Sashe 93
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gimbiya ko ga shagonta ga aiki amma duk da haka ta zauna Yallaɓai na neman kasheta da haushi. Wai tana faɗin ya fara gyaran bangaren shi bai sanar damu ba na ce ina ruwan ki? Shi da gidan shi da kudin shi? Ni ko a gefen gyalena to da Rabi'atu za ta dawo bai sanar da mu ba ranar ni ba na nan na je gidan Ma'u na duba ta tun da ta haihu ɗin ba ta ƙara lafiya ba lafai lafai ce, Gimbiya kuma tana shago yara suna makaranta danginta suka zo suka yi mata gyaran bangarenta sannan da daddare suka dawo da ita. Ni ina muka sani ba sai dai muka gan su ba kawai ni dai na shiga bangaren Rabi'atun na yi musu sannu da zuwa itama na yi mata sannu duk ta yi wani fari ta rame.
"Ai mun zo É—azu gyaran bangaren Rabia megadi ya ce duk ba ku gidan"
Kai tsaye na ce ni na je dubiya ne Gimbiya kuma daga wajen aiki ta wuce shago. Kuma ba mu san yau za su dawo da ita ba.
"Ai ko dai tun jiya ma Megidan ya so ta dawo Allah bai yi ba sai yau."
Wato kenan yana sane mu ne dai bai ga damar sanar damu ba ya yi ma kansa ruwa na kawo musu ba su ma sha ba.
"To ga Rabi'atu nan mun san ana ƙoƙari kula da ita Allah ya ba da lada."
Na amsa da Amin Gimbiya sai da suka fito haraba ta leƙo suka gaisa direban da ya kawo su ya kwashe su ya ma yar. Na koma na sake duba Rabi'atun muna ɗan yi hira kaɗan ta ji sauki sai dai ta rame. Ni dai na ga abin mamaki yarinyar nan tana jin diran shigowar mota ni ko ina zaune na ce ina jin Yallaɓai ne ai sai da na yi suman zaune saboda barikin da na gani ganin idanuwa. Yarinyar nan tana zaune amma sai ga ta kwance ta narke kamar ruwa, yana shigowa da man bangarenta ya nufo, yadda ya ganta kwance tana wani lumshe ido ko lura da ni bai yi ba ya nufeta duk ya rufe ya tarairayota jikinsa yana tattaɓa goshin ta.
"Baby me ya faru jikin ne?
Kan ki ke ciwo? Ko zazzaɓin ne?
Ya ke faɗa yana taɓa kanta da cikinta ita ko ta narke masa tana shagwaɓa kamar wata jaririya.
"Abba uhm"
Ta ke faÉ—a har da gutun hawaye, shi kuma gabaÉ—aya ya ruÉ—e.
"Me Abba ya yi? Uhm faÉ—a mini."
"Ba kai ne ba'
Kawai sai ta fashe masa da kuka cikin rawan jiki ya ƙamƙameta yana faɗin"Abba ne ko? To Abba ba zai ƙara ba kin ji ko?
ÆŠankari!
Haka na faɗa a zuciyata. Gimbiya ta daɗe tana ce mini yarinyar nan muguwar yar bariki ne ban sani ba, sai yau da ta nuna mini Umma na ke ita kuma Rabi'atu ina zaune tana abin da ta ga dama in shi bai ganni ba ita ai ta san da ni. Zuciyata ta motsa amma ban bari na zubar dakaina a gaban su ba sai na miƙe ina mirmishin ƙarfin hali.
"Mu kwana lafiya Rabi'atu."
Sai a lokacin shi ya farga da ni, ya É—an yi shock tun da har ya É—an sake ta, ta bar cinyarsa ta zauna da É—uwawunta a saman kujera.
"Umma to sai da safe."
Ta faɗa cikin sanyin murya ji na yi kamar ma juya na kamata na yi bugu. Ban taɓa jin kishinta da haushinta irin na yau ba.
"Sadiya da man kina nan zaune?
"Sannu da dawowa."
Na faɗa ban jira amsar shi na bar musu falon, duhu duhu hazo hazo na ke gani kafin na kai bangarena. Na yi shuru zaune ina tunani,ko ma me ya faru yarinyar nan da gangan ta yi, tun da ai ni da ita ne zaune muna hira, raina ya ɓaci kenan ta shirya mini wulakanci ne? Daga abin arziƙi duk abin da ta ga ina yi mata darajan Yallaɓai ne da sauke haƙƙoƙin zaman tare amna ni ai ba ta isa na koma bayan ta ba. Amma tun da ta ce haka mu zuba mu gani, ni ko zan nuna mata na riga ta zuwa duniya ita yarinya ce har yanzu. Ranar raina a bace na kwana ko Jidda ta kira ni a waya ban wani saurareta ba na ce ina jin barci washegari da safe sai ga Yallaɓai ya shigo yana yi mini kame kame ya ɗauka zan nuna masa wani abu ne ya ga bayan gaisuwa kallon musulumci ni ban yi masa ba ma shima ai munafukin ne.
