Sashe 102
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau amarci na ke so mu tuna, rabon da mu hada shimfiɗa da Yallaɓai sama da wata uku, kwanakin baya in ranar girkina ne ban ma cika bin shi turakan ba in ya yi magana na ce barci ya dauke ni na manta, in kuma na je babu abin da na ke yi sai barci ko ma ya neme ni sai na kawo masa ƙorafin na gaji, tun da ya fahimci haka sai shima ya ba ni lokaci amma ya shafa faɗa mini Sadiyata kin sauya, amma don Allah ina roƙon ki, kar ki sauya ni, har duniya ta tashi kar ki manta ruwa na mganin daula, shi ya sa yau na ce zan faranta mishi.
saƙo na tura masa.
"Yallaɓai na yau me kake son Sadiyarka ta da fa maka?
Na ma ɗauka bai ga saƙon ba har tsawon mintina sha biyar sannan ya dawo mini da amsa.
"Kin tuna tuwon shinkafar da kika taɓa yi mini kina Amarya? Har na yi ta gudawa? In kin tuna to ki yi mini irin shi Sadiya ta."
Da na ga saƙon shi sai da na yi dariya ina tuna lokacin. Na tuna kwana Yallaɓai ya yi yana zagayawa tiolet na zambaɗa ma miyar yaji. Rayuwa kenan.
Tuni na mike na shiga kitchen Jidda ta shigo ta ce za ta taya ni na ce ta fita ta ba ni waje, yau girkina mijina zai ci.
"Kai Umma"
"E yau dai a fita a ba ni waje ni da kaina zan yi ma mijina girki"
Jidda ta kwashe da dariya har tana kiran Baby tana faɗa mata abin da na ce suka zo suna yi mini shaƙiyan ci.
"Umma kawo mu taya ki"
"Bana son rashin kunya. Tun kafin ku zo duniya na ke dafa ma mijina abinci."
"Yau Yallaɓai sharr da shi"
In ji Baby tana dariya na yi kamar zan kai mata duka suka fice suna yi mana dariya.
Na duƙufa ina ta faman aikina ina da naman rago ga man shanu, sai da na tuƙa tuwo na je na yi salla isha'i, Yumna ta biyo ni tana kukan yunwa ta ke ji na saka Baby ta dafa mata indomie, Ammar ma yana gani ya ce zai ci su Khalipa ma suka ce yunwa suke ji, na ce su Jidda su ji da su ni dai ina ta mijina ne.
"Umma ma su miji."
Ta faÉ—a tana dariya.
"E É—in na ji "
Na faÉ—a ina murguÉ—a mata baki suka kwashe da dariya har suna tafawa da Baby.
"Mara sa kunyan yara."
Gimbiya ta shigo da man ta kan shigo a yi hira ta iske ni ina ta aiki tana tambaya Baby ta ce" Yallaɓai ake yi ma girki."
Gimbiya ta zauna gefen su Baby É—auke da Afiya tana faÉ—in" Lalle yau za mu sha gara."
"Yallaɓai kika ji an ce ba ku ba"
Na faÉ—a ina haÉ—e rai Gimbiya da ya'yanta suka kwashe da dariya.
"To Yallaɓai zai sha gara "
"Yauwa gwara da kika gyara."
FaÉ—i take yi ta zo ta ya ni na ce ta yi zamanta wannan ba huruminta ba ne ina Kicthen ina kai da kawo sun haÉ—a kai suna gulmana.
"Ku yi ku gama"
Na faÉ—a ina kyfaci sai suka kwashe mini da dariya.
Na yi banza da su na cigaba da aikina tas na lailaya tuwo a leda miya kuma ta ji nama da manshanu ga ganyen ogun da ya ke mun shukata muna da shi a gida na saka Baby ta É—ebo mini na yanka na wanke na yi amfani da shi.
Zuwa takwas da rabi na gama tun da ba da yawa na yi ba bai kai ko leda goma ba ma tuwon
Wanka na yi na shirya cikin wando plazo bakin wando da jan riga mai ratsin baƙi. Na gyara gashina da ya ke ban yi kitso ba na saka bakin dankwali na yi ɗauri da shi na feshe jikina da turare na fito falo ina tashin ƙamshi. Ihu suka saka mini yaran nan kamar wasu sa'ar su Gimbiya na ta ya su.
"Su Umma manya."
In ji Jidda.
"Umma an sha kyau.".
In ji Gimbiya na yi mirmishi na yi fari na É—au wayata ina faÉ—in" Bari na kira Yallabai na ji ko yana ina ne?
Baki suka sake suna kallona ina kiran shi ya daga.
"Uwargida ta."
"Yallaɓai na "
Na kashe murya kawai sai suka saka mini ihu sai na yi É—aki da gudu ina dariya.
"Su waye ke ihu?
"Su Jidda ne da Gimbiya suna ta mini tsiyan wai yau na ce za mu tuna da zan yi maka girki mu sha soyayya "
Yana dariya ya ce" Share su. Kazan amarci zan siyo mu ci mu sha mu kwana ɓarnan ruwa."
"Allah ya ja zamanin ka Yallaɓai na."
"Sai na iso.'
Muka yi sallama cikin shauƙi
Yallaɓai a muryan ma za ka gane yana cikin farinciki
Ɗaure fuska na yi na fito suna kallona suna kunshe dariya. Jidda Abdullahi ya kira ta ta bar falon Baby ce suke hira da Gimbiya akan tana son ta yi ma Yallaɓai mgana za ta fara koyon mota.
"Na ji yana mganar kuwa. Ki tuna masa."
