← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 123

Sashe 10

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Sunday throughout bai ganta ba har yamma, duk sai yaji bbu dadi ganin har karfe shidda bai ganta ba, mikewa yyi daga karshe ya fita ya dau hanyar gidansu kamar me strolling har ya gama tafiyarsa bai ganta ba ya juya kawai ya dawo gida, har ranan laraba Abuturrab bai hadu da Samantha ba duk yaji sa bbu ddi har abun ya dinga basa mamaki, wai d'an sabon nn da suka yi har xai damu don bai ganta ba, yana xaune parlor tare da su Mami da yammacin ranan alhamis, Mami tace "Abuu!" D'agowa yyi da Sauri yana kallonta, tace "What's wrong with you?" Buda ido yyi yace "Nothing Mami...." Ta girgixa kai tace "Noo, ni fa na haifeka daga jiya xuwa yau naga you are not ur self....." Khaleesat tace "Mami baki yi noticing da kyau ba, for the past two weeks yanxu ya Turab ya canxa, he no longer talk to us, idan ma muka je part dinsa koran mu yake, he no longer treat us well...." Ilham tace "And he's alwayz closing his door don ma kar mu shiga" Ramlah tace "I think his dog is now his everything...." Abuturrab dai sai bin su da kallo yake, Khaleesat tace "or may be yana jin haushin Abba ya maida sa BQ ne, but it's not too late ya Abuu you can still beg him ya bar ka ka dawo nan" Abuturrab ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, Mami tace "Aliyu!" Kallonta yayi tace "Meye matsalar ka?" Ya girgixa kai yace "Bbu komai Mami, am just occupied with work ne yanxu" Mami tace "Toh shknn Allah ya mana jagora..." Mikewa yyi yana kallon khaleesat yace "Ke kuma kika sake ce min Turab sai na gurje bakin ki" daga haka ya kalli wayarsa dake ring yace "Jaheed ya xo Mami...

Later xa mu shigo" Mami tace "Ohk Allah ya kai mu" daga haka ya fita xuwa bangaren sa Khaleesat ta bi sa da harara, Xaune ya ga Mujaheed yana ta kallon k'aren dake xaune cage, Abuturrab yace "Welcome!" Mujaheed ya mike yace "Yanxu pls meye ma'anar Dog din nn maimakon mai gadi" Abuturrab ya wara ido yace "Ya fi su iya gadi...." Mujaheed yayi dariya daga haka suka shiga parlor, Abuturrab ya dauko masu can coke a fridge, Jaheed yace "Kaga maganan serious nake son muyi Man kada kuma ka raina min hankali" Abuturrab bai ce komai ba sai da ya ajiye empty can din coke din hannunsa snn yace "Ina jin ka" Jaheed yace "Old man dina ne ya takura ni maganan aure this dayz wllh, am just confused donno what to do..." Abuturrab ya buda ido sai kuma yyi murmushi yace "Salima fah?" Harara Jaheed ya watsa masa yace "Salima har macen aure ce?" Abuturrab ya d'aga kafada yace "Ohk, nima of recent Dad dina ke min xancen aure...." Jaheed yace "Ae gwara kai kana da Saudat" Shiru Abuturrab yayi, Jaheed ya shafa kai yace "Gaskiya ka sama min solution, just few months ya ban if not ya hada ni da koma wacece ta xo masa a kai" Abuturrab yyi yar dariya yace "Amma kuma duk yan matan ka Mujaheed" Jaheed yayi tsaki yace "Kaga if you don't have anything good to say in tashi in kara ma motata mai" Abuturrab yayi murmushi yace "Kawai ka fara neman mata yanxu...." Jaheed yace "Wacece wnn yarinyar da ka taho office da ita ranan" wani kallo Abuturrab ke yi masa, wanda hakan Mujaheed yace "Ohk sorry ban san budurwar ka bace" Abuturrab yace "Ba budurwa ta bace" Jaheed yace "Then why the frowning of face?" Abuturrab ya tabe baki, sai kuma yyi murmushi yace "She's a Christian" xato ido Jaheed yyi yace "Christian kuma?" Abuturrab ya gyada Kai, shiru jaheed yyi yana kallonsa, can ya girgixa kai yace "That's sad, amma a ina ka san ta?" Abuturrab yace "Ga gidansu can few houses from ours" Jaheed yace "Lallai, babban magana kenan" Mikewa Abuturrab yayi jin kamar motsi a gate ya fita da sauri jaheed ya bi sa da kallo, bai ga kowa gate din ba da kuma alamar iska ce don a bude Jaheed ya bar sa, juyowa yyi ya koma parlon.

Washegari friday Abuturrab na dawowa daga masallaci misalin biyu da rabi ya dau faran kujerar roba ta xauna waje jikin flower yana dannar wayarsa kunnensa sakale da earpiece, tun daga nesa ya hangota tana tahowa, ya kasa dauke idonsa a kanta ko kiftawan kirki bai yi har ta iso inda yake, ga mamakinsa sai ya ga taki kallon gun har ta wuce sa, bai san lkcn da yace frnd ba, ta juyo tana kallonsa.
*Haske writers Asso*
*Noorul Huda*
7......

