← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 103

Sashe 57

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daran Yallaɓai da ya dawo ya gani ya ce sai na kwace mata wai an ci zalin yarinya don an ga ba ta mgana tun ballanta da take ta kuka shi a tafau zafin kan ne ya saka ta kuka tun kuma daga ranar ya ce ba za a ƙara mata kitso ba sai ta girma an yaye ko sai kanta ya yi ƙwari. Sanin halin Yallaɓai da naci wani lokacin in har aka sake kuma ya gani ni ce zan sha mgana sai kawai na ƙyaleta ban ƙara yi mata ba, amma kowa ya ganta sai ya ce ga ta da gashi amma ba a yi mata kitso sai na ce babanta ne ba ya so. Daga karshe ma sai na sissiya mata huluna kananun size kamar nata, na ke saka mata in zamu fita yau ma kalan ja mai maroon, na saka mata na rufe mata kan ta da shi, sannan na je ɗakin su Baby na ɗauko mata kaya a cikin dirowanta. Shadda na ɗauko mata doguwar riga da ƙaramin mayafi. Hauwa na tsaya ina ta jira sai wajen azahar ta shigo gidana shi ya sa sai da muka tsaya a gida muka yi salla sannan muka fito na rufe gida na tuƙa mu a mota ta, sai da muka tsaya a kan hanya na sha mai da safe Yallaɓai ya saka mini 5k ya ce na saka mai a mota, wani lokacin ma Adnan zai turo ya ɗau motar ya je ya saka mini wata rana ma da kan shi zai tura ya je ya ciko mini da tankina ya kawo mini. In ba lokaci kuma sai kawai ya ba ni kuɗin amma ba ko yaushe ba wani lokacin ina sakawa da kudina. Ai ya gama yi mini mai wuyar tun da ya siya mini motar. Na man da zan yi zirga-zirga na a cikin gari ba zai gagare ni ba.

  A gidan man kafin layi ya zo kanmu na kira wayar Salisu na sanar da shi in ya ɗauko Baby daga makaranta gidan Maman su Khalipa zai kawo ta. Sai ya ce mini to, a bakin shi na ke jin ashe su Khalipa ba su je makaranta yau ba. Hauwa na ke faɗa mawa ta yi dariya kafin ta ce" To da man ai ba za su je ba. Suna fa ake yi sunan ma na gidan su."

Ban ce komai ba, illa Yumna da nake kallo wacce ke hannun suna ta wasa da yaron Hauwa. Ita har ta yaye shi ma yana neman shekara uku ne ma. Munnira na tuna shi ya sa na kalli Hauwa kafin na ce" Wai kina ganin zuwan Hadiza ba zai hana Munnira zuwa gidan sunan nan ba kuwa?
Na faɗa ina kallon Hauwa. Domin na kira wayar Munnira da niyyar na ce mata mu haɗu a gidana sai mu wuce gabaɗaya. Sai ce mini ta yi mu tafi kawai ƙanwarta Hadiza ta zo daman mun yi ta ɗin da ita tace mini ta zo garin da yake a garin Minna take aure. A yau ɗin ne ta kai ma Munniran ziyara.

"To wa ya sani. Ina jin kamar fa Hadizan nan gidan Munniran za ta kwana "

Hauwa ta amsa mini daidai lokacin layi na zuwa kan mu sai ban ba ta amsa ba sai da na yi mgana da mai zuba man na faɗa masa na adadin da zai zuba mini ina da kuɗi a jaka ta, sai na bashi sai da muka bar gidan man muka ɗau hanyar sharaɗa sannan na kalli Hauwa kafin na ce" Wataƙila nan za ta kwana. Kila su zo tare in ta yi niyya ba."

"Ai fa. Ta bakin ki in ta yi ra'ayi za ta jawo ta su taho tare"

Muna tafe muna hira ni da Hauwa har gidan Gimbiya. A waje na yi parking ɗin motata tun da ga na wasu nan duk a wajen, har da na Anty Bahijja na gani da man na san ai tana gidan tun safe. Gimbiya ce fa ballantana tana dukan ƙirjin cewa an sake yi musu farar haihuwa. Mun shiga gidan ina ɗauke da Yumna da jakata da key ɗin motata. sai Hauwa itama riƙe da goyonta ita ta ɗauko ledan kayan Baby da saƙon Gimbiya tun da ita ba ta ɗauko jaka ba.

Gida fa cike da baki, ashe har anko sun yi ba mu sani ba, ba wanda ya nuna mana. Ni da Hauwa muka kalli juna amma ba mu yi magana ba. Marwa ne da Ashe suka tare mu shi ya sa ma muka saki fuska sun sauka tun É—azu. Ashe har tana yi mini tsiya.

"Anty Sadiya sunan na ku har da anko kuka fitar amma ba labari "

"Nima yadda kika gan shi haka na gan shi."

Na faɗa ina dariya da yake tana da barkwanci ne ita Aisha. Ashe su Hauwa ke kiranta, lokacin sunan Yumna ba ta da lafiya ne shi ya sa ba ta zo ba, karɓan Yumna ta yi, ta fara ƙoƙarin yi mata kuka da sauri ta ce" Ke ƙaniyarki nima uwarki ce."
Ni da Hauwa muna ta dariya. Mun gaisa da Marwa na dauƙi Afra ina faɗin ta yi mini girma a ido sosai ba kamar ganin ƙarshe da na yi mata ba.

