Sashe 1
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TKGB30A1*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
A hankali na riƙa buɗe idanuwana da suka yi mini wani nauyi. Da farin POP da a ka yi rufin ɗakin na fara cin karo, a hankali na juya dama da haunina amma na rasa fahimtar a in da nake, kamar dai ƙaramin ɗaki ne sai da idanuwana suka sake washewa sannan na soma fahimtar in da na tsinci kaina.
Da ƙyar na miƙe zaune, ina sake bin ɗakin da kallo in har idanuwana sun ganin min daidai in kuma ba mafarki na ke yi ba tabbas ina asibiti kuma a gadon asibiti. Sakamakon ɓarayin hannun damana da na kalla sai na ga hannuna saƙale da abin ƙarin ruwa da na ɗaga idanuwana sama kuma sai na ga ruwa ake ƙara mini. Ɗis! Ɗis haka na ƙura ma saukan ruwa ta cikin ma zubar sa zuwa cikin jikina idanuwana jikina na bi da kallo sai na ga ba kayan da na baro gida da su ba ne jikina ba. Wata doguwar riga ce a jikina wanda in dai ban yi kuskure ba kayan Amina ne a jikina.
"Me ya faru da ni?
Na faɗa a sarari saboda na kasa tuna komai. Na kasa tuna lokacin da na tsinci kaina a gadon asibiti. Ɗakin ba kowa sai ni kaɗai kamar irin daƙunan ne na VIP. Kaina na dafe da hannuna na hagu jin ya ɗan saramai ina tunanin lokaci na ƙarshe kafin a hankalina ya gushe. Tabbas a gidan Amina na tuna ina cikin Toilet ɗin ta ina amai daga nan sai na ga jini. E tabbas na ga jini daga nan ne na fita hayyacina ban ƙara sanin in da kaina ya ke ba sai yanzu da na tsinci kaina a gadon asibiti.
"Innalillahi."
Na faɗa Daidai lokacin da na shafa kasan marata na ji kunzugu. Da gaske ne na yi zubar jini amma me ya kawo mini zubar da jini? Damuwa ce da firgici suka kawo min zuwan period ba tare da lokacin sa ya yi ba. Haka na faɗa ma kaina a cikin zuciyata. Yanayin lokaci nake so na fahimta amma na kasa ganewa. Sakamakon ɗakin akwai wutar lantarki sannan window ɗin ɗakin ya na nesa da ni. Sai dai duk da haka na ɗan fahimci akwai haske daga waje kenan duk abin da ma ya same ni bai daɗe ba tun da har yanzu dare bai yi ba akwai sauran rana.
Na muskuta kenan na gyara zama daidai lokacin aka buɗe ƙofar ɗakin a ka shigo. Na bi wacce ta shigo da kallo Nurse ce domin fararen kaya ne a jikinta wata yar mai ƙiba da ita.
"Sannu ya jikin na ki?
Ta faɗa bayan ta ƙariso gaban gadon da na ke zaune.
"Yauwa. Da sauƙi"
Na bata amsa a hankali ita kuma sai ta saka hannu ta dauƙo wani fayel da ke saman ɗan teburin da ke gefen gadona ta buɗe ta na dubawa.
"Don Allah wa ya kawo ni nan?
Sai da ta kalleni kafin ta cigaba da duba fayel É—ina na ma É—auka ba ta ji ba ne.
"Dr Ibrahim Aliyu."
Sai na kalleta amma na kasa mgana saboda na kasa tuna waye na sani mai wannan sunan.
"Jiya tare da wata mata suka kawo ki."
"Jiya?
Na faÉ—a cikin mamaki har ina waro ido.
Ijiye fayel ɗina ta yi lokaci ɗaya ta na cire min ƙarin ruwan da ke hannuna kafin ta cigaba da faɗin.
"Yes. Sun kawo ba kya cikin hayyacin ki. Kin farfaÉ—o amma muka sake mai dake da alluran barci."
Kallonta kawai na ke yi na kasa magana. Tun jiya na ke asibiti ban sani ba? Me ya same ni haka?
"Na cire miki ki É—an huta. Zuwa an juma sai a mayar miki da shi"
Har ta juya za ta tafi na kasa haƙuri.
"Sister don Allah me ya same ni?
Sai ta juyo ta na kallona kafin ta kaÉ—a kai ta na faÉ—in.
"Miscarriage
"Miss cra gge."
Na maimaita a rarrabe.
"Yes. Kin samu ɓarin ciki ne a jiyan."
Ta na gama faÉ—in haka ta juya ta na faÉ—in" Matar da suka kawo ki jiya ita ta kwana da ke. Ta je gida ta dawo nan ba daÉ—ewa ba."
Tana gama faɗin haka ta fice lokaci ɗaya ta na jawo min ƙofar ɗakin har sai da ta ɗan ba ta sauti.
"Æari? Wani irin É“ari kuma?
Domin sai na ji tunani ya tsaya cak na kasa fassaran ma'anar maganar Nurse É—in.
"Daman ana ɓari ba a samu ciki ba?
Tambayar da na yi ma kaina a fili kenan kafin na samu amsar ta an sake buɗe ƙofar ɗakin an shigo. Da rinannun idanuwana da suka yi min nauyi da na ɗaga ina kallon mai shigowa.