Sunkuyar da kanta tayi ta dawowa cikin sarkewar murya tace "Ina yini" kallonta kawai yake ganin yanayinta yace "Baki da lafiya ne?" Kin cewa komai tayi kuma taki d'agowa ya mike yace "Talk to me mana, what's wrong?" hawaye ya cika idonta ta gyada masa kai, kalle kallen anguwar yayi, kawai ya kama hannunta suka shiga gida ya kulle gate din, parlor ya nufa da ita bayan yasa ta shiga da takalmanta ya rufe kofar yana kallonta yace "Since when?" xaunawa tayi kan kujera ta kwantar da kanta jiki ya durkusa gabanta yace "ina ke maki ciwo?" Xamowa kasa tayi ta hade kanta da gwiwa ta fashe da kuka bata ce komai ba, jin kukan nata ya dinga yi har xuciyarsa ya dago kanta ya dafa shoulders dinta da damuwa yace "Talk to me mana, ina ke maki ciwo" kalle kalle ta shiga yi can ta mike da sauri ya rikota xai yi magana ta toshe bakinta tana kkrin kwace hannunta, da sauri ya saketa ya mike ya kama hannunta suka nufi toilet dake parlon da ita, amai ta dinga kwararawa yana kallonta har ta gama tana mayar da numfashi ya debo mata ruwa ta wanke bakinta ya gyara wajen ya fito da ita, kwanciya tayi nan tsakiyar parlon tana juye juye, sai kuma ta fashe da kuka, ya hade rai yace "Kinga idan baxa ki min magana ba ki tashi kiyi tafiyar ki, leave now" mikewa tayi da kyar xata fita ba tare da ta kallesa ba ya bi bayanta da sauri ya jawota ta fado jikinsa, rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, sun kusa minti uku a haka ya dago kanta a hankali yana kallonta yace "You are on ur period?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba sai hawaye, komar da ita yayi ya xaunar kan kujera ya shiga bedroom dinsa, da yake baya rasa magunguna da allurori na Dysmenorrhea sbda kanninsa daukowa kawai yayi ya fito parlor, kwance ya ganta kasa, ya fara hada alluran yana gamawa ya dawo kusa da ita yace "Kin ci abinci koh?" Cikin kuka tace "Na sha tea" yace "Ohk, let me inject you, xa ki samu relief kin ji" bai jira cewarta ba ya fara daga doguwar gown din jikinta, ta rike da sauri don dama ita ba gwanar sa dogon wando bace, muryarta na rawa tace "Doctor ban sa komai ba...." shiru yayi yana kallonta sai kuma ya mike ya shiga daki ya dauko towel dinsa ya fito ya bata yace "to tashi ki daura," ta mike ta karba ya dauke kai ta daga gown din ta daura, kujera ta tafi tayi rub da ciki ta runtse ido ya bi bayanta, a hankali ya sauke towel din yayi mata alluran, yana gamawa ta fashe da kuka ya dagota xuwa jikinsa yace "It's okay xae daina maki yanxu" Kai kawai take gyada masa, sai da yaga ta nutsu snn ya saketa, ta xamo k'asa ta kwanta ta rufe ido, durkusawa yyi yana kallonta, ba a wani dau lkci ba bacci ya dauketa, ya mike yayi disposing syringe da kwalban alluran ya dawo parlon ya taimaka mata ta koma kan kujera.

Yana bedroom aka danna bell ya fito da sauri ya nufi kofar, ganin Ramla ce yace "What again?" Tace "Ohh ya Abuu Mami ce fa ta aiko ni ka bude kofar plss...." ya hade rai yace "Pls go am busy yanxu, or you say it out there" murguda baki tayi don bata san yana kallonta ba tace "Ni fa....." Yace "Leave immediately idan ba haka ba xan sa ki kuka if I shud open this door" juyawa tayi fuu ta wuce.

Sai kusan karfe shidda Samantha ta tashi daga baccin, yana parlor har lkcn yana danna laptop, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo tace "Wayyo my mum is at home...." ya kalleta snn ya kalli agogo ta mike da sauri xata sauke gown dinta ta cire towel dinsa taga towel din yyi stain, still tayi tana kallon wajen, ya mike yace "What" girgixa masa kai tayi ta nufi toilet dake parlon da sauri, ya bi ta da kallo, cire towel din tayi xata wanke taji yace "Don't worry xan wanke....." Kasa juyowa tayi ta girgixa kai tace "No, xan wanke" juyo da ita yyi yace "Nace xan wanke" ta sauke idonta kasa bata ce komai ba, murmushi yayi yace "Yess" ajiye masa tayi ta nufi kofa ta fice daga toilet din sannan ta bar gidan gaba daya, tana isa gida gabanta ya fara faduwa, daga taje chemist a bata Magani tun uku saura sai after six take dawowa, mai aikinsu Blessing ce ke ta goge goge parlor, Samantha tayi kasa da murya tace "Mumy fah Blessing?" Blessing tace "Ta fita church tun daxun" Samantha ta sauke ajiyar xuciya tace "Bata tambaye ni ba" Blessing tace "No, tayi tunanin kin sha Magani kin kwanta a daki ne" Samantha bata ce komai ba sai dai tausayin kanta kawai take don kwata kwata Mumynta bata da wani lkcnta sai na church, duk ciwon da xata yi bbu abinda xae sa Mumy tayi fashin church in ma bata tilasta ta a hakan sun je church din tare ba, ga Abbanta ba wani xama yake ba ta dalilin aikinsa.
Chapter 10 · 0% Book details