← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 103

Sashe 33

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai na fashe da dariya yana ta ya ni, a gurguje na shirya muka yi ma Ya Aina sallama muka fita muka barta tana ta wankin kayan haihuwa. Wayata ma a gida na bar ta, muna hanya ne, na ce ma Yallaɓai alkunyar Ruƙayya za mu riƙa kiran ta YUMNA. Ya ce abin da na ke so ai shi za a yi tun da Yallaɓai ya zama ni, nima na zama shi muna ta hiran mu har muka isa asibitin Aminu kano shashen masu awo suma sun yi mamakin haihuwanta da nake faɗa musu yadda lamarin ya faru, suka karɓi Yumna suna ta santi barin ma da suka ganni ras da ni kamar ban haihu ba. Ita dai Yumna an yi mata alluran su na jarirai ne domin rigafi aka ce ranar da ta yi kwana bakwai za mu dawo a yi wasu, ni kuma suka duba ni a tunanina ma na samu ƙari sosai sai suka ce na samu ƙari amma ba sosai ba. Amma dole ne suka rike ni sai sun yi mini ɗinki shi ya sa na kira Yallaɓai na faɗa masa sai ya ce ba damuwa sai ya jira ni daman muna zuwa sai da ya je ya yi sallar azahar da ta suɓuce masa.

Ni ban sani ba ashe Yallaɓai ya ɗora hoton Yumna a status ya yi magana sannan ya tura a family group ɗin su na gida da cewa na sauka lafiya. Ana ta kiran waya ta, mu kuma muna asibiti sai wajen gab da la'asar muka koma gida bayan an yi min ɗinki da dokokin na yi ta shiga ruwan ɗumi,tare da wasu magungunar da likita ya rubuta mini.
Tun muna asibitin ruwan Nono ya fara zuwa har na ma bata ta sha, saboda tana ta rigiman alluran da a ka yi mata. Mu na mota a hanyar komawa gida sai da na ƙara ba ta, tana ta rigima ni kaina azaban nake ji daga ƙasana, saboda ɗinki kana ganina duk na jigata shi kuma Yallaɓai sai kiran shi a ke yi a waya a na masa barka yana amsawa a muryan shi cikin farinciki da Annushuwa.

Ko da muka koma gida, jama'a cike. Rahila ta zo ita da Ma'u da Ya Murja. Ya Balki ce ba ta nan ta je suna a dangin mijinta Jigawa amma ta ce gobe za ta dawo. Nan na iske Hauwa mun dawo ba daɗewa sai ga Munnira da Mubeenan Musbahu sun iso suma, suna ta mamaki wai kamar ban haihu ba, ita kuma Munnira ta kama min masifa wai ace na haihu tun sha biyun rana amma na kasa kiran su sai dai kawai ta ga Mimisco ta poster jaririya a status ina dariya na ce ta yi haƙuri wayar a gida ma na bar ta mun tafi asibiti amma ba ta haƙura ba tana ta mita yadda suka shirya ma haihuwan nan ai kamata ya yi a ji haihuwan daga bakin su da ƙyar na samu ta haƙura amma in dai Munnira ce akwai ta da na cin magana.

Nan na bar musu jaririyan Ya Murja ta saka mini ruwan ɗumi na shiga na gasa ƙasa na sannan na sake yin wanka ina fitowa suka kawo abinci mai rai da lafiya shinkafa da miya da nama suka ce cefane a ka kawo bayan fitan mu na san Yallaɓai ne ya tura kuɗi a ka kawo mana cefane, sai da na natsa sannan na ɗau wayata na ga tarin kira ba adadi. Har Gwaggo ta kira ni sai da na sake dubawa ne sannan na ga har Alhajin mu ya kira ni. Ya Auwal da Ya Hamza dukkansu tare da matayen su sun kira wayata. Sameena ma ta kirani ita da Nafeesa, ina ga lokacin da suka ji labarin haihuwan ne suka yi ta kirana sai dai na riƙa bin su ɗaya bayan ɗaya ina kiran su muna gaisawa da ƙarfin gwiwata na ke faɗin sunan Mamana ta ci Rukayya amma za mu yi mata alkunya da Yumna. Sameena ta ce ai sun sa ni Yallaɓai ya saka a status ɗin shi lamarin ya ba ni mamaki na san ya kan saka hoto wani lokacin amma bai cika yin rubutu a ƙasa ba. Ban da Haihuwan Jidda lokacin a na cikin samartaka wannan ya ɗora ta ya yi ta ma Allah godiya amma Haihuwan Baby bai saka hoto ba ya dai yi rubutun ya samu ƙaruwa. Haka ma na su Anwar da Khalipa amma ita Yumna ta zo a sa a tun da har ya ɗora ta ya yi rubutu nan da nan na buɗe data na shiga na gani. Ta yi kyau ƙwarai a hoton wato wanda ya ɗauke ta ina zaune ne a ɗazu ne. Rubutun da ya yi a ƙasan hoton shi ne.

"Alhamdulillah. Allah na gode maka. Ubangiji ya sake azurtani da samun ƙaruwa daga Sadiyata. Na yi ta jira ban fidda rai ba, na yi ta ji a jikina Ubangiji bai yanke mini samun zuru'a daga tsatson Sadiya ba. Na yi haƙurin jira. Na shekara ɗaya,biyu, uku har zuwa shekaru goma ban cire tsammani ba. Kwatsam sai ga Ruƙayyatu(Yumna) kyautar da Ubangiji ya yi mana ita da misalin ƙarfe 12pm na rana. Ku yi mata addu'ar Allah ya raya mana ita tare da sauran ƴan'uwanta."

