← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 123

Sashe 89

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana kwance gefen Samha dake bacci yana kallo a tv wayarsa yyi ring, ganin Anty Maryam ce ya mike xaune ya daga, tace "Aliyu mun iso fa" yace "Toh gani xuwa Anty" daga haka ya tashi yana kallon Samha, bai tasheta ba ya dau mak
ulli ya fita, uku da yan mintuna ya isa park din, da fara'arsa ya nufi Anty Maryam dake tsaye rike da hannun autarta ya gaisheta, ta amsa da murmushi tace "Mun same ku lfya" ya duka ya dau kyakkyawar yarinyar da baxa ta wuce shekara hudu ba yace "Pretty how are you" yarinyar tace masa "Fyn" ya wara ido yace "Waow, then what's ur name" kallon uwarta tayi, Anty Maryam tace "Have u forgotten ur name?" Yarinyar tayi dariya tace "I am Ihsan" shafa kanta yyi yana murmushi yace "Welcome little Ihsaan" daukar jakarsu yyi yace "Anty ga mota can" Anty Maryam tace "Okay" daga haka suka nufi motar ya bude mata baya ta shiga ya mika mata ihsaan snn ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver, suna isa gida yyi parking ya juya yana kallon Anty Maryam murmushi dauke fuskarsa yace "Anty bata san fa ku ne bakin da xa su xo ba" tayi dariya tace "Au haba" ya bude motar yace "Wllh kuwa Anty" bude motar tayi ta fito da ihsaan ya dau kayansu yace "This our home Anty" Tace "Maa sha Allah, Allahu ya ci gaba da hada kanku" yace "Ameen Anty" tana biye da shi suka wuce balcony ya bude kofar parlorn suka shiga, Xaunawa Anty Maryam tayi da autarta, ya nufi fridge ya dauko masu ruwa da drink da cups ya ajiye ya xuba masu ya mika ma Ihsaan nata yace "Take pretty" Karba tayi tace "Thank you" yana kallon Anty Maryam yace "Anty ga ruwa bari in taso ta, bacci take" daga haka ya wuce daki, har lkcn kuwa baccinta kawai take, ya xauna kusa da ita ya dinga shafa mata fuska a hankali yana jan hancinta, ta bude lumsassun idonta tana kallon sa, yace "Baby har yanxu baccin dai" murya can kasa tace "Am very hungry" Yace "Toh muje ki gaida aunt din tawa sai ki ci abinci" Da sauri ta mike xaune tace "Ta xo?" Yace "Yea naje park na daukota yanxu" kamar xata yi kuka tace "Ae ban ma gama girkin ba doctor" yace "Khadija ta karasa maki dear" Shiru tayi bata ce komai ba ya mike ya dagota ta tashi tsaye ya bata veil din abayar ta yafa a kai, kallonta yake ganin yanda Abayar ya fito mata da cikin jikinta sosai, yaga tayi masa kyau ba kadan ba, kallon kanta tayi ganin irin kallon da yake mata ta daure fuska ta koma ta xauna tace "Ni baxan iya fita da kayan nan ba" Ya wara ido yace "Me yasa baby?" Tace "Bana so" yace "Ya fa maki kyau sosai dear plss mu je haka tana ta jira fa" kmr xata yi kuka tace "Ni baxan iya ba" yace "Toh sbda me" tace "Ni dai Hijab xan sa" murmushi yyi yace "See you, to ance maki bata da ido ne, ko me xa ki sa ai ba boyuwa abinda kike boyewa xai yi ba" kallonsa take kmr xata yi kuka ta wani hade rai, yyi dariya ya dagota ya rungumeta ta baya yana shafa cikin yace "Baby plss mu je tana ta xaune parlor fa ita kadai" daga haka ya kama hannunta suka fita tana nonnokewa ita a dole kunya, suna shigowa parlon ta tsaya cak tana kallon warce ke xaune tana kallonta murmushi dauke fuskarta, wani kara tayi ta nufeta a guje, har cikin ransa yaji uban tsallen da ta daka, ita kanta Anty Maryam sai da tace "Ke kina da kai kuwa Daughter" bata ko saurareta ba ta fada kanta ta kankameta tace "Antynahh dama ke ce" Anty Maryam tace "Xa ki ji ma kan ki ciwo fa, kina da kai ma kuwa" Shi kam sai kallonsu yake, can ta sake Anty ganin Ihsan ta rungumeta