← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 123

Sashe 91

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari da safe Anty Maryam ta fara shirin komawa kd, Samha ta dinga rusa kuka ita sai ta bi ta fa, shi dai bai samu bakin cewa komai ba, Anty Maryam ma ta fita harkanta don ji take kmr ta make ta, bbu ynda bai yi da ita ta taho su tafi tasha ba amma taki, Sai da Anty Maryam xata fita taji tausayinta, ta dawo ta durkusa kusa da ita tace "Haba daughter, u re married yanxu fa bai kamata kina behaving kamar karamar yarinya ba, kuma na fa ce maki soon xan dawo, ko baki son in xo in xauna da ke idan kin haihu?" Ita dai Samha bata ce komai ba sai hawaye take, shafa kanta Anty Maryam tayi tace "Toh kiyi hakuri, tashi ki raka mu park" girgixa kai tayi alamar baxata je ba, cike da tausayinta Anty Maryam ta bar parlon Abuturrab ya wuce da ita park, shi ya biya kudin motar duk da bata so hakan ba, har ihsaan sai da ya biya mata seat snn ya bata dubu goma a hannu, bai saurare Anty Maryam dake cewa ya karbi kudinsa ba, ganin ta dage yace "Haba Anty, ni fa ihsaan na ba" sai da yyi da gaske ta hakura, yana tsaye har motar ta cika suka tashi snn ya nufi motarsa ya koma gida.
*Haske writers asso*
[11/27, 7:53 PM]
+234 703 709 9528
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
82.....
3months later.

Samha na daki kwance misalin karfe daya na rana sai juye juye take tsabar yunwar dake cinta gashi ta ki tashi, shi kam Abuturrab na kwance parlor da yake ranan lahadi ce yana kallo, a watanni ukun da suka wuce ba karamin matsala Samha take basa ba, kullum jarabanta karuwa yake abu kadan xata daga masa hankali da fitina, gashi bai son hayaniya duk ta sa ya rame, sai dai ynda take sllh bbu fashi ke burgesa yake kuma jin tausayinta tunda aikin baban giwa kawai take, kuma girman cikin bai hanata sllh ynda ya kamata ba, bata ma son kusantarsa ko kuma shi ya kusanci inda take bare ma ya dinga yin abubuwan da Anty tace yyi don jan hankalinta, fata yake ta sauke cikin nn lfya ya samu kwanciyar hankali, ta dawo Samha dinsa ta da mai miskilanci, shi dai yasan wasu masu ciki na da bala'i amma nata daban ne, yanxu kam cikin ya fito sosai sai kayi tunanin haihuwa yau ko gobe amma watannin cikin bakwai, har lkcn kuma bbu wani aikin da take don cikin yyi mata nauyi sai uban bacci kmr k'asa, hakan yasa yake tausayinta, babban tashin hankalinsa idan ranan Antenatal ya xagayo, da kyar da kyar yake lallabata su je asibiti, iyakar abinda take a gidan shine ta girka abinda xata ci me yawa kuma ita kadai ke cinye kayanta ko tayi bata masa, kuma ko sau daya bai damuwa da abinda take masa, sai ma dariya da ta ke basa, lkci lkci Abbanta na kiranta ta wayarsa har ma shi ma su gaisa, babban tashin hankalin da yafi na Antenatal a gun Abuturrab shi ne idan fatima ta xo gida weekend to fa ba shi da kwanciyar hankali har sai ta koma sch don wani shishshige masa take gaban ko waye har uwarta, Samha kuwa in ta dinga masa jaraba rike kai kawai yake don xuwa ynxu ciwon kai hayaniyarta ke sa masa, ynxu dai kwana biyu masifar ya lafa kuma ya rasa dalili, jin fitowarta daga daki ya dago yana kallonta, tayi masa kallo daya ta wuce kitchen, a hankali yace "Baby..." Juyowa tayi tana kallonsa yace "Kuna jin yunwa knn" dauke kai tayi ta shige kitchen ta daura shinkafa ta fito, parlon ta dawo ta xauna kan 2sitter, har hakan ya basa mamaki yau kuma ta xauna gu daya da shi, bayan minti bakwai ya juya ya ga ta kwanta ta rufe ido, kallonta ya dinga yi, can yyi murmushi ya mike ya wuce daki, jaka ya bude ya fiddo kayan xanensa da ke cikin jakar da Maminsa ta aiko masa da, ya fito parlor ya xauna inda yake yayi sharpen din pencil din snn ya dau takardan ya daura kan hannun kujeran ya fara xana ta, ya fi minti talatin yana xanen kafin ya mike ya dau stool ya dawo kusa da ita ya daura takardan ya duka ya ci gaba daga inda ya tsaya, bayan minti goma ta bude ido a hankali jin k'aurin shinkafa, ja baya yyi da sauri, ita ma kmr warce aka mintsila ta mike tana kallonsa tace "What r u doin here?" Kame kame ya fara ta karbe takardan a hannunsa tana kallo, kasa daina kallon xanen tayi, a hankalo yace "Am sorry Baby bari a yaga idan baki so..." Ta dago kai ta kallesa, murmushin da ya bayyana fararen hakoranta tayi underneath her breathe tace "Woaw i love it, it's perfect" Murmushin shi ma yyi don har ya mance rabon da tayi masa murmushi yace "Really?" A hankali Tace "Yeahhh....