Ko kunya bai ji ba yana faɗa mini Rabi'atu na son tuwo, na ɗauka zai ce ne ni na yi mata wallahi da in na fara faɗa masa mgana sai abin da na manta sai ya taimaaki kan shi ya kira Baby ya saka ta. Asabar ne ba makaranta Tahfiz kuma suna ajin bita ne yau ba ta je ba. Tun da y'arsa ya saka ban yi magana ba na yi shuru kamar zan ce ta je can bangaren nata ta yi mata sai na fasa ganin gogan yana can ya tare. Ranar ko fita bai yi ba har su Adnan gida suka zo suka same shi Gimbiya ko tun safe ta wuce Rano an yi musu rasuwa sai gobe za ta dawo shima Yallaɓai in dacewa zai yi ai ya dace ya je tun da yaron ƙanin Hajiya ce ya rasu saurayi ne ma Gimbiyar take faɗa mini to yarinya ƙarama ta saka shi a gaba har lahadi bai fita ba Baby ya samu tana yi mata wahala ranar ma da na ce ta wuce ta je Tahfiz hanawa ya yi wai ta bari wani sati kawai.
Ban yi magana ba saboda na shirya mafita na. Ranar litini da safe ya fita ya ce mini za su je Rano gaisuwa. Na ce Allah ya tsare ni da man mun tsara da ni da su Munnira Gimbiya gobe za ta dawo ranar bakwai za mu koma tare da ita amma na kira ta a waaya ta haɗa ni da Hajiya na yi mata gaisuwa. Tun ranar nan da na kama shi yana wannan ɓare ɓare jikin ya daina sha mini ƙamshi, ni ko na yi kamar ban ma gane shi ba tare suka fita da Rabi'atun ya sauke ta a makaranta ai ko ta gane ba ta da wayau sai yamma ta dawo gida ban yi kuma abinci da ita ba. Sai ga ta shigo shashena ta zauna ta ɗauka irin baya ne in ce ta shiga kitchen ga abincin ta ga na yi mata kiri ƙiri.
"Umma ba ki yi sauran abinci ba?
Kai tsaye na ce mata yau ban yi girki ba indomie ce Baby ta dafa da suka dawo makaranta. Ba su nan kuma sun tafi islamiya na samu an saka su wata islamiya anan anguwar da muka dawo ba nisa. Su Khalipa da man wajena Gimbiya ta bar su da za ta fi.
"Ki je ko yar indomoe ki sulala ki ci.'
Ta ce mini to, ta tashi ta wuce na rakata da harara ba wai haushin abin da ta yi mini ba ne a'a haushin yadda ba ta raga mini ko don karan da na ke yi mata ba.
Na yi kyafci na ce za ki gane ba ki da wayau yarinya.
Tun daga ranar na daina ije mata abinci sau biyu tana zuwa tambaya na ce yara sun cinye daga nan ta fahimci dai ba zan ba ta ba ta kama kanta. Sai Yallaɓai ya ce ba ta da lafiya ba ita iya komai amma ranar girkinta su kule ba ka jin motsin su to da man ni ce na ɗaukar ma kaina kuma na yaye Gimbiya da man yar gaskiya ce ba za ta yi ba shi ya sa bai taɓa saka ta ba.
Da Gimbiya ta dawo kamar zan faɗa mata sai na fasa kawai na share saboda kowa ya ji sai ya yi mini Allah ya ƙara. Munnira ta zo ranar jumma'a mganar tafiyar mu Gobe muka shiga wajen Rabi'atu ta duba ta. Da ya ke muna ta knoking shuru ni kuma na ɗauka ko tana salla me tun da bayan mangariba ne sai muka tura kofar tun da a buɗe yake muka shiga abin mamaki ta gyara ɗakin nan tas yana tashin ƙamshi sai na tuna ashe yau gogan yana ɗakin ta ne, sai muka zauna saman kujera muna jiran ta ba ta ji shigowarmu ba sai ga ta fito da wata shigewar riga marabanta da tsirara kaɗan ne. Ko ta yi tunanin shi ne ya dawo ko da man dai haka take yawon ta a ɗakin ta ban mu sani ba da ta gan mu ta ji kunya da gudu ta koma ɗaki ta ɗauko hijabi ta saka ta fito muka gaisa tana rufe fuska muna fita haraba Munnira ta kalleni kafin ta ce.
"Ke na taɓo ki da mgana. Wai yarinyar nan ne ta kile haka?
Ina dariya na ce" Ras. Ai Namiji ya kilar da ita."
Munnira ta riƙe baki kafin ta ce" Wallahi in ka ganta kamar ka saka mata yatsa a baki ba za ta iya cizawa ba.'
Uhm kawai na ce saboda Rabi'atu ta sauya idanuwanta sun buÉ—e ko na ce yanzu ta san daÉ—in namiji shi ya sa.
"Kin ga idanuwanta ƙif ƙif na marasa kunya yanzu."
Mirmishi kawai na yi ban yi mgana ba.
"Ba shakka Tafida ya ba ta zuma ta É—anÉ—ana. Sadiya sai ku shirya za ta haÉ—a kafaÉ—a da ku yanzu."
"Me ya rage? Ai tama fara haÉ—awa."