ita ma tace "Anty me yasa baki taho da Asiya da Farouq ba" Anty Maryam tace "Suna gun grannynsu" Rasa inda xata sa Auntyn tata Samha tayi da ganinta tayi farin ciki ne ba na wasa ba, duk sai Anty Maryam taji tausayinta barin ynda taga ta rame, ganin ba kyale Antyn xata yi ba Abuturrab yace "Anty ku yi sllh ku ci abinci, kun kwaso hanya fa" Sai a snn Anty Maryam ta yakice ta jikinta ta mike suka wuce daki, har bedroom ya kai masu abincin don bai ga alamar Samha xata yi hakan ba, Anty Maryam tayi dariya tace "Aliyu kai ne da wahala haka" yyi murmushi yace "Toh Anty naga taki kawo maku ne, kuma da ita ke jin yunwa bbu me kwanciyan hankali sai ta ci" Samha dake jikin Anty Maryam ta daure fuska ta turo baki, ya juya ya fita dauko sauran abincin, Anty Maryam tace "Ji shashanci daga yana maki wasa sai ki hade rai ki cunno baki gaba" tace "Bana son wasan" Anty Maryam tace "Toh ina laifinsa, naga dai duk ni yake ma hidimar ko baki ji dadin hakan ba" tace "Toh ai nima nayi masa da nasa yan uwan suka xo" Anty Maryam ta hade rai tace "Toh ya ishe ki bana son fitsara, yaushe kuma kika xama fitinanna" Samha bata ce komai ba ta dauke kai, a haka Abuturrab ya shigo ya samesu ya ajiye abincin yace "Ga shi Anty, ku ci abinci" Anty Maryam tace "Sannu Aliyu nagode" satan kallon Samha yyi ya fita, ba dau lkci ba ya dawo kuma rike da plate din abinci ya ajiye gabanta yace "Kin ce kina jin yunwa ga abinci" kallon abincin tayi tace "Am nt any longer" Ajiye ma Ihsan abincin yyi yace "Pretty ke ki ci" Anty Maryam dai kallonta kawai take ganin har lkcn ita fushi take, murmushi kawai tayi ganin condition dinta ta kuma san ba laifinta bne, tunanin irin abubuwan da uwarta tayi lkcn da take dauke da cikinta take da irin wahalan da ta sha, can tace "Daughter daga magana sai fushi, to yi hakuri" ita dai bata ce komai, har Anty Maryam ta gama cin abinci Samha na xaune ta xuba ma tv ido, Anty Maryam tace "Yauwa daxu kin ce min yan uwansa sun xo?" Sai a snn Samha ta kalleta tace "Ehh" Anty Maryam tace "Amma bnda Mum dinsa koh?" Tace "A'a kanwar mum dinsa ce sai sisters dinsa biyu" Anty Maryam tace "Ayya, did they stay long?" Ta girgixa kai tace "Just 2 days suka yi" tace "But are they okay" Samha ta kwantar da kanta tace "Yes his mum sis is very kind, har da zinari ta ban na dan kunne, sisters dinsa kawai ne basa so na" a hankali ta kare maganar, Anty Maryam tace "Don't worry duk xa su so ki kin ji Daughter, everything is just time" Daga haka suka dinga hira har aka kusan Magrib, shi kuma Abuturrab yana bedroom dinsa da Ihsaan suna kallon cartoon, yana yin alwala yace "Pretty kije Mumy ta sa maki cartoon a can dakin xan je masallaci" tana fita ya wuce masallacin, Anty Maryam na idar da sllh ta kalli Samha tace "Ke ko ki d'an yi kara ki dinga yin sllh bakya yi koh?" Samha ta kalleta tace "Anty ae baya cewa in yi" Anty Maryam tace "Sai yace maki daughter," murmushi tayi tace "Toh xan na yi Anty" Anty Maryam tace "You still don't have interest in joining us koh" tana murmushi tayi maganar, Samha tayi dariya tace "Uhm Anty ae bance haka ba fah" Anty Maryam tace "Ko akwai abinda yake maki that's prohibited in Christianity?" Kmr xata yi kuka tace "Eh mana...." Anty Maryam ta d'an yi shiru tana kallonta, sai kuma a hankali tace "Gaya min me yake maki Samantha?" Ta turo baki bata ce komai ba, Anty
Maryam tace "Noo ki gaya min kar ki ji komai"
*Haske writers asso*
[11/27, 7:18 PM]
+234 703 709 9528
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
81......
Chapter 89 · 0% Book details