← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 123

Sashe 47

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ina kaduna..." Tace "Karya kake Abuu, ina yar mutane?" A hankali yace "Tana nan Mami..." Mami ta girgixa kai tace "Yanxu rayuwar da ka xabar ma kanka kaga shi xae fishsheka Abuturrab, warce ba muharramar ka ba kake rayuwa da ka ajiye koyarwar addinin ka aside?" Shiru yyi bai ce komai ba, tace "Aliyu..." Nan ma dai bai ce komai ba, ta kuma san yana jin ta baxae dai yi maganan bane, tace "Toh yanxu meye amfanin haka Abuu, me yasa har gobe baxa ka dawo gentleman ba?" Xaunawa tayi gefen gado ta dafe kanta, can tace "Look kayi min magana ynxu bana son wlknci, tell me what's the meaning of what you did?" Ya bude idonsa dake rufe da kyar yace "I want to convert her...." Mami tayi tagumi tace "Ta haka ake converting din mutum Aliyu, ka dauketa ku gudu kamar wani Indian film kace min you want to convert her?" Murmushi yyi cikin sanyin murya yace "Kiyi hakuri Mami, ke ma kinsan ynxu idan na dawo da matsala, mami you've got to trust me, kinsan abinda xanyi da wanda baxan yi ba, ni bana fasikanci kin sani, just that this the only way out, xan dawo gida in shaa Allah amma har sai naga hankalinta gaba daya ya karkata ga islam, nasan duk abinda nayi ma 'yar wani surely xa ayi ma nawa kidz din kuma har kannina xai iya shafa sbda haka am very cautious of what i do...." Mami tace "A ina ku ke ynxu?" Yace "Muna Gombe Mami" ta xaro ido tace "Wa ka sani a can Abuu?" Yace "Bbu kowa gashi kuma har nasan mutane ynxu har na fara aiki" tace "Da wani CV din??" Yayi murmushi yace "Da na brain dina Mami" Mami tace "Aliyu ka rufa min asiri ka mayar da yar mutane, Aliyu ni wnn abinda kke son yi ko kadan bai gamshe ni ba, yanxu rayuwar nn wa kaga xae yrda xuri'arsa a samu irin haka, ba fa ce maka tayi tana sha'awar addinin ka ba, kai ke cusa mata kawai, gaba nake jiye maka wllh, shawarata kawai ka dawo in taga tana son musulunci xata yi ne ba sbda kai ba...

Ka dawo kayi auren da iyayen ka ke son kayi Abuu, ka ajiye shashancin nn da kake yi son" da damuwa yace "Mami ni wllh ita kadai naji xan iya aure...

Pls ki bani go a head ko yanxu xan iya aurenta nasan zata amince kuma dawowa addinina baxae mata wahala ba in har na aureta" Mami tace "Toh ba da yawuna ba wllh, in kuma shakiyancin naka har ya kai ka fara tsallake magana ta to bismillah, na fada na sake fada ba da yawu na xaka je a daura maka aure da Christian ba...." Daga haka ta katse wayarta, ya rike kansa.

Can ya mike da kyar ya cire shirt din jikinsa ya kwanta kan gado hade da lumshe ido, ya fara bacci samha ta shigo dakin, durkusawa tayi kusa da shi tana kallonsa a hankali tace "Doctor..." Bude ido yyi don baccin nasa bai yi nisa ba, tace "Abinci fa?" Ya mike xaune yace "I've eaten sai anjima" tace "Toh..." Mikewa tayi xata fita yace "Samha!" Ta koma ta durkusa tace "Na'am..." Ganin kallonta kawai yake tace "Doctor i prayed today also..." Yace "Really?" Tace "Yea, tare da khadija, she came back from islamiyya around 1, shine ta xo nan...

Tace min ita ma recently tayi waec" Yace "Waow, shknn kin samu frnd knn...

Which means you weren't lonely today!" Tace "Yeah, tare muka yi girki da ita, i like her she's very nice" yace "Uhnn!

Ai naga alama" ta langwabar da kai tace "Toh ko nima in dinga bin ta islamiyyan i don't want to be staying at home all alone kafin ta dawo" ya sauko da kafafuwansa yana kallonta yace "If that's what you want love sai in sa ki..." Tace "Ehh ina so!" Yyi murmushi yana kallonta yace "Alryt gobe sae ki fara koh?" Ta gyada masa kai, mikewa tayi tace "Let me go back tana parlor, nayi xaton xaka ci abinci ne" yace "Am ohkay dear, ltr xan ci" tace "Tohm" snn ta fice daga dakin ya bi ta da ido murmushi dauke fuskarsa, sosai yaji ddin islamiyyar da tace xata, and he was happy she brought the idea her self.

