Sashe 64
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To na ji daɗin haka. Allah ya sa. Allah ya yi muku albarka addu'ata a koda yaushe ya zaunar da ku lafiya sannan ya yalwata ma mazajen ku samun su yadda za su riƙe ku bisa gaskiya da amana."
.
Na amsa da Amin kafin na yi tambayar da ke sosa mini rai.
"Alhaji me Rahilan ta yi ma Ya Muntari?
"Ina ruwan ki? Wannan tsakanina da ɗana ne. Ya faɗa mini kuma na sauke haƙƙi na kirata a wannan falon na yi mata faɗa ta yi mini kuma alƙawarin ta daina. Kamar yadda kema ba zan yi taɗin nan da kowa ba itama ba zan zo ina faɗin rashin kyautatarwarta ba. Ni kamar alƙali ne shi kuma alƙali ana son shi da gaskiya da rike sirri "
"Ai ni za ta faÉ—a mini Alhaji"
Na faÉ—a ina mirmishi shima mirmishin ya yi kafin ya ce" Wannan shima dai duk tsakanimku ne. In ta faÉ—a miki ba ta yi laifi ba. Domin tare kuka tashi kuka girma, akwai sirrukan masu yawan da zaku tattauna a tsakaninku na yan uwa."
"Haka ne Alhaji."
"To kin gani. Allah ya yi muku albarka gabaÉ—aya. Tashi ki je ki samu wani abu ki ci sannan ki kwanta da safe ki koma É—akin mijinki ki tallafi yayanki. Ke da kika kusa kai ga suruki Dubu amaryata da na saka ana can jami'a ana ta karatu ko?
Ina dariya na amsa masa" E Alhaji amma ai ta ce ba ta ssku ba auranku na zoɓe ne."
"Manta da ita, ga matata ta gaskiya me zan yi da ta roba?
Amma dai ina nan ina jiran ta a falon nan ta kawo mini suruki na ga ko na fishi dogon hanci."
Me zan yi in ba dariya ba, da man shi Alhaji dariyan ya ke so na yi. Ya sallame bayan ya ce na ce Marwanatu ta zo su gaisa ita da wannan yarinyar na ta mai kukan tsiya duk ta cika masa kunni.
Na fita ina dariya na koma ɗakin Gwaggo na iske su suna ta hira na faɗa mata saƙon Alhaji sai ta sunkunci yarta ta fuce tana faɗin" Shi ta ke jira ya lallasheta."
Bayan fttan ta Gwaggo ba ta matsa mini sai ta ji yadda muka yi da Alhaji ba amma dai na faÉ—a mata zan koma saboda Yumna.
"E gaskiya ya kamata baiwar Allah na san za ta sha kuka."
"Wallahi Gwaggo Nonuwana har sun fara tasawa."
"Wayyo sannu. Ko za ki sha panadol ne in kin ci abinci."
"To Gwaggio"
Ita ta kawo mini abincin Tuwo ne miyar kubewa bushasshiya. Na ci da yawa muna hira ban gama ba Marwa ta dawo ta ce ma Gwaggo ta je ta ba ma Alhaji Tuwo kafin ya suma saboda Yunwa.
"Ai da man ke ce kika tsayar da shi, amma shi uwarhaka ai ya koshi ya kwanta."
Muna ta dariya ta fice ta bar mu, Marwa ta zauna muka ƙarishe cin tuwo da ita ta fita da kwamukan ta ɗibo mana ruwa na sha mgani da shi.
Akwai katifa a É—akin Gwaggo ita Marwa ta shimfiÉ—a za ta kwanta ni kuma na ce ina gado
Na yi mata sai da safe ganin waya a hannunta sai na yi tunanin mijinta za ta kira.
Har na juya ta kirani.
"Umma."
Na juyo ina kallonta.
"Za ki koma ko?
Sai da na yatsina fuska kafin na ce" Alhaji ya matsa. Zan koma gobe in sha Allahu."
Sai ta kama murna. Na yi shigewata na bar ta. Kayan jikina na cire, na samu wata rigar Gwaggo ta makka ce Ma'u ta kawo mata ita da daÉ—ewa lokacin da mijinta ya koma. Gwaggo a lokacin ta ce ba ta so wai na yara ne muka matsa mata ta karba. Ashe za ta yi mini amfani ita na zuba mai taushi har kasa na É—aure kaina dakallabi na haye gadon Gwaggo. Na daÉ—e ban yi barci ba kewan gidana kewar 'Æ´ayana da mijina. Su suka taru suka yi mini rufdugu na yi ta juye juye sai can barci ya kwashe ni har ina makara sai da na ji Gwaggo na kiran sunana.
Sannan na iya tashi na je na ɗauro alwala na yi salla nonuwana sun yi mini nauyi sun kwana a ba tsotsa ina jin kamar zazzaɓi zai kama ni amma haka na fita na share tsakar gidan nan tas na haɗa wamke-wanke Marwa ta karba sannan na je na gaida Alhajinmu ƙara jadadda mini yake yi da na ƙarya na shirya na koma gidana. Ni dai ba ni da ta cewa daman ai dole na koma ko domin Yumna amma a kasan zuciya ina cewa ba don halin Yallaɓai ba shima.
Ɗumamamman tuwon jiya muka ci da safe, na ƙara shan panadol na kwanta da niyar na dan runtsa barci ya sarkeni, tun wajen tara na kwanta ni ce sai wajen sha ɗaya na tashi. Shima ɗin tada ni Marwa ta yi wai tana faɗa mini ga su Kawu nan.
