← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 123

Sashe 92

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Kina ma da hankali kuwa yarinyar nn?" Saketa yyi ganin da yyi fatima numfashinta na seize, Samha ta juya ta shige gida ta bar su a gun, dagota yyi ganin xata samu attack yayi part dinsu da ita da sauri, Ummi dake parlor tana ta jiran makulli ta mike tace "Subhanallah, ya aka yi?" Ya xaunar da ita kan kujera, kan yace komai Ummi ta wuce ciki don dauko mata inhaler, su Salima suka shiigo parlon, Ummi na fitowa ta mika ma Abuturrab inhalern tana kallon su Salima tace "What happened?" Salima ta tabe baki tace "Matarsa ce ta hau ta da duka" Shiru Ummi tayi tana kallonsu, bata kuma cewa komai ba, Abuturrab kam bai iya dagowa ya kalleta ba har fatima ta dawo dai dai sai dai kuma da sauri take breathing, Ummi ta kalli su Salima tace "Ku shiga da ita bedroom" suna wucewa daki, Abuturrab ya dago da kyar yace "Mami don Allah kiyi hakuri, i don't knw whats...." Katse sa tayi tace "Noo ba komai boy, it's okay bani makullin" mikewa yyi duk jikinsa yyi sanyi ya mika mata makullin ya juya ya fita, Daki ya tadda Samha fuskar nan nata a murtuke, cikin fushi yace "Kinga you should be careful Samantha, matsalar ki ya fara isana, a kan wani dalili xa ki kama yar mutane da duka, are you mad?" Ta kallesa a takaice tace "I am not" daga haka ta mike xata fice dakin ya fixgota a mugun fusace yace "Kee, ni kike ce ma you are not??" Kkrin kwace kanta ta shiga yi tana huci tace "How will i admit i am mad, da ina hauka xan baka sha'awa har kaji kana so na, har ka rabo ni da iyayena, har ka aureni, let go of me right away Aliyu" a tsawace ta kare maganan, daga nan ta dinga masa tsawan ya saketa tana kokuwa da shi, ba karamin daurewa yyi ba na ganin bai wanka mata mari ba, ya dunkule hannunsa jin irin urge din da hannun ke basa na ya wanketa da mari, ganin idan ya ci gaba da saurarenta baxai iya controlling kansa ba ya turata har sai da ta buge da bango ya fice daga dakin kamar wani xaki, ficewa gidan yyi gaba daya, rabon da yaji irin wnn bacin ran har ya mance, wani xugi xuciyarsa ke masa, fuskar nn tasa bbu alamar rahama ya dinga tafiya down the street, can ya sa hannu aljihunsa ko akwai kudi ya fiddo dari biyar ya nufi gun wani me kiosk dake kofar wani gida, kwalin cigarette ya nuna ma mai kiosk din ya dauka ya mika masa, karba yyi ya mika masa kudin ya dau lighter da ya gani ya bar gun, gida ya koma ya shige bedroom dinsa ya sa key ya bude taban ya fara abinda ya dde bai yi ba, Samha kam dama yana fita taci kukanta me isanta tayi karfin halin tashi ta dauko yar jaka ta fara xuba kayayyakin ta ciki, Abuturrab na gama xuke xukensa bacci ya daukesa, bai yi minti goma yana baccin ba karan wayarsa ya tada sa, ya bude ido da kyar yana kallon wayar, can ya mike xaune ya jawo wayar, har lkcn bai ji xuciyarsa ta dawo masa dai dai ba duk da yaji sauki ba kamar daxu ba, hajiya Mariya ce ke kiransa ya daga wayar ya amsa sallamarta snn ya gaisheta, tace "Ya naji muryar ka haka Aliyu are you okay" yace "am okay mum bacci nayi" tace "Samha fa" yayi shirun kusan second biyar snn yace "She's fine mum" Hajiya Mariya tace "Hajiya Hajarah tace min cikinta ya tsufa koh?" Yace "Ehh" tayi shiru kafin tace "Are you okay kuwa Aliyu?" Yace "Mum daga bacci na tashi ne" tace "Toh shkkn, Aliyu ina tunatar da kai ka rike azkar da tsayuwar dare, kayi ta addu'a son, i had a dream that's nt encouraging...." A takaice yace "In shaa Allah mum" tace "Sai mun yi waya, Allah yyi albarka a gaida Samha" "Ameen" kadai yace ya katse wayar ya mike ya shiga bathroom, yana fitowa ya bude kofar dakin dai dai lkcn da Samha ta fito daga daki da jaka, wani kallo yayi mata daga sama har kasa, ita ko ko kallonsa bata yi ba xata wuce ya fixgota, sai da ta girgixa da irin fixgar da yyi mata, cikin kaushin murya yace "If am nt mistaken ai ba da kaya kika shigo gidan nan ba".

Bata kallesa ba ta sake jakar hawaye na sakko mata tace "Naji toh" turata yyi har sai da ta kusa faduwa ta juya ta bar wajen, ta nufi kofar parlor ta fice daga gidan, tafiya take har ta isa bakin titi, ba karamin daurewa tayi na ganin ta tsaida hawayen dake xuba mata ba, ta tsayar da adai daita, a hankali tace "Don Allah ka taimake ni ka kai ni tasha ban da kudi" Hawaye na sakko mata ta kare maganan, yace "Ba can nayi ba," daga haka ya ja adai daitansa, ta tsayar da adaidaita yafi biyar kafin ta samu wani bawan Allah da yace ta shiga, haka ya kai ta tashan tayi masa godiya snn ta wuce ciki, direct gun motar kano ta nufa, nan tayi ta tsayuwa ta rasa abin cewa tun ana tambayarta inda xata har aka kyaleta, wata Hajiya ce aka sauke a mota ta nufeta da sauri, tana kkrin mayar da hawayen idonta tace "Mumy don Allah ki taimaka ki biya min kudin mota bani da kudi" kallonta kawai dattijuwar ke yi, sai taji tausayinta a tunaninta yawon duniya ta fito yi, ta kalli uban cikin dake gabanta ta girgixa kai tace "Toh shiga" risinawa tayi tayi mata godiya snn ta shiga motar, matar ma ta shiga ta bada kudinsu, nn da nn motar ya cika suka dau hanyar kano.
*Haske writers asso*
[11/30, 7:16 AM]
+234 814 219 6835
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
83.....
Chapter 92 · 0% Book details