Doctor u remember the dog u drew....." Ya wara ido yace "Yea my dog" kasa daina kallonta yyi tuna farko farkon haduwarsu, ita ma din tunanin da take kenan ta kasa cewa komai, ya dawo kusa da ita ya kamo hannunta murya can kasa yace "That moment.....

When we were still strangers to each other, ranan da na fara daura idanuwana a kanki kina cewa in taimake ki, though u didn't think twice before leaving ganin cigarette a hannu na, how i saved u at the end, the day we met again at d front of my gate with my frnds, how u came back greeted and thanked me, how i was stunned seeing a Rosary round ur neck, ranan da na baki lift daga bakin titi, the day u gave me ur textbook to draw for you, a mammalian heart nd the Human Skeleton, the day u came into our compound nd was frightened by my big dog, how....

How i made you feel at home.....

And that was how everything started....

" daga haka yyi murmushi yana kallon idonta da ya cicciko, rungumesa tayi, ya lumshe ido yace "I have always love u from the very beginning Samha" a hankali tace "Me too" kwace kanta tayi tace "My rice...." Daga haka ta mike da sauri tayi kitchen yace "Baby ki yi a hankali dnt harm ur self nd our babies" Ranan dai ya ci sa'a cokali biyu ta saka a shinkafa da mai da yajin da ta xubo a plate, ya lura she derives pleasure eating shinkafa da mai da yaji, bbu ynda ya iya shi da ba son yaji yake ba haka suka ci abincin, yamutse fuska ta fara yi bayan sun gama ci yace "Baki koshi ba ko baby?" Kamar xata yi kuka tace "It's kicking me" Ya d'an xaro ido don idan akwai abinda ta tsana baby yayi kick dinta ta dinga complain knn har da kuka wani lkcn, yace "Forgive dem plss, na sha gaya maki wasa fa suke maki dear, they are just being lively in der momy's womb....." A fusace tace "Don ba kai ake yi ma ba shi yasa xaka ce haka..." Tashi tayi da kyar ta nufi kofar fita ya bi ta da kallo yana murmushi, shi bai taba ganin mai jin haushi idan abun cikinta yyi motsi ba sai a kan Samha, Danna bell aka yi gabansa ya fadi, ya mike ya nufi kofar, fatima dai ce tsaye da kawayenta biyu, Samha dake xaune balconyn don in dai ta koshi nan take xama ta juya tana kallonsa, ya hade rai yana kallon fatima yace "Ya aka yi?" Wani kallo tayi masa ta hade rai ita ma tace "Ummi tace a karbo mata makullin motar ka nata na gun mechanic" Bai ce komai ba can ya juya ya koma ciki, wani tsaki Samha ta ja ta mike xata wuce ciki, ita dai fatima bata ce komai ba, Salima tace "To fah, da wa kuma matar gidan take, dake dai ko fatima?" fatima tayi dariya tace "Ke nifa kallo kafurai basu ishe ni ba wllh, da dai musulmai ne yan uwana....." Ae ko rufe baki bata yi ba Samha ta fincikota ta sauke mata tagwayen mari kan kace me sai gashi ta yi kasan balcony da ita ta shiga nakadar ta, Ihun da Salima tayi ya ja hankalin Abuturrab dake daki ya rasa ynda xai fito da makulli kar Samha ta cinyesa, xaro ido yyi ganin abinda Samha ke wa fatima, su Salima sun kasa ta6uka komai a tsaye, ya sauka kasan ya janye Samha a fusace yace "Kee, Are you stupid, kina hauka ne xa ki hau ta da duka?
Chapter 91 · 0% Book details