"Kawai na saka ma raina ba don ni kaɗai Ubangiji ya hallici Yallaɓai ba. Kuma ni ban isa na hana shi abin da Allah ya ce ya yi ba. Sannan ina yi ma zamantakewar mu kara saboda nima ya yi mini kara, ya yi mini hallaci kamar yadda na yi masa shi ya sa nake tausan zuciyata ina karɓan duk wani abu da ya fito daga bangaren shi da zuciya ɗaya. "
Kai ta girgiza alamun gamsuwa kafin ta ce" Ga shi kuma kina ta ganin riban haka. Ki yi haƙuri a da ina yi miki kallon kin gama da Daddy domin yadda yake darajs ko sunan ki aka kira abin mamaki ne. Ya taɓa faɗa mini bayan Nene ke ce macen ta farko da yake jin kunyar ki roƙi sa abu ya kasa yi miki. Ya taba ce mini ke ce ragamar gidan shi, wakilyarshi da ba shi da haufi a kan karan da kike yi masa. Ke ya taɓa faɗa mini cewa ke ɗin ta musammance a rayuwar shi da har gobe ba ki samu madadiya ba."
Sai na kalleta ita kuma ta cigaba da faÉ—in" Ni ban gane ba na yi ta fada da shi a kan ki. Karshe dai ni ce ba na cin riba. Sannan su Anty Bahijja su yi ta nuna mini yana jin tsoron ki. Halima ma har ce mini ta yi in ban dage ba saboda ke Daddy zai iya rabuwa da ni."
Bsn wani ji mamaki ba da man na san ai ba sa sona. Saboda haka ba za su faÉ—i alheri a kaina ba.
Kamar an matsi bakin ta nan ta shiga faɗa mini mganganun da suke fada a kaina ba daɗin ji, da bakin ta da ke cewa duk in da Halima ta zauna sai ta zage ni, ta ce mini Naja ce ma kr kwaɓanta wani lokacin amma su Anty Bahijja sai dai su yu ta zugi in abu ya kwaɓe su koma gefe. Ko a nan hatsaniyar auren Rabi'atu duk suka kai ta suka baro miji duk ya gaji da ita.
"Kin gani ko? Kuma da abubuwan da kika yi ta yi ne yake tarawa shi ya sa ya ce ya gaji. Na sha faÉ—a miki ki yi hakuri domin hakiri shine mafitan ki, wata rana akwai wani abun da zai faru da za su nuna miki sun fiki kusa da shi akan ki."
"Gaskiya ne"
"To gwara ki gyara tun kafin lokaci ya ƙure miki "
Sai ta yi shuru amma ta daima kuka sai jan majina. muna zaume muka ji ƙaran buɗe get sai na miƙe lna leƙe ts window ina faɗin" Ga ta man ina jin ta iso"
"Wa kika kira?
"Nene"
Na bata amsa sai ta ware ido ina dariya na ce" Ba ita ba ce ta zo Mimisco ta kira."
"Na shiga uku Kin san faÉ—an Momi kuwa?
Gimbiya ta fada tana É—ora hannu a kanta.
"Ai gwara ta yi miki faÉ—a"
Kafin ta samu zarafin magana muka ji ana taɓa kofa ni na fara fita falo sai muka haɗe da Mimisco sama sams muka gaisa na yi mata jagora zuwa ciki yadda ta ga an yi baza baza da kaya ba sai ma ta tambaya ba.
"Me ke faruwa ne Nene ta kirani cikin damuwa da cewa na zo na gani Sadiya ta kira ta ce kun sami saɓani da Tafida har yana mganar saki?
Ta faÉ—a tana kallon Gimbiya ko zama ba ta yi ba.
Sai Gimbiya ta kasa mgana ta fara matsan ƙwalla.
"Ba kuka na ce ki yi mini ba malama"
Bakinta na rawa ta fara faÉ—a mata tana zuwa wajen fashe gilasan mota Mimisco ta ce" Amma dai ba ki da hsnkali ko Saudatu?
Sai ta fashe da kuka tana faÉ—in"Momi.."
Hannu ta É—aga mata kafin ta ce" in kina hauka ne Tafida ya fi ki hauka. Saboda kishi ki jawo masa asara? Ina ruwanta ita ta siya motar! Ba kuÉ—in mijin ki ba ne?
Ke da Allah ya rufa ma asiri amma kina ma yar da kan ki baya? Kin taɓa jin an ce ga Sadiya can da Tafida suna rigima sabo da ku! Ko ita ba mace ba ce?
Ta ƙarishe faɗa cikin faɗa har tana yi mata tsawa.
"A yi hakuri Mimisco."
"Sadiya Saudatu ba ta jin mgana gwara Tafidan ya sake ta ko za ta yi hankali."
"Ba za a yi haka ba in sha Allahu.'
