← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 123

Sashe 11

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari asabar da safe Mumy ta shirya xa su Kaduna da tawagar pastoci kamar ta, Samantha na bacci ta tada ta tace "Rebecca you take care of ur self plss xan tafi yanxu, idan baxa ki xauna tare da Blessing ba ki tafi gidansu Stella, by the grace of God ran Monday ko Tuesday xa mu dawo, ki tabbatar kina shan maganin ki...." Samantha dake ta murxa ido tace "Toh Mumy Abba yaushe zai dawo?" Mumy tace "I don't know, just take care of ur self and make sure kin je church anjima da yamma da gobe da safe even if you cannot go to lesson" Samantha tace "Ohk, amma ni gidansu Stella xanje, Blessing ta tafi gida kawai" Mumy tace "Ohk better, ki kuma tabbatar kin tafi da wayar ki ni ban ga amfanin wayar nn naki da kike yasarwa a daki ba" Samantha tace "Toh xan je da shi Mumy, ki taho min da abu me ddi kin ji" Mumy ta nufi kofa tace "Ohk, tashi ki yi wanka ki ci abinci ki sha magani" daga haka ta fita, Samantha ta kalli agogo taga karfe takwas yayi, hamma tayi ta mike ta shiga bathroom, wanke baki tayi, tayi wanka snn ta fito ta kimtsa jikinta ta shirya cikin doguwar rigarta 'yar kanti pink colour da flowers din blue, ta fito da plain veil dinta blue colour ta daura a kai, bata wani yi make up ba sai eye pencil da tasa a ido snn ta sauko, tea kawai ta iya sha dan idan tana period bata iya cin abinci, tana xaune parlor tana ta kallo har Blessing ta gama aikinta tace "Blessing xa ki iya tafiya gida sai Monday nima gidansu Stella xan je ynxu" ba a wani dau lkci ba Blessing ta wuce.

Samantha ta kashe kayan wutan gidan gaba daya misalin karfe tara ta hada kayanta kala uku ta dau bible dinta da textbooks na karatu da yake saura sati uku su fara Waec, a hannu ta rike wayarta ta fito ta kulle main gidan tayi ma mai gadi sallama ta wuce, tafiya take kamar mai tausayin kasa har ta iso gate din gidansu Abuturrab, har ta wuce ta dawo ganin kamar gate din a bude yake ta leka, ai ko ta gansa xaune yana sanye da singlet da short hannunsa rike da lighted cigarette, ido hudu suka yi ta juya da sauri xata bar wajen ya mike yace "Frnd" bata ko juyo ba, ya wurga taban hannunsa ya fita gate din, Sauri ya ga tana xubawa yace "Uhm not even a good morning frnd?" Tsayawa tayi bata juyo ba, ya rungume hannayensa yace "Hmm ae shikenan...." Juyowa tayi ta masa murmushi tace "Good morning" yafito ta yyi, ta make kafada, yayi shiru yana kallonta, ta langwabar da kai tace "lesson xan je" yace "Ohk" daga haka ya juya ya koma cikin gate, bin sa da kallo tayi a sanyaye can ta bi bayansa, tsaye tayi bakin gate din tana kallonsa tace "Are you angry" ba tare da ya kalleta ba yana tsaye kusa da karensa yace "No!" Shiga gate din tayi ta rufe ta karasa kusa da shi kamar xata yi kuka tace "You are" ya juya yana kallonta yace "Am not" murmushi tayi tace "Am sorry Dr, um naga baka shirya bane" rungume hannayensa yayi yace "Uhm ban shirya ba kamar ya?" Sunkuyar da kai tayi tana murmushi tace "Kila fa baka yi wanka ba...." Murmushin yayi yace "Toh mu je ki min" xaro ido tayi sai kuma ta juya da sauri xata bar wajen ya rikota yace "Ae sai kin min" boye fuskarta tayi a kirjinsa tace "Nooo Doctor lesson xan....." Rufe bakinta yayi ya ja ta suka shiga parlor ya rufe kofar da makulli.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
_Happy Belated born day Asmy B Aliyu, age with grace dear sis, Allah ya karo shekaru masu albarka ya nuna mana auren ki mu xo mu sha biki_
8.....

Kwace hannunta tayi kamar xata yi kuka tace "Doctor...." Yace "Toh in ruwan ki da rashin wanka na?" a hankali tace "Toh yi hakuri...." Murmushi yayi ya juya ya nufi daki ta bi sa da kallo, can ta ajiye jakar hannunta ta xauna tana kallon program din da ake a tv, bayan minti kusan ashirin taji an danna bell, mikewa tayi da sauri tana kallon kofar, ji tayi ance "Ohh ya Abuu me yasa kake kulle kofa ne yanxu, ni dai ka bude min Mami ce ta aiko ni wllh...." Da sauri Samantha ta mike ta shige bedroom dinsa ta tura kofar tayi lamo jiki, kwata kwata bata ji fitowarsa ba sai gyaran muryarsa da taji a bayanta ta juyo da sauri, daure yake da towel a waist, bakin gashin kirjinsa ya kwanta luf luf don ko goge jiki bai yi ba, a rikice ta juya xata bude kofar dakin ya riko hannunta kamar xata yi kuka tace "Doctor ur sister is outside....

