← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 123

Sashe 42

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

But you re in trouble in har ka shigo hannunsa" Aliyu yayi murmushi yace "Na sani" da damuwa tace "Ka dai kula Aliyu tausayin yarinyar nake, tunda har ta guji iyayenta sbda kai, jan ra'ayinta xuwa musulunci baxai yi wahala ba" Yace "Hakane Mum, dama am planing of marrying her soon don ban son in cuceta, i don't want her to regret trusting me, idan nayi haka komai xae fi zuwa da sauki" Hajiya Mariya tace "Anya, naga kamar ya fi ka jira sae ta amshi musulunci, kar ta ga kamar kana using advantage din auren ne..." Bude gate ta ji anyi da sauri tace "Za mu yi waya Aliyu, don't call again xan dinga kiran ka..." Daga haka ta katse wayar, Abba ta gani bakin gate waya kare a kunnensa ya rako abokansa xa su wuce, tayi dialing din number wata da xata bata kudi suka yi magana snn ta juya ta nufi gate din ya bata hanya tayi wucewarta, bin ta yayi da kallo har ta shiga cikin gida, ya juya ya koma ciki shi ma bayan abokan sun shiga mota, ya shiga part dinsa ya kira Mami, bbu bata lkci Mami ta iso, yana tsaye bakin window rungume da hannunsa (Inda Aliyu ya gado rungume hannu knn, lol" ya juyo yana kallonta yace "Hajarah! i won't take it likely with ur sister idan naga da sa hannunta a abubuwan nan da Aliyu yake, xan ajiye cewar yar uwarki ce a hukuntata yanda ya kamata...." Mami tace "Ban yi mamaki ba...

You can do more than that, yanxu kuma ka bar xargina ka koma xargin yar uwata" ya daga kafada yace "Ni dae na gaya maki" juyawa tayi ta fice daga dakin, dakin su Ramla ta shiga ta ci kukanta Ramla na lallashinta kafin ta fita ta koma dakinta, Hajiya Mariya na ganin Abba ya kira Mami dama ta yi saving din number Aliyu da wani suna daban tayi deleting dinsa daga call log, ko da Mami ta shigo dakin Hajiya Mariya na bathroom, ta dau wayarta ta fita, kiranta na karshe ta kura ma number ido, can tayi dialing taji muryar mace, ta dudduba dai bata ga alamar komai ba ta koma daki, Hajiya Mariya bata tambayeta dalilin daukan wayarta ba sae harkan gabanta take.

Tunani Abuturrab ya dinga yi ko dai gida xae kama masu nan gombe ne, duk ya rasa takamaiman solution, kallonta yayi ganin tana juye juye kan gado, can ta mike xaune yace "Cikin ya fara koh?" Ta gyada masa kai, ya mike ya dauko mata abinci yace "Sauko ki ci in maki allura"
ba musu ta sauko ya bude mata abincin ta fara ci, alluran ya hada ya ajiye yana jiran ta gama, bata wani ci da yawa ba ta mike yace "Sauran fa" da kyar tace "Anjima xan ci" daga haka ta kwanta ya mike ya karasa kusa da ita yayi mata alluran, Finger dinta ya kura ma ido ganin har lkcn xoben da ya sa mata na nan, ya kama hannunta a hankali yace "Samha!" Dago kai tayi ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya kai lips dinsa kan hannun cikin sanyin murya yace "I will never let you down dear, i will be ur hero, i will be ur everything...." Hawaye ya cika idonta ya dago ta ya rungumeta, ta fara kuka a hankali, jin tayi shiru ya dago kanta a hankali ya ga idonta a lumshe, kwantar da ita yayi ya mike ya nufi window yana tunanin next action din da xae dauka, can ya dau kudi ya fita, wani me taxi ya tsayar bayan tsayuwar kusan minti sha biyar a bakin titi duk yana duba responsible cab man da xae tsayar su yi magana, yana kallon mutumin yace "Pls ina d'an tambaya ne" cab man din yace "Allah yasa na sani" Abuturrab na shafa beard dinsa yace "Kasan inda xan samu agent...

I mean their office, anywhere around?" Mutumin yace "Wae na gida?" Abuturrab yace "Yes!" Mutumin yace "Wanda na sani da nisa daga nan, sae dai..." Abuturrab yace "No mu je kawai ka kai ni" daga haka ya shiga mutumin ya ja taxi din.

Tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso office din wasu agent, Abuturrab ya fito yayi masa godiya ya basa dari biyar ya shiga office din, ba shi ya fito ba sae kusan karfe shidda bayan an basa tabbacin nan da xuwa gobe xa a karbar masa gida.

Ko da ya dawo lodge dinsu tana bathroom tana wanka, ba a dau lkci ba ta fito daure da towel, tana ganinsa ta tsaya nan bakin kofa, yace "Naga alamar ba kya gajiya da wanka yarinyar nan...." Murmushi tayi bata ce komai ba ya mike xae shiga yayi alwala ta durkusa da sauri tace "Nooo" xaro ido yayi yace "Ina ruwana da ke?" Murmushi yayi ya shiga toilet din, ta mike da sauri.