Ni kaÉ—ai ina ta faman mirmishi, hoton na É—auka nima na É—ora a status É—ina.
"It's Baby girl. Name Rukayyatu Yusuf Muhammad(Yumna)"
Nan na ga ruwan comments ana ta Allah ya raya.
Har Hauwa Jamilu sai da ta buga ihu ta  yo mini VN tana ce mini ikon Allah ba ta taɓa tunanin zan ƙara haihuwa ba.
Maijidda Bala yar anguwan mu kuwa ta ce mini ita ko in sha Allahu sai ta zo suna sai na ji daɗi na ce mata ina gayyatar duka yan set ɗin mu in sha Allahu gagarumin suna zan haɗa saboda murnan samun Rukayyatu da na yi a lokacin da na fidda tsammani. Nan ta ke Maijidda ta tura mganar haihuwan tawa a cikin group ɗin mu na makaranta sai tagging ɗina a ke yi ana mini barka wanda bai gane ni ba ma su Hauwa na ta yi masu kwatance, a zuciyata sai na ji wani iri lokaci ya yi da zan gyara mu'amalata da ƙawayena ana  yi da kai ai ya fi a ce ba a yi da kai.

Ranar yini na yi amsa waya da zirga zirgan mutane. Da yamma su Jidda suka dawo daga makaranta ai sai buga ihun murna da suka ganni da jaririya na haihu, Baby ta haye gadon ta ɗauke ta ta ƙamƙame tana faɗin na bar mata ina ta mata dariya Hauwa ta ce ta ɗauka ai daman na ta ne. Jidda kuma ni take kallo kafin ta ce" Wai da gaske kin haihu ne Umma?
Ina hararanta na ce" A a ban haihu ba jaririyar roba ce."
Munnira da Hauwa na ta mata dariya sai ta ji kunya ta kauda kanta. Baiwar Allah sai ta matso kusa da ni a hankali ta na ce min" Umma amma ba abin da ya same ki ko?
Sai na dafa kafaÉ—anta ina faÉ—in.

"Ba abin da ya same ni Hauwa'u. Na gode da kulawa Allah ya yi miki albarka."

Sai ta yi mirmishi ta amsa da Amin a hankali. Da ƙyar Baby ta bari ta ɗauki jaririyar nan sai da Munnira ta zare mata ido tana faɗin" Ke ba fa taki ce ke kaɗai ba." Sai Baby ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka Hauwa ta rumgumeta tana  lallashinta ni dai ina gefe ina mirmishi su da iyayen su. .Su Rahila da Ma'u da su Ya Aina suna can tare da su Mubeena suna aiki Tuwo suke yi Ya Murja kuma ta koma gida sai da safe za ta dawo da yamma nan sai ga Zabba'un Ya Abubakar fakam fakam da cewa daga gidan Gwaggo take ita ke faɗa mata na haihu sai a lokacin na tuna ban kira su  ita da Alhajin mu  ba sai na bari sai da a ka idar da sallar mangariba sannan na fara kiran Gwaggo. Ita ce bayan ta min barka na faɗa mata sunan Mama jaririyar ta ci.

"Haka Aina'u ta ce. Allah ya raya mana ita cikin addinin musulunci"

Na amsa mata da Amin Amin sai ta miƙa ma Alhajin wayar ni na fara gaishe shi cikin girmamawa.

"Lafiya lau Dubu an buÉ—e ido lafiya! Na amsa masa da lafiya lau.

"Kin tabbatar da ba abin da ke damun ki?

Ina mirmishin jin daÉ—i na amsa masa da cewa ba na jin komai alhamdulillah.

"To Allah ya ba ki lafiya. Gwaggon ku ta faɗa mini sunan jmRukayya kika ma yar  ko?
Na ce E Alhajin mu nan take ya fara kwarara mata addu'o'i.

"Allah ya albarkaci rayuwarta Allah ya raya ta. Allah ya tsare ta daga sharrin zamani. Allah ya ba ku ikon yi mata tarbiya. Allah ya yi musu albarka ita da sauran yan'uwanta gabaɗaya. Shi kuma mahaifin su Allah ya yalwata masa arziƙinsa yadda ba zai gajiya ba wajen hidimar ku gabaɗaya."

Na yi ta amsa da Amin Amin ni dai sai da na kashe wayata ina jin tahowar ƙwalla a cikin ƙwarmin idanuwana. Allah sarki iyaye ma su daɗi a fili sai da na ce" Allah ya jiƙan ki Mama "
Na faɗa ina mai kallon jaririyar da ta ci sunan ta, ta na kwance tana sharan barcin ta, duk ba su tafi ba sai bayan isha'i bayan har wanka Ya Aina ta sake yi ma Yumna ni ma na sake yi na shiga ruwan ɗumi sannan na take cikina da tuwo miyar agushi da kuni dukkansu sun tafi da cewa sai gobe za su dawo suka bar sai ni kaɗai sai yara can zuwa ƙarfe tara sai ga Yallaɓai ya dawo gidan ya taho mini da fura da kayan marmari da yawa na ce Jidda ta karɓa ta ɗaurayo ma na sauran kuma bayan sun ɗiba ta saka shi cikin frizer.
Chapter 33 · 0% Book details