← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 103

Sashe 46

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni kike yi ma kallon maƙaryaci sannan macuci tun da kin ce abu ba kyauta ba tun da na cinye kuɗin ki kuma ban buɗe miki shago ba."

"Ni fa ban ce ka cinye mini kuÉ—i ba Yallabai ka tsaya ka fahimci maganar nan don Allah"

"Me zan fahimta! Bayan wanda na gama fahimta. Wato ke dai yanzu ma kina tunanin na zalunce na cinye miki kuɗi ban cika miki alƙawari ba ko?

Ya faÉ—a yana mai tsareni da ido.

"Haba mana Yallaɓai."

"Haba ko gaskiya"

Ya faɗa a fusace ni kawai sai na yi masa shuru ganin ya harzuƙa.

"To na gode ban taɓa tunanin irin kallon da kike yi mini ba kenan amma yanzu tun da kin furta mini kuma na ji zan yi lamarin tufkan hanci. Ki faɗa mini nawa ne kuɗin ki da kike tunanin na cinye, zan biya ki kuma ba na son ki yafe mini ko naira biyar a ciki in kuma kika yafe mini to ni wallahi ban yafe miki ba"

"Yallaɓai."

Na faɗa ina buɗe baki cikin mamakin kalaman shi. Daga magana sai ciɓi ya zama ƙari duk tsawon wannan shekarun da ban taɓa masa magana duk bai ga hallacin da na yi masa sai yau ne zai ce ni ce butulu saboda kawai na faɗa masa gaskiya.

"Kuma maganar buɗe shago kuma ni na yi niyya alƙawari ne kuma zan cika in sha Allahu. Na yi kuma ranstuwa da Wallahi tallahi zan buɗe miki shagon Saloon na muka mallaka miki shi halak malak in sha Allahu Sadiya."

Sai kawai na gyaɗa kai ban ce komai ba, na mai da kaina da hankalina wajen ba ma Yumna, saboda na fahimci ko magana na sake yi ba zai taɓa fahimta ta ba.

"Nawa ne duka kudin ki da ke hannuna?

Ko kallon shi ban yi ba saboda haushi.

"Ki rubuta ki tura mini cikin satin nan zan tura miki kuÉ—in ki ba na so ki sake yi mini kallon wanda bai yi miki adalci ba."

Tsaki na so na ja masa sai na fasa ni na É—auka ma zai ce ne yau yau É—in nan zai tura mini kudin ganin yadda ya yi zuciya.

"Sai maganar Daughter kin ce wai ita da ta zo a bayan ki ga ta nan na buɗe mata shago businness ɗin ta na ta haɓbaka. To ina so na faɗa miki ko na ce tunasarwa ce tun da kin sani sai dai in kin runtse ido ne saboda wata munufarki, ko da na auri Daughter da kuɗin ta na ganta mijinta ya mutu ya bar mata gado. Da kuɗin ta da buɗe shago, ni dai na taimaka mata wajen neman shago da sauran su amma wallahi tallahi ba sisi na a cikin kasuwamcin ta ban rantse miki domin ina jin tsoron ki ba sai domin na fita daga zargin da kike yi mini na rashin adalci."

Ban san tsakin da na ke riƙewa ya fito ba sai da na ga ya kalleni cikin mamaki kafin ya ce" Ni kike yi ma Tsaki Sadiya? Ni Yusuf?

Da zan ce ya yi haƙuri sai na fasa na yi masa banza. Na gama ba ma Yunma Nono na rufe rigata na ɗora ta a saman jikina na ja key zan ta da mota Yallaɓai ya make mini hannu yana yi mini ihu a saman kaina.

"Ni kike yiwa Tsaki Sadiya? Rashin kunya za ki yi mini?

Sai kawai na koma na jingina da kujeran mota ina sauke numfashi, sai tsorata mini yarinya yake yi da ihun shi.

"Na gode kin ji ko? Tun kina yarinyarki ba ki yi mini rashin kunya sai yanzu da girma ya kama ki ko Sadiya?

Ya faɗa har ya na nuna ni sai ma ya ba ni dariya har sai da na ɗan dara shi kuma sai ya jijjiga kansa kawai bai ƙara maagana ba sai ma ficewarsa da ya yi a motar ban kira shi ba na ta da mota na zo na wuce sa, na koma gida ina ta jiran shi duk da wata zuciyar na faɗa mini ba zai dawo ba tun da ya yi fushi haka ko aka yi bai shigo gidan ba daga can ya yi gaba da man a gidan Gimbiya yake, sai washegari ne zai dawo gidana kuma har sai washegarin da dare na gan shi, haka ya shigo mini gida a daƙune ina gaishe shi da kyar ya amsa kamar na faɗa masa cuta.

Daga shi sai yaran shi ya riƙa mgana. Shi da Jidda sun kai har wajen sha biyun dare yana mata solving Quention paper na Neco wancan shekaran. Tun da sun kusa gama WEAC bai wuce paper biyu su gama ba za su fara Neco kafin babban salla shi ya sa ba ta samun natsuwa ko da yaushe cikin karatu suke yi. Ni dai ganin ba a yi da ni ya sa na kama kaina na ja jikina ni da Yumna muka shiga ciki muka kwanta sai cikin dare da na farka ne na gan shi rumgume da Yumna ni uwar Yumna tun da ana fushi da ni, ni kaina kamar jikina ya sani duk mugun barci yau ban ganganra jikinsa ba. Da safe ma haka ya yi mini wani nuku nuku da fuska ni dai ina ganin ikon Allah har ya koma gidan Gimbiya ba ma yar daɗi da shi, da farko na so na biye masa a yi zaman doya da manjan sai daga baya na zauna na yi tunanin ban kyauta ko domin tsakin da na yi masa shi zai fi tsaya masa a rai. Shi ya sa ranar da zai dawo gidana na ci kwalliya saboda ina son sulhu.