Ko kafin ya fito har ta gama shiryawa, yana kallonta yace "Xan je mosque, will be right back" ta gyada masa kai ya fita, sae bayan Magrib ya dawo dakin, ya ganta xaune shiru da alamar tunani take, ya karasa kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Sorry Dear, na jira anyi magrib ne" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, ya xauna ya bude mata ledan fruits din yana kallonta, Apple ta dauka ta kai baki a hankali, shi ma ya dauka ya kai daya baki, wayarsa dake kan gado ya fara ring, ya dauka yana kallon screen din yaga Hajiya Mariya ce, ya daga ya kai kunne yace "Hello Mum!" Tace "Aliyu where is she?" Kallon Samantha yayi ya mika mata wayar yace "My mum!" Ta sa hannu ta karba ta kai kunne, Hajiya Mariya tace "Ya kk Samha?" Samantha tace "Lafiya Mumy ina yini?" tace "Lafiya lau, kiyi hakuri kin ji, Allah na tare da ku, kar ki sama kanki damuwa...." Kai kawae Samantha ke gyada mata kamar tana ganinta.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
34.....

Mikewa tayi a hankali ba tare da ta kallesa ba ta dau rigar baccin ta shiga bathroom, ba a dau lkci ba ta fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai, ta nufi kan gado a hankali ta kwanta ta juya masa baya, bayan kusan minti goma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya shiga bayi, ko da ya fito kashe tvn dake aiki yyi ya kashe wutan dakin ya karasa gado ya kwanta, a hankali ya birgina inda take, cikin sanyin murya tace "Doctor..." Yace "Samha...." Bata ce komai ba ya juyo da ita ya kwantar da ita kan faffadan kirjinsa yace "Sleep tight love, am with you" ta lumshe ido tayi lamo jikinsa, a haka har bacci ya dauketa, a hankali ya kwantar da ita ya mike ya koma kujerar dake dakin yayi kwanciyarsa amma ya kasa bacci sae juye juye yake, can dae ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, sae kusan karfe uku da rabi ya samu yayi bacci, da asuba a masallacin dake cikin Hotel din ya fita yyi sllh sae da gari ya waye ya shigo masu dakin da breakfast, har ta shirya ya sameta, yana kallonta da mamaki yace "Ina fita kika tashi amma koh?" Kai kawai ta gyada masa, yayi murmushi yace "Alryt xo kiyi break kafin in shirya" daga haka ya shiga bathroom, ko da ya fito har ta gama cin abinda xata ci, yace "Are you sure kin koshi?" Ta gyada masa kai, shiryawa yayi ya ci chip da egg din kadan ya mike yace "Bacci nake ji Samha, let me sleep small" murmushi tayi ta mike xata gyara masa gadon yace "Noo don't worry dear...." Daga haka yayi kwanciyarsa, ta koma ta xauna ta rufe sauran breakfast din, yana kwanciya bacci ya daukesa, ita dai tana xaune idonta a kan tv, sae dae ko kadan ba sanin kan film din da ake tayi ba, tayi nisa a tunanin da take, Abbanta kawai take tunani wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, why did she accept to leave her family because of Aliyu, hade kanta da kujera tayi hawaye na sakko mata sae a snn take jin bata kyauta ba, tayi kukanta mai isarta daga nan ita ma bacci ya dauketa don yanda bai yi wani bacci ba haka ita ma bata jiya ba daren jiya duk tana kallonsa yana sllh, sai kusan goma da wani abu Abuturrab ya tashi, ganin yanda ta kife kai ya mike da sauri ya isa gabanta ya dafa ta yace "Samha" dagowa tayi da sauri tana kallonsa, kallon idonta ya dinga yi, da damuwa yace "Kuka kika yi?" Ta sunkuyar da kanta ya dago ta yace "Samha you re regretting everything koh?" Ta fashe da kuka tana girgixa masa kai, duk ya rikice yace "No plss samha, kar ki min kuka don Allah, naji xan maida ki gida...." Da sauri ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Am not regretting" yace "Toh me yasa kike kuka" goge hawayenta ta shiga yi cikin sanyin murya tace "Its just....

We re in trouble" ya lumshe ido ya kamo hannunta yace "Allah na tare da mu Samha, kar ki damu kin ji" sunkuyar da kanta tayi, yace "Tashi ki raka ni!" Ba musu ta mike ya kashe kayan kallon yace "Mu je" kofa ta nufa ya bi bayanta, suka fita ya kulle dakin, gun agents din jiya ya tafi, suna isa daya daga agent din yace su je ya ga gidan ko yayi masa, a motar agent din suka tafi, gida ne babba hadadde mai flats biyu, gidan na dauke da dakuna uku manya, Abuturrab ya kalli Samha yace "You like it?" Sunkuyar da kai tayi, yayi murmushi yace "Alryt, yallabai gidan yayi, thanks much" bbu bata lkci Abuturrab ya biya komai na gidan kusan 450k, da yamma bayan sun dawo hotel din yace "Xuwa jibi sae mu koma can koh dear?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru?" Murmushi tayi bata ce komai ba.
Chapter 42 · 0% Book details