Sai a lokacin ta zauna a gefen gado tana faÉ—in'" Ina shi Tafidan?
Na ce mata yana bangaren Rabi'atu.
"Tun bai iya fada ba kin ko ya ma Tafida iya tsiya kala kala. Ina daÉ—in shi don Allah?
Ita dai Gimbiya tana ta kuka wayarta ta É—auko jaka ta kira shi, har sau biyu bai É—aga ba.
"Nima ya ƙi daga kirana."
"Ki je ki same shi ne."
"Mu je to ki rakani."..
Ta mike tana faÉ—in haka.
"Ke kuma ki gyara ɗakin nan ki ma yar da wannan akwatin ƙaryan na ki."
Ta ce ma Gimbiya da ke kuka
"Kukan me kike yi! Ai ba ki yi kuka in dai kr ba za ki ji magana ba! Me ye ban faɗa miki ba? Na ce ki yi haƙuri ki kauda kai, ki yi ko yi da Sadiya amma ba ki ji ba? Wallahi in yaƙi saurarena ba zsn matsa masa sai ki tattara ki tafi can Rano wajen Hajiya burin ki ya cika kina ta kawo mana matsaloli a dangi."
"A yi hakuri Mimisco "
Na faÉ—a sai ta yi gaba tana faÉ—in" Sadiya lamarin Saudatu kamar ka yi ta dukan ta ne "
Muna tafe tana ta faɗa ni kuma ina bata haƙuri muna kofar shashen Rabi'atu take kara tambayata abin da ya faru na warware mata komai.
"Kin ki ko? Ina tarbiya mijin na faÉ—a kana faÉ—a? Ai bai burgeni ba da dukan tsiya ya yi mata ba kumbura baki ba."
Sai da na yi dariya sai a lokacin na tuna ashe bakin Gimbiya da ya ta sa Yallabai ne ya make mata baki a É—azu da suna mgana.
kiran shi ta sake yi aka samu sa a ya ɗaga sai ta ce ga ta nan a ƙofar shashen Rabi'atu tana jiran shi, ganin ta samu ya ɗauka sai na ce mata zan je na duba yara.
"Je ki Sadiya. Ni ba ri na yazo na ga ko zai saurare ni."
"ZAi saurareki In sha Allahi."
Na faÉ—a ina dariya.
"To tunda ke ma yau aka ƙi sauraran ki nima da sauƙi."
Ni dai ina ta dariya na shige bangarena na iske Baby ta gama soya dankali da kwai suna karyawa ita da su Khalipa nima sai na bi bayan su bayan mun gama na ce Baby ta je ta yi musu wanka ni zan gyara wajen,.
Sama da awa biyu ina bangarena ba wanda ya kirani har Baby ta yi ma su Khalipa wanda da yake akwai kayansu a bangarena ba su da matsala suna can falon su, suna ta wasannin su
Ni ko sai dai waya a hannua Jidda ta kirani muka gaisa ta ce tana ta kira Abban na su ba ya ɗauka na ce wata ƙila yana da bsƙi ne na yi mata ƙarya. Ta ba ni har Ummu Salma mun gaisa sannan muka yi sallama sai can Mimisco ta kirani ta ce na fito za ta fito. Na fito na gan ta tare da gogan yana ts wani cin mgani ko mgana bai yi mini ba a gabana ya sake rantsewa sai Gimbiya ta biya asaran da ta yi masa ita kuma ta ce ba damuwa za ta saka a zo a ɗau motar a kai wajen gyara.
"Shike nan?
Ta faɗa tana kallon shi, kamar ba ya son mgana ya ce" Shike nan amma dom ke ce. Da na sha alwashin sai ta bar ta je Rano ta yi wata tukunna za ta dawo."
Mimisco ta yi dariya kafin ta ce" Na gode daka ji mganata. Ka yi hakuri ai ta baka hakuri kuma na ce ta sake baka."
"Ya rage nata."
Ya faÉ—a yana zakuÉ—a kafaÉ—a hannayen shi cikin aljihun wandon dake jikinsa.
Ni Mimisco ta kalleni tana faɗi " Sadiya ki sake ba ma wannan rigimammen mijin naki haƙuri. Na samu ya hakura na hada su na yi ma Saudati faɗa ta kuma ji ta ce ta yi nadama na sakata ta duka ta bashi haƙuri ya ce ya wuce. Don Allah ki sake kwaɓar ta kin ji ko?
"In sha Allahu '
Na amsa mata ina mirmishi ganin Yallaɓai na ta hararata sai ka ce ni ce na yi masa laifi.
Direba ne ya kawo ta tace na gai da yara tana sauri ne yau baban su Naja zai bar kasar yana gida yans jiranta. Ta shiga mota direba ys ja suka fice daga gidan Yallaɓai ya juya zai wuce bai yi mini mgans ba.
"Yallaɓai."
"Ba ruwanki da ni to."