Ba ƙaramin kai zuciyata nesa na yi ba ina bashi haƙuri yana yi mini cin mgani. Kallona ya yi kafin ya ce" Uhm ni yau na ke magana Sadiya ki kalle ni ki yi mini tsaki? Haka na lalace daman a idanuwan ki?

"Ka yi haƙuri tsakin ya suɓuce mini ne."

Duk da haƙurin da na yi ta bashi bai saka ya hakura duka ba amma dai ya ɗan sassauta tun da har a daran ma ya neme ni mun yi ɓarnan ruwan da safe kuka ya tashi ya na sake yi mini cin magani ni dai na ce ai na ga ta kaina. Bai saki ba sai da ya fi sati yana yi mini isa isa daga ƙarshe dai ya haƙura don kan shi ya sauko amma ko yaya abin ya faɗo masa a rai sai ya yi ƙyafci a cewarsa ba abin da ya kai tsaki reni. Ya tsani ko wanda ya girme shi ne ya yi masa tsaƙi ballanta ni da nake ƙarƙashinsa ni dai nawa cewar ai ban haƙuri ne, ya dawo yana yi mini burga na yi lissafin kuɗina ya biya ni na yi banza da shi, daman can jin ta baki ne muna shiryawa sai shuru kuma bai ƙara ta da maganar ba. Shike nan na samu faɗan mu ya wuce sannan maganar biyan bashi dai ya sha ruwa daga lokacin da man can ba biya na zai yi ba, barazana ne kawai.

Sallar babban salla ne ke ta matsowa muna ta shiri. Daman da sallar ne muke haɗuwa gabaɗayanmu a gida wannan ma salla hakan ce ta faru an hadu gabaɗaya an yi hiran zuumci an yi wasa an yi dariya an yi faɗa an kuma shirya. In ka ganni ni da Ma'u ba za ka taɓa cewa mun taɓa samun matsala ba a baya. Ma'u ta na faɗa mini Amarya da Hajiya Zainab sun haɗa mata kai, na ce ta yi haƙuri duk ta kau da kai haɗuwa in ba ta Allah ba ce tana zaune za ta ji kan su. Duk da ta fara kwantar da hankalinta amma har yanzu Ma'u ba ta mai da jikinta ba, sannan Alhajin ya daina rawan jikin da ya ke yi a kanta a da duk in da Ma'u za ta je in bai kai ta direba zai kaita amma yanzi har ta saba yawo a cikin adaidaita. Ni da na ga ta yi fari ma na ɗauka tana da ciki ne sai da na tambayeta ta rantse mini ba ta da ciki a lokacin ma jini take yi. Marwan Ya Aina ce cikinta har ya fito ita ke gaba sai Rahila ta kunsa ƙarami.

Sai a Gwammaja muka haɗu da Gimbiya rabo na da ita tun wani zuwa da na yi gai da Nene bayan sunan Yunma muka haɗu sai da salla kuma muka sake haɗuwa. Ta yi fari ta ƙara zama wata katuwa ni dai sai na ga kamar ciki gare ta ban dai furta ma kowa ba. Da man ai ta yaye Anwar yana yawon shi ko'ina suna ganina da ga shi har Khalipa suka rumgumeni suna kiran Umma daman haka Khalipa ke kirana saboda ya ji a bakin su Jidda. Shi ya sa sai Anwar shima ya kama sunan. Nan muka yini gabaɗaya ni ban bi ta kanta ba tun bayan da muka gaisa muna ɗakin Maman farko ni da su Munnira muna ta hiran mu sai dare Yallaɓai ya zo ya ɗauke mu daman gidanta yake, mu aka fara saukewa sannan suka yi mana sai da safe suka wuce gidan su.

Nun yi babbar salla a watan june ne. Lokacin Yunma na cikin watan ta na bakwai ne har ta fara wayau tun yaushe har ina koya mata zama. Tana wayau tana ƙara zama burtuka yanzu Baby da nishi take iya ɗaukanta. Jidda tuni har sun fara Neco Baby ce kawai ke zuwa makaranta kullun ita in ba su da paper tana gida. Ta ɗauke mini komai ita ke aikin gida gabaɗaya ni sai dai kawai na ci na kwanta, Yallaɓai ya yi ta mini tsiya wai daman abin da na ke so kenan na ce to sai dai ya yi haƙuri tun da raina ya kai kuma na haifa.

Ni bai faÉ—a mini Gimbiya na da ciki ba amma tun ganin da na yi mata da salla na zargi haka. Sai da Jamila ta shigo anguwar mu wani gaisuwa gidan abokin mijinta ta shigo gidana ta ke faÉ—a mini ashe kuma Gimbiya ciki gareta? Na ce ban sani ba wallahi.
Chapter 46 · 0% Book details