Sashe 34
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yallaɓai na gidan Mimisco ta kira ni ta yi minI barka bayan ita sai Anty Bahijja ita Anty Maimuna daman tun ɗazu ta kira ni, abin mamaki Gimbiya ba ta kira ni ba sannan ta ga status ɗina amma ba ta mini magana ba. Na so na yi ma Yallaɓai magana sai ban yi ba yana gidan har wajen sha ɗaya saura na dare nan ya ci tuwo ya zauna riƙe da Yumna muna ta hira da ni da shi da yara. Amma Gimbiya da ta kafa kira sai da ya yi mana sallama ya tafi, yau girkinta ne a fargabanta kar ya kwana a wajena tun da na haihu. Dama muna mganar abubuwan da babu ne na ce masa akwai komai sai dai kayan abinci in zai ƙaro sai omo da sabulun wanka da na wanki sai geron da Ya Aina ta yi masa mgana sai ya ce mini na rubuta na aika masa da shi gobe da safe Musbahu zai kawo min. Haka ko a kayi kafin na kwanta na rubuta na tura masa, tare da yara muka kwana Yumna ta tashi da kukan dare bayan na ba ta nono na sakar ma Jidda ita tana lallashinta ban ma san yauahe suka kwanta ba ni dai kamar ƴar maye haka na kwanta ina barci.
Washegari tun safe Ya Murja ta fara dira ko da ta zo ma har Jidda sun yi wanka ta gama ɗumama sauran tuwon jiya. Baby ce har da rigiman ita ba za ta je makaranta ba na ce lalle ta na da aiki ni masifa na fara mata za ta fara mini kuka na ce zan mata bugun tsiya ƙarshen ta dai Ya Murja ta lallaɓata sannan ta amince suka tafi. Yau Ya Murja ta yi ma Yumna wanka nima ta taimaka mini na gasa jikina bayan na shiga ruwan ɗumi saboda ɗinkin dake jikina. Sannan ta fara gyaran gidan ba daɗewa sai ga Gwaggo ita da Balaraba Maman Saude sun zo mini barka kamar haɗin baki sai ga Nene da Hajiya Iya sai Maman farko Adnan ya kawo su sai da na faɗa musu Yunma ta zama mai sa'a kishiyoyinta na ta kara kaina a kanta suna ta dariya. Sun ji daɗin ganin mu tas lafiya lau kamar ban haihu ba. Ba su wani jima ba suka tafi amma Balaraba sai ta tsaya tana kama ma Ya Murja aiki. Bayan fitan su ba daɗewa sai ga jama'ar Gandun albasa ni da kaina na kira Inna Mariya na sanar da ita na haihu, tare ta ke da matan su Kawu Tasi'u dukkansu dai suka yi mini barka ba daɗewa suka tafi.
Da safen Musbahu ya kawo buhun gero sai rabin buhun siga sai kwalin omo guda biyu, tissue sai kayan tea da yawa saboda daman na ce masa sun kusa ƙarewa. Kayan abinci kuma ya ce sai anjuma za a kawo daga kasuwa.
Ranar ma kamar jiya ne, yini gidan ya yi a cike da yan barka Amina ta kira ni a waya tana faɗin tun ana jibi suna za ta taho na ce daman ban ɗauke ma kowa ba har su Ya Hamza na faɗa musu in su na yafe musu to ban yafe ma matan su ba. Tun da na haihu kullun gidana Munnira da Hauwa suke yini da Mubeena , Su Ya Aina ma kullum sai sun leƙo Ma'u da Rahila suma kullun sai sun taho kamar haihuwar farko. Yadda na daɗe ban haihu ba , ba shakka na faɗa ma Yallaɓai taro zan yi ba ni da taro ba domin na yo gayya. Har Tariq da ya kira ni ya yi mini barka sai da na ce ban ɗauke ma Farida ba. Haka ma Kawu da ya kawo Marwa shi da ita na ce to ya sani tun ana gobe suna domin suna zan shirya sunan da ban taɓa yi ba yana dariya ya ce ya amince mini domin ya cancanci na yi taro na gani da za a ba da labari.
Amma Yallaɓai na neman ya kawo minI yawa wai shi ba shi da kuɗi ya faɗa mini an gama ginin kamfamin shi yanzu oder kayan amfani ke gaban shi zuwa farkon shekaran 2021 yake son su fara aiki. A takaice dai yana faɗa mini ba shi da kuɗi na ce na ji ya ba ni iya abin da ya yi niyya.
