← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 123

Sashe 99

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranan wata Asabar Abuturrab na kwance kmr mai bacci sai dai ba baccin yake ba, Sadeeq kuma na xaune yana operating laptop Ummi ta shigo dakin da sallama, Sadeeq yace "Sannu da xuwa Ummi" tace "Yauwa Sadeeq bacci yake?" Sadeeq ya kallesa yace "Ba wani bacci idonsa biyu tun safe yake a haka, always pretending" Ummi ta karasa ta xauna gefen gadon tana kallonsa, Sadeeq kam sai kallon warce suka shigo dakin tare da Ummi yake, can dai tace "Ina kwana" ba tare da ya kuma kallonta ba yace "lfya lau" Ummi tace "Boy" a hankali ya bude ido, ya kirkiri murmushi yace "Welcm Mami" tace "Baka cin abinci boy koh?" Mikewa xaune yyi yace "Mami tambaye sadeeq na karya daxu" Sadeeq yace "Noo plss ba wani Sadeeq, you think am daft ko, toilet fa ya xubar da shayin Ummi, potatoes da egg din ma da xaki daga gado xaki gansu, sai dare yyi ya faki ido ya kwashe ya xubar, which is very bad of him" Xaro ido Abuturrab yayi yana kallonsa can yayi dariya yace "Sa ido sana'a mara amfani" Sadeeq ya bude hannu yace "Noo ba wani sa ido, da ina sa maka ido da ai baxan bari kke xubar da abinci ba, yanxun ma naji xaka yi karya da sunana ne shi yasa na tona" Ummi ta kalli Sadeeq tace "But you re nt doing him good kana barinsa baya cin abinci Sadeeq" Sadeeq yayi dariya yace "Ummi it's a deal muka yi da shi ae" Hararansa Abuturrab yyi yace "Wani deal bayan gashi kana sa idon har ynxu" mikewa sadeeq yyi yace "Nan gaba abba xan dinga shigowa da ina daga masa karkashin gadon yaga almunbazzarancin da kke masa da abinci" daga haka ya fice daga dakin yana wani irin murmushi, Ummi tace "Alryt, pls pls Boy ka dinga cin abinci kaga yanda ka rame kuwa am not happy gaskiya, to ko Samhan ta dawo ynxu ai ba gane ka xata yi ba wllh, u have changed totally, haba Aliyu" Murmushi yyi bai ce komai ba, sai a snn suka hada ido da fatima dake ta kallonsa, ta sunkuyar da kanta tace "Ina Kwana?" Ya kirkiri murmushi yace "Lafiya lau, ya hanya" kanta a kasa tace "Lafiya, ya jiki?" Yace "Alhmdllh" Mikewa Ummi tace "she said tana son xuwa ta dubaka shine muka taho tare sun yi hutu ne" yace "Alryt am grateful" fita Ummi tayi daga dakin, Fatima ta dago tana kallonsa a hankali tace "Am sorry Aliyu, it seems i caused everything, Allah ya bayyanar da ita lafiya" Bai iya ya kalleta ba yace "No you caused nothing, haka Allah ya tsara, after all, there is always a reason for everything, God plans best you knw" gyada kai tayi tana kkrin mayar da hawayen idonta, yace "Ya su Khadijah da Rabi'ah?" Kanta a kasa tace "They are fine" Daga haka ta mike ta kwashe kwanukan dake dakin ta nufi kofa ya bi ta da ido har ta fita, karfe uku Ummi ta fara shirin komawa gombe, Mami tace "Hajiya baxa ki bar fatima ba tunda kince sun yi hutu" Ummi ta kalli fatima dake tsaye sakale da handbang dinta har ta shirya tace "Bata taho da kaya ba ai Hajiya" Mami tace "Ba ga kayansu Ramla ba, ki bar ta tayi mana kwana biyu mana" Ummi tayi murmushi tace "Toh shknn." Yau ma kamar kwanaki biyun da suka wuce haka Noor ta tashi da ciwon baya, a kwanaki biyun bata bari kowa ya gane halin da take ciki ba, iyakar dauriya ta iya sa ba kadan ba, duk da Umma na yawan ce mata in dai taji ciwo a ko ina tayi magana sai dai tayi murmushi kawai, jin ta kasa kwanciyar kuma ta mike xaune da kyar, shima taji xaman na neman gagararta, tashi tsaye tayi ta durkusa don axaban ya mata yawa, bude kofar dakin aka yi Sadiya ta shigo rike da tray din breakfast don Umma bata bari ta sauka kasa, komai daki ake kai mata, Sadiya ta ajiye trayn da sauri tace "ya aka yi Noor?" Ta d'an kirkiro murmushi tace "Kai na ke d'an min ciwo" Sadiya tace "Toh bari a kira Umma" da sauri tace "A'a ai ba sosai bane, idan na sha tea sai in dau paracetamol" Sadiya ta durkusa ta shiga hada mata tea'an, duk da irin axabar da Noor ke ji bata bari ya nuna a fuskarta ba, ganinta a durkushe Sadiya tace "Toh ki xauna ki karya" gyada mata kai tayi tace "Toh" cike da karfin hali ta xauna taji kmr ana kara mata ciwon amma ko da wasa bata nuna ba, ta jawo cup din tea ta kai baki, ji tayi waist dinta ma ya dauka, ganin ta kasa shan shayin Sadiya tace "Are you okay noor" murmushin karfin hali ta kuma yi tace "Am ohk" Ae bata rufe baki ba taji wani mugun axaban da ya linke na wanda take ji, bata san lkcn da ta ajiye cup din ba ta runtse ido, mikewa sadiya tayi tace "Subhanallah" da sauri ta fice daga dakin, sai ga ta da Umma sun shigo, Umma ta dagota tace "Noor ba nace in kin ji ciwo ki min magana ba, ina ke maki ciwo" kasa cewa komai tayi don ciwon ya fara fin karfinta, can ta fara yarfe hannu hawaye na sakko mata, Umma tace "Sadiya maxa kira min yayanku mu tafi asibiti" da sauri Sadiya ta fita daga dakin don xuwa part din yayan nasu, Umma ta dauko hijab dinta ta sa mata, ixuwa yanxu sunan Umma kawai Noor ke kira don ita kadai tasan abinda take ji, Umma na rike da ita suka sakko parlor, tafiyar ma dauriya kawai take, Sadiya ta dawo tare da Maryam, haka suka fita waje, Maryam ta taimaka mata ta shiga mota Umma da sadiya ma suka shiga motar, Maryam ta shiga gaba, Mijinta dake ta yi ma Noor sannu ya tada motar suka yi asibiti.

