← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 123

Sashe 45

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Abuturrab yace "Har kin dawo?" Kai ta gyada masa tace "Tace xa mu je saloon gobe da yaranta" Shiru yyi yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Allah ya kai mu" ciki ta shiga tayi kwanciyarta tun da tace kar tayi girki, fatima ce ta kawo masu abinci kusan Magrib bbu sallama ta shigo parlon, Abuturrab na xaune yana kallo a system Samha na gefensa ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa idonta a kan system din ita ma, a tare suka daga kai suna kallonta, ko kunya taji sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Assalamu alaikum" Samha ce kawai ta amsa ta karaso ta ajiye abincin tace "Mum tace a kawo" Samha tace "Mun gode" daga haka ta juya ta fice.

D'an tsaki Abuturrab ya ja can ciki, Samha ta kallesa tayi murmushi bata ce komai ba.

Washegari khadija ce ta taho Balcony tana kallon Abuturrab dake duba newspaper da ya siya daxu da ya fita karo masu kaya a boutique, gaishesa tayi ya amsa tace "Wae Ummin mu in kira Anty Samha idan ta shirya" Abuturrab yace "Toh ga ta nan xuwa, ya sunan ki?" Tayi murmushi tace "Sunana khadija" yace "Alryt xan fadi mata Khadija" juyawa tayi ta wuce ya bi ta da kallo ganin banbancinta da yayarta, baxa ta wuce shekaru sha bakwai ba amma tafi yayar hankali, yana xaune parlor samha ta fito da hijab har kasa tana kallonsa, murmushi yyi yace "Cute" murmushin ita ma tayi, yace "Sae kun dawo but kar ki bari a dinga kalle min ke fa" dariya tayi yace "Yeah nikab ma xan siyo maki" kofa ta nufa ya bi ta da ido har ta fita, jiranta ta samu su Fatima na yi, Hajiya Hajarah tace "Toh sae kun dawo, Allah ya tsare hanya" driver ne xae kai su saloon din, fatima ta shiga gaban mota, Khadija da Rabi'ah suka xauna baya tare da Samha, su kadae suke mata hira har suka iso saloon din, fatima ta bude mota ta fita su ma suka fita suka bi bayanta xuwa cikin babban saloon din, khadija na kallon fatima tace "Big sis a fara yi ma Anty Samha koh?" Fatima ta kalli Samha ganin kallonsu take bbu yabo bbu fallasa tace "Alryt" daga haka taje tayi xamanta kan daya daga kujerun Saloon din sae dae can kasar xuciyarta ji take kamar ta shake yar uwar tata, Samha da Rabia aka fara ma gyaran gashin don akwae mutane saloon din, tun da aka bude kan Samha Fatima da duk yan saloon din ke kallo, matar mai gyara mata gashin sae cewa take "Maa sha Allah you've got a very fine long hair" Samha ta kirkiri murmushi bata ce komai ba sai dai duk a takure take ganin yanda ake kallonta, cikin minti ashirin aka gama mata ta mayar da hijab dinta da sauri, aka kama kan fatima sae dai ita kitso tace xata yi, ita din ma ba baya ba gun gashi, mai saloon din na kallonta tace "Baxa kuyi lalle ba Madam?" Khadija tace "Xa muyi" wani kallo Fatima ta watsa mata tace "ke da wa, waye xae jira kuyi lalle?" Khadija tace "Ae na tambayi Ummi tace mu yi" dauke kai fatima tayi bata ce komai ba, khadija aka fara yi ma snn Samha da taki yarda da farko har sae da Khadija da Rabi'a suka tilastata, suna saloon din har aka kira azahar, Khadija ta kalli Samha tace "Mu shiga daga ciki mu yi sllh Anty Samha" shiru Samha tayi sai kuma ta mike kamar mara laka ta bi bayanta, Khadija ce ta fara alwala a toilet ta fito snn Samha ta shiga, tsura ma tap din ruwan ido tayi, lkci daya xamanta