Washegari yana dawowa daga masallaci ya shiga dakin da take ya tada ta, ta mike xaune tana mitsike ido yace "Yau baxa kiyi sllhn ba knn?" Ta kallesa tace "Sllh kuma?" Ya wara ido yace "Alryt dear, yi kwanciyar ki nayi xaton xa kiyi sllhn ne" bata ce komai ba hakan yasa ya juya ya nufi kofa, mikewa tayi ta bude kofar bayi ya juya ya kalleta bai dai ce komai ba ya fita ya shiga wani dakin don shiryawa tunda yyi wanka kafin ya je masallaci yana buttoning din shirt dinsa ta shigo da hijab jikinta, ta karasa dakin tana kallonsa tace "Nayi sllhn" yace "That's very nyc of you love...

Allah ya karba" murmushi tayi tace "Me xan yi maka for brkfst?" Yace "Just lipton xa ki dafa dear, akwao bread" tace "Kwai fa?" Yace "Noo, ni baxan ci ba sai dai ke" juyawa tayi ta fita, ko kafin ya fito har ta dafa ruwan Lipton din ta ajiye a parlor da kayan beverage, ya karaso parlon ya xauna ta hada masa tea'n yana kallonta, ganin irin kallon ta sunkuyar da kanta, murmushi yyi ya jawo cup din tea din, tace "Baxan je islamiyyan ba yau?" Yace "Xa ki mana baby" mikewa tayi tace "Tohm bari in shirya" daga haka ta shiga daki, yana gamawa ya fita xuwa part din Hajiya, karo ya kusa ci da fatima da ta fito daga parlon hannunta rike da makullin mota tana sakale da jaka alamar boko xata, Bai ko kalleta ba ya bi ta gefenta ya isa kofar ya danna bell, kin tafiya tayi ta xuge jakar hannunta tayi pretending kmr neman abu take, Khadija ce ta bude kofar ta gaishesa da fara'a ganin shi ne, yace "Mami fa?" Tace "Tana ciki bari in mata magana" daga haka ta juya ta koma parlor, ba a dau lkci ba ta dawo tace "Wai ka shigo" Bin bayanta yyi suka shiga parlon, dai dai lkcn da Mami ma ta shigo parlon, xauna yyi kan sa a kasa ya gaisheta ta amsa tana murmushi tace "Kun tashi lfya Boy?" Yace "Alhmdllh Mami" tace "Har ka shirya knn, in dai ka gama abinda kke tun da akwai makullin mota gun ka sai ka dinga wucewa kawai boy" yace "Toh Mami, dama samha ce ke son shiga islamiyyar su khadija, ina son in fara xuwa can da ita ne...." Mami tace "Maa sha Allah, kace mata in dai ta shirya ta xo sai in kai ta....

Kai kayi wucewar ka kawai" A hankali yace "Toh nagode Mami" daga haka ya mike ya fita duk da hakan bai gamshe sa ba don bai son Mami tasan bata san komai ba.

Fatima dai na nn tsaye fa har lkcn, wnn karan tare masa hanya ma tayi duk don yyi mata magana, ga mamakinta sai gani tayi ya tsallake karfen dake xagaye balcony din yyi wucewarsa.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
Hmm where are you blood!

Ke ma ga naki, Allah ya kara hada kawunanmu sweet sis Iqram Mujaheed (Maryam M Bello) proud to have a sister like u.
39.....

Parlor ya tadda Samha yace "Dear ki shirya Mami xata ajiye ki a islamiyyan...." Shiru tayi tana kallonsa, ya kamo hannunta yace "Yea, i wanted taking u there by my self but she insisted...." Ta langwabar da kai a hankali tace "Toh" mikewa yyi yace "Yauwa baby, sai ja dawo" tace "Allah ya tsare...." Har ya kai bakin kofa ya juyo yace "Bbu rakiya dear" murmushi tayi ta mike ta bi bayansa suka fita a tare, hada ido suka yi da fatima dake tsaye tsakar compound din ta kasa tafiya, Samha ta kirkiri murmushi tana kallonta tace "Good morning sis fatima" Fatima ta mayar mata da yake tace "Same" daga haka ta nufi gun motar ta da take xuwa makaranta da, Shi dai Abuturrab bai ko kalli inda suke ba har ya isa gun motar da Hajiya ta basa ya juyo yana kallon Samha da ta bi bayansa, jawota yyi gabansa yana kallonta yace "Tohm sweet sai na dawo" murmushi tayi ta gyada masa kai, har xai kai bakinsa nata ko me ya tuna kuma ya bude mota kawai ya shiga tana tsaye ya gama bata wuta snn ya kalleta ya kashe mata ido ya ja motar hade da horn mai gadi ya bude masa gate, Kallon motar fatima kawai Samha take har ita ma ta fita da gidan, ta kusa minti uku tsaye tana kallon gate din gidan snn ta juya da kyar ta koma ciki.
Chapter 47 · 0% Book details