"Umma ta kusa wattani shidda fa?

Sai na buÉ—e baki ina faÉ—in" Lokaci ba wuya. Allah ya sa mu da ce."
Ta amsa da Amin tana dariya, Baby ta tambaya na ce tana makaranta amma in sun dawo nan za a kawo ta na ma taho mata kayan da za ta sauya.

"Su Jidda ana can makaranta ko?

"Wallahi tana can. Yau ma dai ba mu yi waya ba."

"Allah ya ba da sa'a."

Duk suna falon ne, tare da sauran dangin Gimbiya na Rano. Ban ware su ba na bisu muka gaisa cikin sakewa. Su Anty Bahijja da Naja ana ta kai da kawo su leshi ne a jikinsu iri É—aya ina tunanin anko suka yi.

"Barka da aiki Anty Bahijja an yi suna lafiya?

Na faÉ—a lokacin da ta zo wucewa. Waigowa ta yi sai ta nuna kamar yanzu ta gani alhalin ni na san tun shigowata ta gan ni har ido ma mun haÉ—a da ita.

"Sadiya ce! Sai yanzu za ki zo mana Suna?

Ina mirmishi na tashi na isa wajenta ina faɗin" To ka ga ku Anty Bahijja ai ba sai mun yi samakko ba, kuma dai kin ga na tsaya na shirya angon ƙarni a gida ne kafin na fito "

"Gaskiya ne. Ina Yumna?

"Tana hannun Marwa"

Na bata amsa sai ta ce na shiga ciki mana, ta waiga ba ta ga Munnira ba sai Hauwa tun da har sun gaisa.

"Ina É—ayar yar tawagan na ki?

Sai da na yi dariya kafin na ce" Ta yi baƙuwa ƙanwar ta, ta zo kila anjuma ta leƙo "
Sai ta wani jinjina kai kafin ta ce" Kina dariya karya na yi ba yan tawagan ki ba ne? Duk wanda ya ce miki kule sai sun ce masa caass."

Ni dai ina ta dariya ban yi magana ba, na tuna can kwanaki Mubeena ta taɓa faɗa mini Anty Maimuna ta ce wai tsoro na su Hauwa ke ji, sai abin da na ce shi suke yi shi ya sa duk in da nake suna bina a baya. Ni kuma na san haushi suke ji saboda suna tare da ni. Sai na jujjuya ina neman Mubeenan ban gan ta ba, wata kila ba ta zo ba ne, Anty Bahijja ta ce na shiga ciki Gimbiyar na ciki tare da ƙawayenta.
   
Na kama hanyar Bedroom ɗin da Gimbiya ke ciki muka haɗu da Naja, ta gaisheni na amsa ina tambayan ta ya hidima ta ce sun gode Allah. Daga nan na shiga ɗakin Gimbiya dake cike da kawayenta da ƙannenta har da yayyenta. Da fara'ata na shiga aka gaggaisa nan na ga autar su Gimbiya Maryama da ke aure a can Lagos ba ts cika zuwa ba na dai ji labarinta amma ban taba ganin ta ba sai yau, ni na fara yi mata mgana amma sai na ga tana amsa ni a fuzge ban bi ta kanta ba na isa gefen gado kusa da Gimbiya na zauna muna gaisawa ta ci shadda pink ta ji aiki an yi mata makeup ta yi ras da ita.
Suma ƙawayenta sun sha kwalliya sun sha anko.

Gaisawa muka yi ta ba ni Muhammad na É—auka shima an yi masa gayun su na yara da kaya masu kyau da tsada.
"Allah Ya raya mana Muhammad"
Na faÉ—a sai ta amsa da Amin Amin.
"Ina Baby? Ko ta je makaranta ne?
"E ta tafi. Amma na kira Salisu zai kawo ta nan, tun da na zo mata da kayam da za ta saka."

"Ayya. Su Jidda ana can makaranta. Ta kirani da safe muka gaisa ta ce Anty wani suna za mu riƙa kiran Muhamnad na ce ta saka masa suna cikin sanyin ta ta ce Anty Ammar ya yi?
Ina dariya na ce" Ta ko iya zaɓan suna. Allah ya raya Muhammad(Anwar)"
Aka amsa da Amin gabaɗaya da waɗanda ke gefen mu suna jin mu. Ina nan zaune sai ga Hauwa ta shigo sai na matsa mata gefena tazauna ta mika mata Muhammad, sannan na karɓi ledan sakonta na mika mata ta karɓa tana faɗin.

"Ba kya gajiya Madam! To na gode Ammar na godiya Allah ya saka da alheri "

"Haba ba yawa fa. Amin"

Yumna ta tambaya na ce tana wajen Marwa, yarinya Marwa ɗin ma ta yi barci nan saman gadom Gimbiya na kwantar da ita. Har ita Gimbiyar sai da ta tambayi Munnira wai ya ta gan mu mu biyu daga ni sai Hauwa na yi dariya na ce ta yi baƙuwa ne amma za ta taho daga baya. Mun saba in dai wani abu ne a dangin mazajen mu to mu uku suke ganin mu. Kowa ya san ni da su Hauwa mun zama aminai ne ba facaloli ba.
Chapter 57 · 0% Book details