← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 123

Sashe 67

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai kusan karfe bakwai da rabi Samha ta tashi ta ga baya dakin, mikewa tayi ta nufi gun da kayanta yake ta dau brush da toothpaste ta shiga bathroom, bata yi mamakin ganin har yyi wankansa ba, tana gamawa ta fito daure da xani, ta isa gun kayanta ta dau wanda xata sa, tana durkushe gun har lkcn ya shigo dakin, kallo daya tayi masa ta dauke kai, ba karamin kyau yyi cikin kananun kayan jikinsa ba, tayi karfin halin mikewa rike da kayan a hannu ta yi hanyar bathroom, da ido ya bita kafin yayi maxa ya rikota, ta hade rai tace "Doctor bana son haka kaya xan je in...." Yace "Ba gaisuwa?" Turo baki tayi tace "Ban sa kaya ba ae" K'ara ta sakar masa a rikice ta rike xaninta ganin kwancewa xai yi tace "Bana son haka doctor, i don't like it..." Sae kuma ta fashe da kuka, ya rungumota hade da lumshe ido murya can kasa yace "Good morning wife...." Daga haka ya kai bakinsa nata, tun tana turasa tana son kwace kanta har dai ta hakura, kamar me rada ta ji yana ce mata "Are you still on ur period?" Bata iya ta basa amsa ba, yayi tambayar ya kai sau uku amma shiru, saitin kunnenta taji yana cewa "Talk plss dear" sai a snn ta bude ido da kyar, ae lkci daya wani karfi ya xo mata ta turasa a rikice ta fara ja baya tace "Doctor" fixgota yayi ta fashe da kuka sosai tace "Plss ni ka bar ni" saketa yyi ya mike daga gadon ya fice daga dakin, ko ina na jikinta rawa ya dinga yi ta mike ta dau kayanta ta shiga bathroom.

Ta kusa minti talatin da fitowa kafin ya dawo dakin, ya ajiye ledan hannunsa ya kalli inda take yace "Breakfast" fingers dinta take fidgeting bata ce masa komai ba, yace "You hurry up kafin in dawo" daga haka ya fita, ta bi sa da ido kafin ta murguda baki ta mike ta bude ledan, irish ne da kwai da plantain, bata wani ci sosai ba sbda tea take son sha, kwanciyarta tayi kan gado har ta fara bacci ya shigo dakin, ya karasa ya xauna gefen gadon yana kallonta.

Hannu ya kai fuskarta ta bude ido da sauri ta mike xaune, wara mata ido yayi yace "Ki shirya yanxu xa mu je gun Anty" ba musu ta mike ta nufi gun da hijab dinta yake ta dauka, yace "Baxa ki yi kwalliya ba" ta d'a
n kallesa kafin ta dauke kai tace "Meye shi?" Hijab dinta ta shiga sa wa ya mike ya isa bayanta tana juyowowa ta ja baya da sauri yace "Nuna maki xan yi meye shi" murmushi tayi ya jawota jikinsa yace "Hakan ma kin yi kyau sosai baby kar a kallan min ke" Yana rike da hannunta suka fita.

Kawar Anty Maryam ce ta masu kwatancen gidan a waya suna isa ya ba mai adai daitan kudinsa snn ya kira yace ga su a waje, Anty Maryam ce ta fito shigo da su gidan, Abuturrab ya gaida ta kansa a kasa ta amsa tana tambayarsu ya suke, har parlon gidan suka shiga bayan ya gaisa da Hajiya Salamatu da kawarta yace xai je ya dawo anjima, daga haka yayi masu sallama ya d'an saci kallon Samha kafin ya fita parlon, barin parlon kawar Hajiya Salamatu ma tayi Anty Maryam ta kalli Samha tace "A ina ku ke yanxu?" Kanta a kasa tace "Hotel" Hajiya Salamatu tace "Ina yace maki xa ku daga nan?" Girgixa kai tayi tace "Ni ma ban sani ba" Duk suka yi shiru, can da Hajiya Salamatu tace "Ya ma sunan ki?" Samha bata dago ba sai wasa take da yatsunta a hankali tace "Samha ake ce min yanxu" Anty Maryam ta bude ido tace "Samha?