100k ya tura mini na shgalin suna, 100k kuma ya ce na siya kayan fitar suna ni da yara. Daman ni bai san ina da kala uku a ɗinke ba cikin kuɗin da ya ba ni na hidimar haihuwa na siya ma kaina. Da kuɗin da ya ba ni sai na siya mana wani swiss lece mai kyau blue ni da yara daman suma na yi musu kala ɗaya na Atamfa super kowaccen su na yi mata riga da zani. Nima na ɗinka super wax ɗin amma kalata na dabam ne. Sannan su Munnira sun fitar da ankon suna wata vatik mai kyau da yarari, suka kuma ce ba su ɗauke ma kowa ba. Kaf yayyena sun siya tun da Munnira ce ta saro ankon haka Farida ta ce a ɗaukan mata in kai mata ɗinki ita da Amina Marwa ma an nan kano a ka kai mata ɗinki har Saude da ke dutse ta siya itama za ta zo matan su Ya Hamza a mota a ka sanya musu na su a cewar su ba su yarda a ɗinka musu a nan ba. A dangin Yallaɓai daga Sameena sai Jamila da Suwaiba suka yi, Mimiaco ba ta yi ba amma ta yi ma yaranta ƙananun Mubeena daman yar gidana ce, Munnira duk ta nuna ma su Anty Bahijja amma take faɗa mini Anty Maimuna sai da ta ce wai na cika tsirfa haihuwa ta ukun ne sai na fidda anko ita kuma ta ce su suka fidda. Ba dai wacce ta yi mu ma ba mu damu da su yi ɗin ba domin ba saboda da su muka fidda ba. Na tura su Hauwa Jamilu da su samira duk sun siya an akai musu har gida sun yi mini alƙwarin zuwa mini suna.
Gimbiya ma ba ta siya ba ni da sai da na kwana biyu da haihuwa sannan ta zo mini barka da borin kunya wai ba ta samun zama ne ga aiki ga shago ni dai tak ban ce mata ba. Da Munnira ta nuna mata ankon sai ta ce ba a nuna mata da wuri ba ba lalle ta samu ɗinki ba har tana cewa ai irin wannan in an san za a yi sai a fiddo shi tun kafin in haihun. Munnira na ba ni labarin amsar da ta ba ta sai da na yi dariya wai su yanzu suka ga damar fiddawa kuma ba dole a ka ce sai ta yi ba daman fita haƙƙi ne. Na yi dariya sanin halin Munnira da ba ta barin ta kwana. Har Naja tana ta ya ƙawarta kishi ba ta yi ankon nan ba, ba domin ya gagare ta ba Anty Zabba ba za ta samu zuwa ba amma ta ce mini zan ga saƙo in sha Allahu. Su a tunanin su sunan da zan yi duk na salon na saka ɗan'uwan su kashe kuɗi ne domin Anty Bahijja ma ta furta a can gidan Nene a na jibi suna Suwaiba da ta zo ta ke faɗa mini, ni ko na ce ya ba ni kuɗi da kayan abinci amma sauran hidima tawa ce ba hannun Yallaɓai a cikin shi. Ni Halima ce ma ta ke ƙara ba ni mamaki sau ɗaya ta zo mini barka shima ba ta wani daɗe bs ta yi tafiyarta. Na tuna lokacin da nake zuwa gidanta na ci uwar aiki amma yau ni ce banza a idanuwanta Gimbiya ce gwana. Na yi kyafci a cikin zuciyata domin na saka ma raina akwai ranar da in ta mu ta haɗo mu sai na yi mata wankan tsarki da za ta gane ba ta da wayau.
Tun ranar litini da ya kama ana goben sunan Yumna gidana ya ɗinke da baƙi. Daman tun da na haihu na ce Yallaɓai ya koma wajen Gimbiya ya ce bai ga dama ba sai jiya ne ya tafi can amma ban sanin masa ko zai dawo bayan suna ba amma ni dai na ce masa ya koma gidanta har sai na yi arba'in ya ce ban isa ba. Amina tun safe suka sauka ita da Farida tare suka haɗa tafiyar Marwa ma da azahar ta iso. Rahila da Ma'u da kayan su suka taho tare da yaransu daman na faɗa musu in suka zo sai an gama suna can kuma sai ga Sameena sai da muka rumgume ga shi dai ƙanwar Gimbiya ce amma tana ƙaunata saboda da Allah. Daga Rano ta ke sannan ta sauka a gidana. Su Munnira daman ai suna nan sai suna ya tashi. A ranar mai ƙunshi ta zo ta yi mini saloon kuma tun safe na je shagon Amesty ta yi mini. Har su Munnira sun ce za su yi ƙunshin. Can sai ga Saude ta iso itama sai na ji daɗi su Khaleesat ne sai gobe amma Laila Ya Auwal ya ce mini ta na hanya.