Shi yasa na shigo" key ta ga yasa ma kofar ta juyo da sauri tana kallonsa a tsorace, ya wara ido yace "Tell me what you are afraid of?" Girgixa kai tayi da sauri tace "Noo...

Nothing" yayi 'yar dariya yace "Why is it that girls always have this negative thought?" Juyawa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Am not a bad person, erase that thought off ur mind immediately" a hankali tace "Ohk!" Ya kama hannunta ya nufi gado da ita ya xaunar da ita gefen gadon, snn ya dau kayansa ya shiga bathroom, ba a dau lkci ba ya fito sanye da kananun kaya ya dau turaren gaban mirror ya feshe jikinsa da shi ya karasa kusa da ita ya feshe ta ita ma, boye fuskarta tayi jikin gado tana murmushi, can ta dago a hankali taga bbu shi a dakin, mikewa tayi tana kare ma dakin kallo, ko ina fes except from the bed that's untidy, murmushi tayi ta bude curtains din room din ta fara gyara gadon, cikin yan mintuna ta gama ta fita xuwa parlor, xaune ta gansa cup din coffee a hannunsa, ta wuce kitchen ta dauko sweeper da mop ta dawo ya bi ta da kallo har ta shiga bedroom, tana fitowa yace "Well done, thank you" tayi murmushi ta kai abubuwan hannunta kitchen ta fito, yace "Come and make a tea for ur self" tace "Nayi breakfast" yace "Nasan kin yi ae, karawa xa kiyi" tace "Noo na koshi sosai" kan kujera ta nufa ta dau jakarta yace "Ina xa ki?" Tace "Lesson!" Yace "Lesson da jakar kaya?" Ta kallesa tace "Aa xan ajiye gidan wasu family frnds dinmu ne, Mumy ta tafi Kaduna, Abba baya nan, ni kadai baxan iya zama a gida ba shine xan je gidansu" Abuturrab ya ajiye Mug din hannunsa yace "Sbda kina tsoron abu xai cinye ki?" Dariya tayi tace "A'a ni bana tsoro kawai bana son in xauna ni kadai ne" yace "Ohk...." Xaunawa tayi kan kujera ta dalilin ciwo da taji cikinta ya fara mata, kamar ko ya sani yace "Kin samu lafiya Yanxu?" Kai kawai ta gyada masa ta jinginar da kanta jikin kujera, ya bude warmer din dake dauke da wainar shinkafa ya debi biyu ya kalleta ya ga kallonsa take, yace "Taho mu ci" a hankali tace "Masa?" Ya gyada mata kai, tace "Sa min guda daya" yace "Sauko mu ci dai" ba musu ta sauko ta dawo kusa da shi ya kara masu guda biyu, ya debi rich vegetable soup din dake wani warmer a waje daban ya fara ci da spoon, dauka tayi ita ma ta fara ci, ganin yanda take ci kamar ana tilastata yace "Bai maki dadi ba ne" girgixa masa kai tayi da sauri tace "Yayi dadi...." Yace "Then me yasa kike haka da fuska" kamar xata yi kuka ta ajiye Masan hannunta ta kwanta gefensa tace "My tummy" sai kuma ta mike ta koma kan kujera ta kwanta, bin ta yayi da kallo ya ajiye spoon din hannunsa yace "Ya fara maki ciwo" kai ta gyada masa lkci daya hawaye ya cika idonta, a hankali yace "Sorry" mikewa yayi ya shiga bedroom sai ga shi ya fito da allura da Magani ya dawo kusa da ita ya shiga hada alluran, yana gamawa ya kalleta yace "Toh juyo in maki sai ki sha Magani" ba musu ta juyo har xata daga gown din sai ta tsaya kuma, kallonsa tayi hawayen da ke makale idonta ya silalo ta juya masa baya tace "Bude min zip din pls" bude zip din yyi a hankali, ta cire hannun gown din don akwai ves jikinta, ta sauke gown din kasa yanda xai iya yi mata alluran snn ta juya masa baya ta kwanta, daukar syringe din yayi ya mata alluran ta juyo tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "Sorry!" Ya mike ya dauko table wata ya bata maganin ta sha snn ta koma ta kwanta, bayan awa daya ya kalleta ya ga idonta biyu, yace "Ya daina" ta gyada masa kai, har bayan azahar tana gidan a kwance, yana dawowa daga masallaci bayan anyi la'asar ya durkusa kusa da ita yace "Baki ci abincin ba har ynxu" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" mikewa yayi ya shiga daki ya shirya ya fito da makullin mota yana kallonta yace "Xan je clinic in dawo yanxun..." Mikewa tayi tace "Gida nima xan je" ya hade rai yace "Noo kiyi kwanciyar ki kina tashi cikin xae fara, don't worry i will lock the door" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, har shidda bai dawo ba, ta sauko da kyar jin cikin xae fara mata ciwo ta xuba abincin da aka kawo masa daxu ta ci kadan ta dau sauran magungunan da ya bata ta sha ts koma ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa..
Chapter 11 · 0% Book details