Wa ke ce maki hakan?" Tace "Shi yake cewa haka duk inda muka je" Hajiya Salamatu tayi murmurshi tace "Yanxu Samha ba ki sha'awar Musulunci" Samha bata ce komai ba bata kuma dago ba, Anty Maryam ta girgixa mata kai alamar ta bar xancen, mikewa Anty Maryam tayi ta dawo kusa da ita tace "You tell me the truth Samha, abu ya taba shiga tsakaninku da shi" k'in dagowa tayi har lkcn kuma bata ce komai ba, Anty Maryam ta dago kanta tace "Nasan ba kya karya daughter kar ki fara yanxu" A hankali ta girgixa kai, Anty Maryam tace "I didn't ask you to shake ur head ki bude baki ki min magana" Da kyar tace "Bbu komai Anty" Hajiya Salamatu ta dawo kusa da su tace "Kar fa ki ji komai Samha, kar ki boye mana komai" ta kalleta tace "Allah ni bbu abinda ya shiga tsakaninmu" Anty Maryam tace "Na yarda daughter, nasan kuma irin tarbiyar da mum nd Dad suka baki" Hajiya Salamatu ta cire hijab din jikinta tana kallon gashinta tace "Kitso xa ayi mata ko retouching?" Anty Maryam tace "Tayi retouching kawai koh" mikewa Hajiya Salamatu tayi tana kallon Samha tace "Toh tashi mu je Samha akwae saloon nn anguwar ai" daga haka ta shiga ciki gun kawarta don cewa xa su saloon, tana dawowo tace "Sai ki hada abinda ya kamata kafin mu dawo Maryam" daga haka ta kama hannun samha suka fita, cikin awa daya aka gama gyaran gashin aka rangada mata lalle mai kyau ba mai yawa ba snn suka dawo gida, Anty Maryam sai murmushi take ganin ynda 'yar tata ta fito, Hajiya Salamatu na kallon Samha tace "Yaushe watan ki ke tsayawa?" Samha ta girgixa kai tace "Gobe xan gama" abubuwan da ya dace Hajiya Salamatu duk tayi mata a spare room dake gidan, ita dai Anty Maryam sa su gaba tayi.

Sai kusan bayan la'asar Anty Maryam ta kira Abuturrab bayan sun mata nasiha sosai, godiya sosai Abuturrab ya dinga yi masu, ita kam Samha bnda kuka bbu abinda take, Antyn ta taji tausayinta sosai, da kyar ta yrda ta tashi Anty Maryam na rike da ita suka fita daga parlon, har bakin titi ta rakasu, sai da suka samu adai daita snn ta juya ta koma duk jikinta a sanyaye, rufe fuskarta tayi da abayar jikinta sae kuka take, ya rasa ta inda xai fara lallashinta, har ransa ya dinga jin tausayinta ya ji kmr ya rungume abarsa, kafin su isa hotel din har hijab dinta ya jike da kuka, ai suna shiga gate ya rungumeta bai damu da kallo da ya dawo kansu ba ya ja ta xuwa karkashin bishiya ya xaunar da ita kan kujera ya durkusa kan kneels dinsa gabanta da damuwa yace "Kar ki fasa min xuciya wifee, are u regretting marrying me?" a hankali take girgixa masa kai har lkcn fuskarta boye a hijab, ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace "I love you Samha, ina son ki, son da ni kai na ban san irin sa ba, i knw i will love you till my very last breathe wife, we re going to start a new life full of happiness, love nd affection, i will be ur everything, i will never disappoint you Pearl.... bbu wata bayan ke Jewel....

Look at me wife ko xan ji ddi plss i beg you" a hankali ta xame hannuwanta tana kallonsa da idanuwanta da ya kada, murmushin jin ddi yyi ya kamo hannunta, ita ma tayi murmushin a hankali, mikewa yayi ya dagota ya rungumeta gam, boye fuskarta tayi a jikinsa ganin irin kallon da ake masu a haraban hotel din.
*Haske writers asso*
Alhmdllh am feeling much much better now, a big tnx to my fcbk fanz for their prayers and everyone Allah ya sa mu dace, My Course mates Nafi, Sophie, Hussy.... tnx for the Jinya Allah bar mu tare mu yi ta fada, My fellow Biochemist mates tnx all for the prayers too sai mun hadu a Dept, My Nafeesat Dut. ina yin ki kawata da bata bacci idan ban yi ba, Jiddo is now Alhmdllh Allah bar xumunci.

My FUD fans...

Khaleesat is saying Hi....

Lng live fudites, lng live we Biochemist
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
62....

Washegari tun da sassafe Abuturrab ya gama shirinsa ya shiga shirya masu kayansu don kafin karfe tara yake son su bar Zaria, har ya fita ya siyo masu breakfast ya dawo bacci take bai kuma tashe ta ba, barin dakin yyi ya fita haraban hotel din yyi xaman sa, kiran Anty Maryam ne ya shigo wayarsa ya daga ya kai kunne hade da gaisheta, ta amsa tace "Dama wllh jiya na mance bn ba daughter sako ba, idan ba damuwa ka taho ka karbar mata don Allah" yace "Toh Anty xan xo ynxu" mikewa yyi ya koma ciki, wnn karan tada ta yyi, ta mike xaune yace "Am coming back soon dear ga breakfast na ajiye maki" tace "Ina xa ka?" Yace "Anty xata bada sako a kawo maki wai" kai ta gyada masa ya mike yace "You can still go back to sleep" mikewa tayi ita ma tace "Allah kiyaye hanya," daga haka ta shiga bathroom, murmushi yayi ya dau kudi da xai dauka ya fita.
Chapter 67 · 0% Book details