← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 123

Sashe 7

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washegari da ya kasance asabar Abuturrab na dawowa daga masallaci ya shiga main house don gaida Abba kasanacewar yana gari, Abba ya amsa gaisuwarsa idonsa dake dauke da glass a kan laptop din dake gabansa, can Abuturrab ya mike da nufin wucewa Abba yace "Ina fa da magana da kai Ali" komawa yayi ya xauna yace "Toh gani Abba" Abba bai ce komai ba har na kusan minti biyar sai kuma yace "How about planing of settling down Aliyu!" Shiru Abuturrab yayi don sai da gabansa ya fadi, Abba yace "Yes it's high time you do that, you will be thirty one soon...." Abuturrab ya sauke kansa kasa kana yace "Abba komai fa lokaci...." Abba ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Don't tell me that, Sai yaushe lokacin xai xo?" Shiru yyi bai ce komai ba, Abba yace "Go and think about it pls" a hankali yace "Toh Abba nagode" daga haka ya mike yyi masa sallama ya fita, bedroom din Maminsa ya nufa ya sameta xaune har lkcn kan darduma, Khaleesat kuma na kwance kan gado tana bacci, ya xauna bakin gadon, can ya gaji da xaman yayi kwanciyarsa kawae, sai kusan bakwae Mami ta gama Azkar dinta ta mike ta dauke darduman tana kallonsa don idonsa a lumshe yake tace "Abuu are you sleeping?" Bude idon yayi ya mike xaune sannan ya sauko kasa ya gaisheta ta amsa tace "Ka tashi lafiya?" Yace "Yea, but Abba spoilt everything" Mami ta d'an bude ido tace "Me kuma ya faru" ya marairaice yace "Mami wai maganan aure fa Abba ke min, yaushe ma na girman" Mami tayi murmushi tace "Mancewa kayi, jiya ka girma" yace "Allah Mami kije kiyi masa magana kice ur son is not grown up yet, yaushe ma kika daina ban madara da daddare?" Dariya Mami tayi ta xauna gefen gado tace "Silly you! c'mon tashi ka ban waje, it's better kaje ka xauna ka yi tunani da kyau kaga what's good for you, kilan idan kayi aure zaka nutsu" mikewa yayi yace "Am not ready for marriage Mami, toh waye xai xama mijin ma idan aka yi auren...

Ita ko ni" Bai jira cewarta ba ya fice ta bi sa da kallo tana murmushi, jallabiyar jikinsa ya cire ya dau kayan sport dinsa ya sa ya dau chill Coke a fridge snn ya fito ya nufi gun da yasa aka tula masa kayan gym, ya kusa awa daya gun yaji kamar an bude gate, xagayowa yayi da sauri, tsaye tayi bakin kofar tana kallonsa hannunta rike da littattafai tana sanye da bakar abaya tayi rolling kanta, ganin kallon da yake mata yasa ta kasa tsaye gu daya, can tace "Um Good morning" sai kuma ta juya da sauri xata wuce, yace "Frnd!" Juyowa tayi, ya mata murmushi ya karasa kusa da ita ya rungume hannayensa yana kallonta, sunkuyar da kai tayi, yace "Ina xa ki this early morning?" Dago kai tayi ta kallesa tace "Lesson, waec lesson!" Yace "Ohh that's nyc, how was ur nyt?" Ta wara ido tace "Splendid!