Kafin su isa asibitin har ta fita hayyacinta, tafiyar ma kasawa tayi bayan sun fito daga cikin motar ta kalli Umma cikin kuka tace "Wayyo Umma Aliyu, kuce ya xo" Umma ta kalli Maryam, Maryam dai ta kasa cewa komai sai kallon Noor take, da taimakon nurses din da Mijin Maryam ya kira suka shiga da ita asibitin sai labour room.

Meanwhile Abuturrab kam tunda ya tafi masallaci sllhn Asuba har gari ya waye bai dawo ba, dole Abba ya koma masallacin ya taso sa a gaba suka dawo gida, Mami ta shiga bedroom dinsa tana kallonsa ganin damuwar dake fuskarsa ta xauna kusa da shi cikin raunin murya tace "Don't start that again Son, wai ya kake son inyi da raina ne, baka tausayina Aliyu, tun da Sadeeq ya tafi abun ka ya kara jagulewa kuma, haba son, ya kake son inyi da raina?" hawaye ne ya cika idonsa ya daura kansa a shoulder dinta cikin rawar murya yace "Mami Samha...." Rungumesa tayi ita ma hawayen ya cika idonta tace "I know son, musulmin kwarai fa an san sa ne da tawakali, sau nawa kuma xa ace maka tana hannun mutanen kwarai idan Allah ya yrda....." Da kyar yace "Mami her delivery may be today or tomorrow..." jikin Mami yayi sanyi, ta shafa kansa a hankali cikin sanyin murya tace "In sha Allah xata sauka lafiya albarkacin wannan rana ta juma'ah, kayi ta mata addu'a kaji son" kai ya gyada mata bai iya yace komai ba.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
88.....89
Har kusan sha biyun rana Noor ban da wahalan labour bbu abinda take, bbu abinda ke kara daga ma Umma hankali irin ynda take kiran Aliyu gashi ta tambayeta ko tana da number sa taki cewa komai, in ta gaji da kiran Aliyu sai ta koma Mumynta da Abbanta, suna nan asibiti har kusan karfe biyar amma shiru, nan likitan ya kira Abbansu Sumayya don yana asibitin shi ma a lkcn yake gaya masa in har wasu awanni biyun suka wuce bata haihu ba to xa ayi mata Cs kar babies su samu matsala, shi dai rasa abun cewa yayi, can dai ya amsa ma likitan ya fita, Umma ya kira ya sanar mata yanda suka yi da likitan, ita ma tayi shiru duk jikinta yyi sanyi, girgixa kai yayi yace "Ina jin Hajiya gwara ki lallabeta ta bada number mijin nata a kirasa ko ya kika ga" tace "Haka ne" daga haka ta koma ciki, ta xauna kusa da ita ta kamo hannunta ta dago kanta, ji tayi kamar ta xubar mata da hawaye ganin yanda ta jigata, ta daure tace "Look at me Noor, ki gaya min gaskiya, kina da number Aliyun?" Noor ta daura kanta jikinta tana girgixa kai ta fashe da kuka sosai tace "Bani da shi Umma, don Allah ku kira min shi mutuwa xan yi wllh" Jikin Umma yayi sanyi ba kadan ba, to ita yanxu ina xa su fara nemo Aliyu?

Usman d'an Umma na uku ne yasa aka debo masa ruwa a cup ya yi addu'a ciki ya ba Maryam ta bata, Umma na rike da ita ta kai mata ruwan baki ta kauda kai da sauri tace "Bana jin kishi Umma" Umma tace "Addu'a ne Noor, ki daure ki sha" da kyar ta bude baki ta sha ruwan, bayan kusan minti biyar ta d'an nutsu har ta samu bacci, ashe duk axaban da take ji na wasa ne don cikin baccin taji ciwon da ya linke wanda take yi tun safe, duk ta haukace masu, nurses suka dawo gunta da likita daya, hankalin Umma yyi mugun tashi haka Maryam da tausayinta yasa ta fita kawai, Umma ma dai ta kasa daurewa ta fita, ko minti biyar bata kara ba ta haifo yaranta maza biyu, kukansu ya cika dakin, Hawaye ne ya sakko idon Umma ta shiga gode Allah a xuciyarta, yaran ma basu wani jigata kmr yanda likitocin ke tunani ba.
Chapter 99 · 0% Book details