"To Anty in sha Allahu."
Kusa da Baby na zauna muka saka ta a tsakiya muna ta hira. Gimbiya ta ce Rabi'atu fushin ne har da mu?
" Mijin ki ya jawo mana."
Mijin ki dai."
Gimbiya ta mayar mini da amsa dukkan mu muna dariya.
Kamar wasa sai ga Rabi'atun ta shigo ita da Salima ina jin gajiya ta yi da zaman shuru yaran duk suna nan shi ya sa ta fito.
"Umma barka da dare. Sannu Anty Gimbiya."
Ta faÉ—a tana zama a kan kujeran da ke fuskantan mu
Muka amsa mata cikin sakewa, ni dai ce na kara da cewa ta gama fushin ne? Sai ta rufe fuska tana dariya.
"To mu da ba laifi ba an share mu."
Na faÉ—a ina dariya.
"Ni fa ba na fushi."
"To mene na É—auke mana? Kwana biyu kenan ko hira ba kya fitowa.'
Sai ta ce ba ta jin daÉ—i ne muka yi mata fatan sannu hancinta ta bude kafin ta ce Umma na ji kamshi me kika dafa mana ne?
Kafin in yi magana Baby ta ce tuwo ne mai daɗi amma na Yallaɓai ne"
Rabi'atu ta ce" Umma wallahi ina son ci ki taimaka."
Ba ni da yadda zan yi na ce ita za ta ci Gimbiya ta ce itama sai ta ci na sawo musu ya'yansu suka ta so suma sai sun ci.
"Ah ku na yi ma girki kawai."
Na faÉ—a ina tura baki.
"Na mijina ne fa."
Na sake faɗa ina riƙe haba.
"Umma ki ba mu kawai mu cinye Abba ya sha tea ya kwanta."
Jidda ta fada bayan ta dawo falon.
"Ba ku isa ba"
Muka ji muryan Yallaɓai daga sama ba ma wanda ya ji shigowarsa yaran na ganin shi suka ruga suna oyoyo Abba.
"Jidda haka za mu yi da ke?
Ya faÉ—a yana karisowa falon
Baby ta tarbi ledan hannun shi guda É—aya ya sakar mata É—ayan kuma ya ce" Wannan na ku ne ku da iyayen ku. Wannan kuma na My Sady ne."
Sai Jidda da Baby suka saka dariya.
Gimbiya ta ce" Son kai dai kake nuna mana kamar yadda itama ta nuna mana yau."
"E É—in an nuna muku son kai É—in."
Ya faɗa yana zama a gefen Rabi'atu da take zaune a ƙasa tana cin tuwo Afiya na miƙa hannu sai ya ce A kawo masa ita Yumna ta mike ta ɗaukota.
"Yauwa my super women É—ina."
Haka yake kiran Yumma a cewarsa tana da karfi.
Sannu da zuwa muka yi masa gabaÉ—aya ya amsa yana kallon mu É—aya bayan É—aya har yaran yadda suka ba je a falo suna cin tuwo.
"waye ya yo gayyar a cinye mini abinci."
Ina dariya na ce masa Rabi'atu na bashi labarin kwaÉ—ayi ya sa ta jiyo kamshi ta bar fushin ta shigo.
"Ai da man cikin nan nata akwai son daÉ—i"
"Abba wallahi tuwon ya yi daÉ—i ka ce Umma ta karo mana "
In ji Rabi'atu
"Ni kuma sai ma ci me?
"Ka sha tea mana."
"Hararanta ya yi kafin ya ce" Ke ki sha tea ɗin mana. Na ki wayau wanda kuka ci sabil ne"
Na ce ƙwarai, dole suka haƙura aka ba je kajin da tsiren da Yallaɓai ya siyo suna ci suna hira, Yallaɓai ya miƙa ma Gimbiya ɗiyar ta ya miƙe yana faɗin.
" Sadiya ta mu je kin ji."
Ya fada har yana miƙo mini hannu na kama yaran nan suka saka mana ihu.
"Kuna fita za mu cinye tuwon nan"
In ji Gimbiya Yallaɓai na jin haka ya ce" To koma ki haɗo komai ki same ni a can"
Ya wuce ya fita bayan ya ba ni ledan hannun shi. Na koma kitchen na hada ƙomai a saman ƙaton faranti na saka lulluɓi na fito ina faɗin" Jama'a mu kwana lafiya."
"Mu kwana lafiya Uwargidan Yallaɓai."
In ji Gimbiya Rabi'atu dai ba ta yi mgana ba ita har gobe ba ta iya boye motsuwar kishinta.
"Umma sai da safe"
In ji Jidda na amsa ina faÉ—in su rufe kofa in za su kwanta.
Yumna ta biyo ni tana faÉ—in" Umma nima za ni wajen Abba"
Yarinyar nan shegen wayau ne da ita haka nan na rasa yadda zan yi da ita da na ce Jidda ta kamata ma kuka ta saka haka nan na ta sa ta gaba muka tafi. Ko da na je har Yallaɓai ya shiga wanka sai na kunna mata cartoon ni kuma na shirya mana dining sai da na kira wayar Jidda na ce su kawo min kunin aya da na haɗa yana nan a fridge da Baby ta kawo ne na samu na yi ma Yunma wayau na ce ta ma yar mini da mayafina ganina nan zuwa.
Sai da na gama shirya komai a falo sannan na shiga ciki na samu Yallaɓai ya fito wanka yana ɗaure da babban towel a ƙugunsa.
"Sadiya ta."
"Yallabai na."