Sashe 85
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk sai hankula ya dawo kan mu, Rabi'atu kanta na ƙasa sai mirmishi amma ba ta mgana. Hauwa na ce ma ga amana nan bar mata zan je na dawo sai ta ce ta karɓa ta dawo kusa da Rabi'atu tana faɗin" ƙyalesu ƙanwarmu."
Munnira ta daddage ta saki guɗa tana dariya, ni ma dariyan na ke yi, Gimbiya na gefe ita da Halima kamar su mutu saboda baƙin ciki. Amma ba halin mgana.
Ciki na shiga in da dangin Amarya suke na ga suna ma zuba abincin wata cikin su na yi ma mgana ina son alele, sai ta ce mini haba bakomai ta samu filet ta saka mini guda huɗu sai da na ce ta rage za ta sanya mini nama na ce wallahi ta bar shi, wannan ɗin ma sha'awa ce wata ƙanwata ke so.
"Allah sarki hala kwaɗayin ƙaramin ciki ne?
Sai na yi dariya kafin na ce" Muna dai saka ran haka"
Sai itama ta rakani da dariya sai da ta faɗa sai na yi jim a zuciyata ina tunanin ko dai an samu rabon ne? Amma kuma ban ga alamun ciki a wajen Rabi'atu ba da man na san ta akwai son alale ko ni in na yi har ajiyewa take yi. Itama tana yawan yin shi sai na cire tunanin haka a raina. Na fito falon dai dai ana cewa mu ta shi mu tafi, tun da mun rako amarya gida fa kamar ba shi da yake sun yi jeren su da wuri Gimbiya kafa ɗaya kan ɗaya kamar falonta ta manta ya tashi daga falonta yanzu ya koma na wata.
Kowa ya ganni da alele bai yi nagana ba sai Anty Maimuna tana tambaya ta ni kuma kai tsaye na ce" Rabi'atu ke so shi ya sa na samo mata.".
Matar nan ba sai ta fara faÉ—a ba.
"Miye haka? Ta son tana so tun a can ba ta yi magana ba sai da muka zo nan?
"Renin wayau ne "
In ji Halima.
Anty Bahijja na can gefe tana waya tana gamawa itana ta zo aka faɗa mata ba ta bi ba a si bq sai ta ara ta yafa wai wulaƙanci mu zo da abinci daga gida amma mu koma muna roƙo saboda zubar da kai.
Sai Rabi'atu ta ba ni tausayi sun ta so mata, cikin rawan murya ta ce" Ban san an yi alelen ba ne sai yanzu na gani raina ya biya. Ku yi haƙuri "
Ta faÉ—a kamar ta fashe da kuka har ta ma fara hawaye. Sai Anty Maimuna ta fara faÉ—in"To daga mgana sai kuka?
Ta faÉ—a cikin mele baki ni kasa ma mgana na yi, na ba ta alalan baiwar Allah ta ce na ma yar ba za ta ci ba.
"Karɓi abin ki me zai hana ki ci?
Sai ta yi shuru. Suwaiba ta ce na samu leda na saka mata in mun je gida ta ci amma yadda aka taso mata yanzu za ta ji ya fita ranta ne.
Sai na yi haka na koma na tambayo leda a ciki aka bani mai girma na juye mata alalan ina fitowa da karfi Anty Bahijja ta kira sunana gaban mutane har da waɗanda ba ahalin mu ba. Na amsa mata duk da na san kiran ba na arziƙi ba ne.
"Ke wai ba za ki kama girman ki ba ne, ji yadda kike rawan jiki a ƙan ƙaramar yarinya?
Sai na buÉ—e baki amma na ma kasa mgana.
"Ai ba da ita ya kamata ki haɗa kai ba. Gimbiya ce dai da ke sai ita data ke ƙarama ta bi bayan ku amma abin da takaici ji yadda kika ma y'ar da kan ki baya a kan yar cikin ki, domin ko za ta girme ma Jidda da kaɗan ne."
Na ji na muzanta amma ban bari ta fahimta ba sai na yi mirnishi kafin na ce" Ai kema kin ce sa'ar y'ata ce. Shi ya sa sai nake yi mata kallon ƙanwa. Kuma maganar na ma yar da kaina baya ba haka ba ne, ni ina daraja wanda ya san ina da daraja, da Rabi'atu da Gimbiya duk ɗaya suke a wajena. Tun da matan Yallaɓai ne, abin da za ki fahimta wanda ba ya yi da kai ba za ka takura shi sai ya yi da kai dole ba. Wanda kuma yake yi da kai kar ka kwabe masa ƙokarinsa ka ta ya sa nuna girman karramawan da ya yi maka."
Sai na dakata ina kallon Anty Bahijja kafin na sake yin mirmishi na ce" In dai wannan shi ne kike kira na zubar da kaina na yarda ki yi ta É—auka a hakan."
Jamila ta kada baki ta ce" Ni ban ga abin ceceku ce a kan wannan maganar ba wallahi ina laifin yarinyar nan? Duk in da Sadiya ta yi tana biye da ita sai kawai ta wulakanta ta! Haba Anty Bahijja kuma ai ba komai za ku rika mgana ba "
Jin kowa ya taso yana mgana yasa sai ta yi shuru. Baiwar Allah har sun saka ta kuka. Yumna ce ta je wajen ta hau jikinta ta ɗauketa shi ne ma ta daina sharan ƙwalla duk sai na ji ban ji daɗi ba. Gimbiya sai taɓe taben baki da fuska take yi amma ba ta yi magana ba, daga nan Gwamaja muka koma, Sadi na kira ya zo ya kai mu gida Yallaɓai na can tare da su Kawu, Gimbiya sai daga baya ta dawo kamar Direban Naja ne ya mai do ta.
