← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 123

Sashe 102

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ana kiran Isha suka iso asibitin kusan a tare har da Col da yyi driving din da kansa, kallo daya xaka yi ma Mami ka tausaya mata, Hajiya Mariya ta fito daga motarta ta nufi tasu motar ta bude ma yayarta kofa, Mami ta fito, Hajiya Mariya tace "Don Allah ki kwantar da hankalin ki yaya, everything will be alright" ko kallonsu Abban Abuturrab bai yi ba ya nufi entrance din asibitin, Hajiya Mariya ta kama hannun Mami suka bi bayansa tana kkrin kiran layin Abuturrab yana ringing Ahmad dake tsaye har lkcn a ward din ya daga, nn ya gaya ma Hajiya Mariya ward din da suke, ganin Col ya nufi gun nurse dake reception Hajiya Mariya tace "Na kira fa su sun fadi dakin da suke" tsaye yyi har suka shiga gaba snn ya bi bayansu, suna isa dakin Shi ya murda kofar ya shiga sannan suka shiga su ma, bai ko kalli mutanen dake tsaye dakin ba ya isa gadon da Abuturrab yake ya rungume hannayensa yana kallonsa, Mami kam kasa karasawa tayi lkci daya hawaye ya shiga sakko mata, Hajiya Mariya tayi karfin halin gaida su Ahmad da dad dinsa dake tsaye ita ma ta karasa gadon tana kallonsa, har lkcn Noor na xaune kusa da gadon kanta kife kan gadon, duk da muryar Hajiya Mariya da taji ta kasa dagowa sai hawaye take, Girgixa kai Col yyi ya kalli Hajiya Mariya yace "We are leaving for india tomorrow in sha Allah" daga haka ya juya zai fita ta sha gabansa murya can kasa tace "Col ga bayin Allahn da suka kawo sa asibiti baka ko gaisa da su ba kuma xaka fita" sai a snn ya daga kai yaga su Ahmad dake kallonsa, karasawa yyi gaban dad dinsu ya mika masa hannu suka gaisa ya ba Ahmad da Usman hannu su ma, snn ya kalli dad dinsu yana kirkiran murmushi yace "Mun gode kwarai da kulawar ku Alhaji, Allah ya saka da alkhairi, though bn ma san ya fito gida coz he is under medication since yesterday," Ita kam Hajiya Mariya idonta na kan Noor tana mamakin wacece ita ganinta kusa da Abuturrab gashi tun da suka shigo bata dago ba, bude kofar ward din da aka yi yasa ta dauke idonta kanta tana kallon kofar, Umma ta shigo hannunta rike da Hussain, Maryam ma ta shigo rike da Hassan, Umma na hada ido da Mami jikinta yyi sanyi ganin ynda take kuka kuma ko ba a gaya mata ba ta gano ita ce Mahaifiyar Aliyu, ta karbi Hussain gun Maryam ta karasa kusa da ita ta mika mata yaran biyu, kallonta Mami take kafin ta kalli jariran sai kuma dai ta share hawayen idonta duk ta karbesu, Umma na murmushi a hankali tace "Ur grandchildren...." Mami ta dinga kallonta ko kiftawa bbu don bata gane inda ta dosa ba, can ta kuma kallon yaran gabanta na faduwa, Umma ta kalli Noor da taki dagowa har lkcn tunani ta fara yi to ko dama basu santa bane, ita ma bata san su ba, ganin confusion tattare da Mami, Umma tace "Yaran Aliyu kenan, ga kuma matarsa can...." Mami ta juya da sauri tana kallon wacce Umma ke nuna mata, Hajiya Mariya ta dago kan Noor da mugun mamaki, ae ko ta ga Samha ce, a hankali tace "Samha???" Noor da ta kasa dago kanta ta mike ta shige jikinta ta rungumeta tana shesshekar kuka, Hajiya Mariya da hawayen farin ciki ya cika idonta ta rungumeta ita ma tace "Meyasa kika mana haka Samha, ina kika tafi all this while," cikin kuka tace "Mumy nima bn sani ba" Col dake kallonsu gaba daya cike da mamaki ya kalli yaran hannun Mami, ya kuma kallon Abuturrab, kofa ya nufa dad din Ahmad ya bi bayansa, Ahmad yyi murmushi ya bi su shi ma da Usman, Hajiya Mariya ta janye Noor jikinta tana goge hawayen idonta tana murmushin farin ciki ta ja Noor gun yayarta tace "Mami kin ga Samhar Aliyu, Allah ya amsa addu'ar mu ya dawo mana da ita lafiya" Mami da ta kasa cewa komai hawayen farin ciki na sauka idonta ita ma ta dinga gyada ma kanwartata kai kawai, Hajiya Mariya ta karbi yaran gaba daya hannunta ita ma hawayen ya ki tsaya mata, a hankali Noor ta taka ta isa gun Mami har lkcn kanta na kasa ta shige jikinta, rungumeta Mami tayi wasu sabbin hawayen na xuba idonta ta rasa wani irin farin ciki xata yi, Su Umma da Maryam dai sai kallonsu suke cike da tausayi, Hajiya Mariya ta karasa gun Abuturrab ta kwantar masa da twins din kusa da shi, tana murmushi ta ja dogon hancinsa idonta cike da hawaye tace "C'mon wake up now Atturab, duk ka daga mana hankali ka mayar da mu hypertensive patients, ka tashi ga Samha ga babies dinka" tana magana ne hawaye na sakkowa idonta, hancinsa ta kuma ja tana girgixa kai tace "Atturab...." Ya bude ido a hankali yana kallonta, ta bude ido tayi wani murmushin farin ciki tace "You are back my only son" A hankali yace "Mum, mum Samha...