Xaka min assignment plss sir" langwabar da kai yayi yace "Assignment kuma, which?" Tana kkrin bude littafin tace "Physics and Biology" mika masa tayi ya karba yana kallo snn yace "Uhm!" Tace "You are busy koh?" Ya kalleta yace "Sai yamma zan fita aiki, am around now" cike da shagwaba tace "Toh ka min plss" kallonta kawai yake, can yayi murmushi yace "Ohk, but I will only show you how to solve it, and you do the rest by ur self" ta xaro ido tace "But am going to lesson...." Yace "Wannan ma ai lesson ne" shiru tayi tana kallonsa, ya mika mata littafin yace "Shiga ki ajiye a ciki, tare xa muyi" a hankali ta sa hannu ta karba littafin ta nufi cikin parlon amma da gani ranta bai so ba, ya sauke hannunsa ya bi ta da kallo sai kuma ya juya ya koma gun gym din ya dau sauran coke dinsa ya shiga parlor, tsaye ya ganta ya karashe shanye coke din ya wurga can din yace "Why standing like a soldier?" Murmushi tayi ta d'an dosana kugunta jikin kujera, ya karasa parlon yace "Let me freshen up sai mu fara" kai ta gyada masa kawai ya dau hanyar bedroom dai dai lkcn da aka danna bell, dawowa yayi da sauri ita kuma ta mike tana kallonsa da damuwa tace "ur sisters koh" bai tanka ta ba ya nufi kofar ya leka ya ga peter ne dauke da breakfast, bude kofar yayi ya karba ba tare da ya amsa gaisuwar da yake masa ba yace "Thank you" sannan ya rufe kofar ya karasa parlon ya ajiye, har lkcn tana tsaye tace "Kar sisters dinka su xo fa" yace "Bbu kowa gidan fa, duk sun tafi islamiyya" a hankali ta koma ta xauna, ya wara mata ido snn ya wuce, ya kusa minti talatin kafin ya fito sanye da farin polo da 3qtr baki ya shigo parlon yace "Sorry for keeping you waiting" murmushi kawai tayi ya xauna kan rug ya matso da tray din breakfast din da aka kawo mai, ya kalleta yace "Je kitchen ki kawo wani cup plss" ba musu ta mike ta wuce kitchen din sai ga ta ta dawo da cup ta samesa yana hada tea me kauri, ta ajiye masa cup din ta koma ta xauna, ya hada wani snn ya kalleta yace "Taho muyi breakfast" ta xaro ido tace "Noo, ni fa na k'arya" gyada kai yayi yace "Ashe ko baxa ayi assignment din ba yarinya" ta marairaice tace "Da gaske fa doctor na ci abinci" ya hade rai sosai yace "Toh ai shknn" shiru tayi tana kallonsa sai kuma ta mike ta karaso kamar xata yi kuka ta xauna, yace "Allah ya taimake ki da bbu abinda xan maki" murmushi tayi ta sunkuyar da kai, ya ajiye mata cup din tea a gabanta, snn ya debi potatoe, yam, egg, plantain a plate daya ya ajiye mata sai pepper soup din naman ram ya ajiye mata, ta marairaice tace "baxan iya cinye su ba Dr" yace "Ohk to mu ci tare" dawowa yayi gefenta ya xauna ta kallesa ta gefen ido, ya dau fork daya ya ajiye mata daya snn ya soma ci, da kyar ta iya daukar fork din don duk a takure take ta dauki potatoe ta kai baki a hankali tana satan kallonsa, sai cin abunsa yake, ganin yanda take tsakuran abincin ya ajiye fork din hannunsa yana facing dinta yace "Kinsan Allah idan baki ci abincin nn ba bbu abinda xan maki" ta xaro ido tace "Kaga ina ci fahhh" hararanta yayi ya ci gaba cin abunsa, haka yasa ta bude ciki ta ci abincin sosai don sai da suka cinye wanda ya diba snn ya shanye tea dinsa ya mike yace "Fast ki shanye tea din mu fara" kai kawai ta gyada masa kamar xata yi kuka don ta koshi.

Yana kallo ta dawo kusa da shi daga kasa ta xauna tace "Doctor na gama" kallon wajen yyi ya ga wayam ta kwashe komai yace "Are you sure kin shanye shayin kuwa" ta turo baki tace "In kawo cup din ka ga?" Ya gyada kai yace "Alryt!
Chapter 7 · 0% Book details