Amina ce a kan gaba sai megidanta biye da ita ɗauke da kwando a hannunsa ita kuma riƙe da ledoji guda biyu suka shigo ɗakin sai da na gan su ne sannan na tuna da sunan da Nurse ta faɗa min. Tabbas mijin Amina ne Dr Ibrahim Aliyu malami ne a jami'ar Kaduna. Da ya ke kuma sai da ya haura arba'in san da ya auri Amina shi ya sa duk wanda ya gan sa zai san ba yaro ƙarami ba ne.
"Ya Sadiya kin tashi?
Amina ta katse mini tunanina sai na kalleta ta zauna a gefen gadon ta na mai riƙo hannuna mara kanular.
"Ya jikin na ki? Jiya kin ba ni tsaro wallahi."
Ta faÉ—a ta na yar dariya lokaci É—aya ta na kallon mijinta.
Kallonta kawai na ke yi na kasa mgana domin sai na ji bakina ya yi min wani irin nauyin da na kasa furta harafi É—aya daga bakina.
"Maman Jidda ya ƙarfin jikin na ki?
Sai a lokacin na ji na yi magana bayan na kalle shi.
"Da sauƙi Dr. "
"Ma sha Allah. Allah ya ƙara lafiya."
Na amsa da Amin a saman leɓe na. Ita kuma Amina sai ta miƙe ta nufi kwandon da suka shigo da shi ta na tambayana me zan ci? Dr na gefe ya ce ta fara haɗa min tea ne ya warware min ciki tun da tun jiya ban ci wani abu ba.
"Kenan da gaske ne tun jiya na ke asibtin cikin rashin hayyaci?
Tambayar da na yi ma kaina kenan ban samu amsarta ba Amina ta haɗo min tea ta kawo min na karɓa hannuna na ɗan rawa sai Amina ta taya ni riƙewa da hannayenta ta na faɗin.
"Har yanzu jikin na ta ba ƙarfi."
"Kin san daman sai a hankali."
Dr ya amsa mata lokaci É—aya yana duba wayarsa da ke hannunsa.
Ina ta taimakamin ina shan tea ɗin da cokali, Dr ba daɗe ba ya ce zai shiga cikin makaranta Amina ta sakar min kofin ganin saura kaɗan ta miƙe domin yi masa rakiya.
"Allah ya ƙara lafiya Maman Jidda."
"Amin Dr. Na gode da ɗawainiya da ga zuwa baƙun ta na zo muku da hidima."
"Haba bakomai. Ai lalura ce Allah ya ƙara afuwa."
"Amin"
.
Na amsa a hankali, sun fice ina mai bin su da kallo kawai sai ina hakaito kaina ni da Yallaɓai. Yanzu itama Amina watan wata rana Dr zai iya nuna mata halin su na Maza ranar da ya yi aure. Wata ƙila shi kuma ba irin Yallaɓai ba ne, wataƙila shi ya san me ake kira hallaci. Duka na shanye tea ɗin domin ina jin jikina fayeu kamar takarda kuma ina jin yunwa kaɗan amma ba da yawa ba sai dai kuma ruwan zafin ya taimaka wajen farfaɗo da bushewar da cikina ya yi tare da maƙogwaro na har da saman labɓana.
Ji na yi marata kamar ta ƙulle ina jin fitsari sai na yi ƙoƙarin miƙewa tsaye a hankali, sannan na ijiye kofin saman drewer ɗin gefen gadon da na ke kwance. Sai a lokacin na fahimci ko hijabi ma babu a jikina daga ni sai rigar nan sai ɗankwali Allah ya sa bai saɓule ba tsabar halin da na kr ci na manta da rufe jikina a gaban suruki. To su da suka kawo ni asibiti cikin rai ƙwakwa mutuwa me ye ya yi saura kuma? Da ƙyar na iya taka kafafuwana zuwa tiolet ɗin cikin ɗakin ji na yi kamar in faɗi jikina kamar fallen takarda saboda rashin ƙwarin jiki.
Tabbas jini ke zubar min tun da ga shi a jikin pad ɗin da ke jikina. To ko dai maganar Nurse ɗin gaskiya ne na samu ɓari? Amma abin tambaya anan daman ina da ciki ne? Dawowar Amina ɗakin ne da ta ga ba ta ganni ba sai ta ƙwala min kira shi ya sa na yi tsarki na fito ina faɗin.
"Gani nan Amina."
Da sauri ta zo ta kamani ganin ina faman da fa bango ta maida ni har saman gado na zauna sannan ta koma gefe na kamar É—azu ta zauna.
"Ya Sadiya jiya kin ba ni tsoro"
"Me ya faru? Na kasa tuna komai"
Na faÉ—a ina kallon ta.
"Suma fa kika yi a cikin tiolet ga shi kina ta zubar da jini. Na ƙwalla ƙara ina ta ihu ba mai jina. Ƙwatsam sai ga shi Allah ya aiko min da Baban Yunma shi ya taimaka min muka kawo ki asibitin nan, ko da muka zo kin fita hayyacin ki tun jiya sai yau kika farfaɗo "
Ina kallonta amma na kasa mgana, sai ta cigaba da faÉ—in" Jiyan kin farfaÉ—o da daddare amma sai kika koma bayan sun yi miki alluran barci."
"Da gaske ne tun jiya na ke kwance a nan?