I saw...." Runtse ido yyi jin kansa da ya wani sara masa, ya shiga kkrin mikewa xaune ta rikosa xata taimaka masa, Hussain ya tsala ihu ta dalilin dannesa da yyi da hannu, Ae noor bata san lkcn da ta janye jikinta a na Mami ba ta nufo gadon da sauri jin ihun yaron, suka hada ido da Abuturrab, a hankali ya sauke idonsa ya dauke hannunsa gun yana kallon yaran gefensa ya mike xaune, Maryam ta juya tana 'yar dariya can ciki, kunya ya ishe Noor ganin kallon da Hajiya Mariya ke mata, sunkuyar da kai tayi tana jan fingers dinta ta juya, Hajiya Mariya ta d'an yi jim ganin reaction din Abuturrab da ya ga Noor, to ko ya riga ya ganta ne, ta dai dau Hussain da ya ki yin shiru ta mika masa, a hankali ya sa hannu ya karbesa, nan da nan yaron yyi shiru, tayi murmushi tana kallonsa Murmushin gefen baki yayi shi ma, ya kai bakinsa kunnen yaron, bayan kusan minti uku ya ajiye sa ya dau d
ayan shi ma yayi masa haka, a hankali ya kwantar da shi kusa da d'an uwansa, ya sakko da kafafuwansa daga kan gado ya rike kai yace "I need rest mum" Umma ta karaso gun gado tace "A'a da ka jira sai an sallameka...." Ya kalleta ya d'an yi murmushi yace "Naji sauki Mama, nagode" ta kalli Maryam tace "Ki kira su Abba a waje" kofa ta nufa, Abuturrab ya d'aga kai yana kallon Mami dake tsaye inda take duk jikinta a sanyaye, murmushi ya sakar mata, murya can kasa yace "Mami" tayi karfin halin mayar masa da murmushin, sauka yyi daga kan gadon ya nufeta ya shige jikinta, cikin sanyin murya yace "Am... am sorry for all the troubles i cause you mother...." Shafa kansa tayi ta kasa cewa komai, Abbansa ne ya shigo dakin tare da Abban su Ahmad da su Ahmad din, suna hada ido da shi ya sunkuyar da kai, can kuma ya nufesa duk jikinsa a sanyaye, barin wajen col yyi ya nufi gun Umma yace "Amm...

Mun gode kwarai Hajiya Allah ya bar xumunci, ya saka da alkhairi" tayi murmushi tace "Amin Alhaji" wani likita ne ya shigo ward din tare da nurse, yana ganin Abuturrab yace "Maa sha Allah, Allahu ya kara kiyayewa" Col yace "Xa mu iya tafiya ynxu ai" Likitan yace "Ehh toh, amma da sauran injections dinsa, xae karbi daya ynxu sae gobe da safe ya dawo" Col yace "Alryt" likitan ya juya ya fita, Col da Abban Ahmad suka bi bayansa, Hajiya Mariya ta d'an tabe baki ganin abinda yyi ma Abuturrab.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
91.....
Chapter 102 · 0% Book details