"Wani kawun?
Na faÉ—a ina mitsike idanuwana masu cike da barci
Kafin ta samu zarafin magana na ji kukan Yumna ai da sauri da diro daga saman gadon Gwaggo a ƙofar falo muka ci karo da Baby ɗauke da Yumna tana ganina ta rumgumeni tare da Yumma tana faɗin" Umma mun yi kewarki jiya. Yumna ta kwana kuka Abba ne ya yi ta lallashinta yana ta ba ta tea"
A zuciyata na ce da kyau na ji daÉ—i da ya É—anÉ—ana.
Ture Baby na yi baya kaɗan ina karɓan Yumna wacce ke ta miƙo mini hannu tana faɗin Uma.
Da sauri na karɓeta na rumgumeta ni da ita muka sauke ajiyar zuciya kamar mun shekara ba mu ga juna ba..zama na yi a saman kujera na fara ba ta nono. Allah sarki baiwar Allah ta karɓe da sauri tana sauke numfashi. Ina shafa kanta ina mai jin tausayinta. Sai na ga an yi mata wanka itama Baby ta yi wankanta.
"Ba ki je makaranta ba?
"Umma mun fa makara. Abba bai yi barci da wuri ba sai 7:30am muka tashi fa."
Ta faÉ—a tana kirga mini da hannunta.
"Uhm wa ya yi ma Yumna wanka?
"Abba mana. Ni kuma na yi da kai na shi ya soya mana doya da kwai Umma."
"Ya kyauta."
Na faÉ—a ina jinjina kai Marwa na kalla ganin tana ta shiri alamun kamar ta yi wanka ne.
"Gida za ki leƙa?
"A'a tafiya za mu yi"
"Ke da wa?
"Ni da Kawu mana. "
Sai ta ga na yi shuru ina kallonta sai ta yi dariya kafin ta ce" Umma ni da Baban Abadallah."
Sai na ware ido kafin na ce" Ya zo ne?
"Ya zo tun dazu tare muka zo da shi da Abba."
Baby ta fanshe ta sai na fara tunanin ko wa ya faÉ—a ma Kawu ko kuma dai ya zo É—aukan Marwa ne bai san abin da ya faru ba sai yau.
"Ni ba ruwana. Nima da safen nan ya ce mini zai zo Abban Jidda ya yi masa waya akan kum samu matsala."
"Uhm"
Kawai na ce na cigaba da ba ma Baby Nono Jidda na ta yi mini surutu na yi kamar ban jiba. Wayata na gida ban san adadin waÉ—anda suka kira ni ba. Ba daÉ—ewa muka ji muryan su a tsakar gida sai ga Gwaggo ta shigo da hijabinta tana faÉ—in"
"Ki ta so ta..'"
Ganina a zaune sai ta ce" Au ashe kin tashi? To maza ki shirya ga mijinki can na jiran ki."
Baki na tura kafin na ce" To ban yi wanka ba zan tafi Gwaggo "
"Ba gidan ki za ki koma ba? In kin je can sai ki yi. Maza tashi kafin Alhaji ya ji ya leƙo da kansa kin san halin shi."
Ba ni da yadda zan yi haka nan na yanke ba ma Yumna Nono Gwaggo ta karɓeta tana yi mata wasa.
Kayana na je na saka na ɗauko hijabina na saka. Baby tuni ta fita wajen babanta Marwa na yi ma magana ko yanzu za su wuce ta ce zai kaita gida ta gai da Ya Aina. Amma kafin su wuce za ta biyo gidan tun da akwai kayanta a can na ce mata toh. Na karɓi Yumna hannun Gwaggo na shiga yi ma Alhajin mu sallama.
"Allah ya yi miki albarka. Mijinki ya yi ta bani haƙuri sharrin shedan ne Allah ya tsare na gaba.'
Na ce Amin sannan ya yi ma Yumna wasa, har yana ba ta 500 ya ce kuɗin zance ne. Na karɓan mata ina masa godiya. Koda na fita kofar gida suna jikin motar Yallaɓai shi da Kawu suna mgana amma kowannen su da motar shi ya zo. Baby na cikin mota da alamu ni suke jira.
Ba domin Kawu ba wallahi shigewata mota zan yi amma saboda shi na tsaya ina gaishe shi.
"Lafiya lau Surukata. Ashe kuma abin da wannann mara mutumcin ya yi miki kenan?
Sai na kasa magana amma na kauda kaina bana son ma mu haɗa ido da Yallaɓai.
"Ai da kin kirani wallahi sai na shigar miki. Amma ko yanzu na yi mata faɗa na ce kuma ya gode ma Allah ma ya samu surukai na gari in wani ne Alhaji ai ko kallon sa ba zai yi ba. Maimakon haka ma sai ya karrama mu, muna bashi haƙuri muma yana ba mu."
Nan ma na yi shuru kaina na kasa, Yumna ce ma ke miƙa ma Yallabai hannu tana faɗin Aba da sauri na janyeta ina ƙara haɗe raina.
"Ki yi haƙuri kin ji ko? Fushi ne da shedan suka yi tasri a kan shi amma ya tuba ya ce ba zai ƙara ba."
Sai na ɗan kalle shi ta gefen ido kansa na ƙasa yana ɗan mirmishi kamar ba shi ne ya yi mini wulakanci ba jiya.
"Ba komai. Allah ya kyauta na gaba.'