Na yi ta ba ma Rabi'atu haƙuri da ta ce ba za ta ci alalen ba.
"Karɓi abin ki ki ci, haka suke kin san kowani dangi suna da na su matsalan. Sai kin kauda kai akan maganganun Anty Bahijja ko Anty Maimuna. Gimbiya kuma tana gaba dake so karki ɗauka da wani abu. A hankali za ki saba."
Sannan ne ta karɓa, kuma na ga hankalinta tun da har kwana biyu da faruwan abun ban ji Yallaɓai ya yi magana sai na tabbatar ba ta faɗa masa ba. Jidda ranar laraba ta koma makaranta laraban ma da ta kai ni ce na saka baki da litini tun safe Yallaɓai ya ce ta koma na ce ya barta ta ɗan yi wanki da sauran shiri, sannan ya amince. Tun bayan bikin Adnan kuma sai na natsa a gida ba in da nake zuwa. Gimbiya tana fita shago ko wajen aiki Rabi'atu kuma makaranta ita da yara ni kaɗai ce ake bari ina gadin wannan wargajejen gidan.
Su Inna Mariya da iyalan Gandun albasa sun zo mini ganin gida gabaɗayansu sun saka albarka kuma wallahi na ji daɗi. Suma dai nasihan su na yi haƙuri na zauna lafiya da abokan zamana domin samar ma da mijin mu kwanciyar hankali na ce In sha Allahu.
Gimbiya ce ta fito da tsarin kwana É—aya amma daga baya sai ta ce wai ba ta ganewa mu ma yar da shi kwana bibbiyu.
Har falona ta zo ta sameni wata ranar asabar da safe. Baby da su Khalipa sun tafi Tahfez Yumna ce kawai ita kuma tana shashen Rabi'atu wajen Yallaɓai da safe da ya shigo mu gaisa ta dafe shi.
Kallonta na yi cikin mamaki ni da man na san tun da na gan ta a falona na san banza ba ta kai zomo kasuwa.
"Kwana É—aya nan gaskiya bana gane mishi. Mu koma biyun kawai Maman Jidda."
Ta sake faÉ—a sai na yi dariya kafin na ce" Ba matsala da man ni biyun na ce ke ce a baya kika ce mu ma yar da shi É—aya."
"Gaskiya mu dawo biyu nan É—ayan nan bana gane mishi."
Sai da na sake murmusawa sannan na ce mata shike nan.
"Za ki faɗa ma Baban su Khalipa ne? Yau ba Daddy su Yallaɓai an koma Baban su Khalipa na fahimci tunda ya yi auren nan ta daina kiran shi da Daddy sai da Baban su Khalipa."
"Ina ruwan shi? In dai duka mun amince shi ba shi da matsala kin sani "
Sai ta gyaɗa kafin ta miƙe tana faɗin" To sai ki faɗa ma ita Rabin"
Sai na amsa mata da cewa zan faɗa mata har ta bar falona ina mamakinta. Ranar Yallaɓai sai Yamma ya fita, Rabi'atun da ta shigo na faɗa mata mun sauya tsari ta ce to, Yallaɓai kuma na manta ban faɗa masa da ya bar ɗakin Rabi'atu ɗaki na ya dawo ya yi kwana ɗaya ya koma ɗakin Gimbiya ya yi kwana ɗaya, ashe ita a tunanin na sanar da shi ni kuma na sha'afa saboda a ranar da yake wajena aka yi ma Ma'u C.S An ciro mata jariri ba rai ta zubar da jini sosai hankulan mu duk sun tashi mun ɗauka ma ba za ta yi rai ba. Ba gidan nake yini shi ya sa ban ma yar da kaina na sanar da shi ba.
Ina gidan Ma'u tun da an dawo da ita gida. Baaba ke kwana da ita can muka kai dare tare da su Ya Aina Yallaɓai ya kira wayata ni na ɗauka zai yi mini faɗan na kai dare alhalin ya hana ni yin dare in dai na fita da mota. Sai na ji muryansa a kausashe sannan ina jin tashin mgana amma ban san ko ta wace ce ba.
"Kin taho ne?
Lokacin takwas ne da wani abu na dare kenan yau ya dawo gidan da wuri.
"A"a zan dai ta so. Ban san ma lokaci ya tafi ba ka yi haƙuri "
"Ki taho yanzu ina jiran ki"
"Me ya faru?
"In kin zo za ki ji "
Ya faÉ—a sannan ya kwashe wayar ina jin haka na san ba lafiya, ina jin haka ban tsaya ba na yi musu sallama tare muka fita da su Ya Aina na ajiye su a juction na wuto gida.
Abin da ya ba ni mamaki Yallaɓai na haraba yana jirana shi da Gimbiya kamar yaƙi.
Ina gama parking ɗin motana na fito Gimbiya ta taroni da cewa" Maman Jidda baki faɗa ma Baban su Khalipa mun sauya tsarin kwanaki kwana ba ne?
"Ban faÉ—a masa ba me ya faru?
Na faÉ—a ina kallonta saboda mamakin abin da ke faruwa.