gidan kanwar Abbanta ya fado mata, a hankali ta bude ruwan ta shiga alwalan kamar yanda take yi a kaduna da yaran Aunt dinta, tana gamawa ta fito ta ga Khadija ta shimfida mata wani darduma ta saka hijab dinta ta hau kan darduman babu abinda ta mance a ynda ake sllhn sae d'an abinda baka rasa ba, har hakan ya bata mamaki, tana idarwa Khadija tace "Me xa a karbo maki?" Murmushi Samha tayi tace "Bana jin yunwa..." Khadija bata ce komai ba ta fita, samha ta mike ta bi bayanta, snacks da drinks Khadija ta sa driver ya karbo masu, bbu yanda samha ta iya haka ta karba, ba su suka bar saloon din ba sai kusan karfe uku, part din su suka tafi gaba daya, Hajiya ta yi masu sannu da xuwa tana kallon Samha tace "Har kun dawo?" Samha ta gyada mata kai, tace "Toh sannun ku daughter, bari a xubo maku abinci" Samha tace "Ae mun ci" Hajiya bata saurareta ba tasa mai aiki ta xubo masu abinci gaba daya, har aka yi la'asar tana parlon, Hajiya tace "Khadija ku shiga ciki ku yi sllh" Khadija ta kalli Samha tace "Muje daki muyi sllh" ba musu Samha ta mike ta bi bayanta xuwa bedroom dinsu, kamar daxu haka tayi sllhn suka fito bayan sun idar, nan Hajiya tasa mai aiki ta xuba mata abinci ta kai ma Abuturrab, ta karbi abincin tayi godiya ta fita, Kwance ta samesa parlor yana bacci, ta ajiye abincin hannunta ta durkusa kusa da shi tana kallonsa tace "Doctor!" Bude ido yayi a hankali, ta langwabar da kai tace "Anyi sllh fa" ya mike xaune yana shafa fuskarsa, tace "Are you okay?" Girgixa mata kai yayi yace "Am having headache..." Tace "Toh kayi sllh sai kaci abinci then you take drugs" tana magana amma ido da hankalinsa na kan kunshin hannunta, ta bata rai tace "Ina maka magana" kamo hannunta yayi murya can kasa yace "Waow, baby kunshin yayi kyau sosai, i like it" ta kwace hannunta tace "Thanks" ya d'an marairaice mata yace "Toh baxan ga gyaran gashin ba?" Murmushi tayi ta cire Hijab din jikinta tana kallonsa, ya lumshe ido underneath his breathe yace "I have always loved you from the very first day i saw you Samha!" Kallonsa kawae take, ya bude ido a hankali yace "Tell me daga ina kike that very Night?" Murmushi tayi xata mike ya jawota jikinsa yace "Noo, talk to me baby" murmushin ita ma tayi tace "I don't want to talk about that now!" Yace "Noo plss baby..." Ganin yanda ya zuba mata manyan idanuwansa ta sauke kanta kasa a hankali tace "My frnd forced me to her birthday party, ni ban san it's an indecent party ba, shine na gudu na bar wajen..." Bude kofar parlon aka yi ta xame jikinta da sauri dai dai lkcn da fatima ta shigo, ta sunkuyar da kai ta karaso parlon, Samha ta xamo kasa a hankali ta xauna, takardun hannunta ta mika ma Abuturrab tana kallonsa tace "Ummi tace in baka wannan..." Mikewa yyi bbu yabo bbu fallasa yace "Drop it!" Daga haka ya shiga bedroom, ta bi sa da ido, Samha ta kirkiri murmushi da kyar ta karba tace "Bari in ajiye" sake mata fatima tayi ta juya ta fice daga parlon.

Samha ta mike a sanyaye rike da takardun ta shiga dakin da ya shiga, xaune ta gansa gefen gado ta durkusa kusa da shi tace "Me yasa kayi mata haka?"
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
_Tohm ya na iya tunda Ummu Ilham na da 'yan adawa irinsu Chamo, Zaarah, Teemahluv, Deezoh...

Gasu nn dai
su ma kuma sun ce sai fa an masu baxa su yarda ba, toh ina ku ke gashi nan sai ku kacalcala shi bbu ruwana naku ne_
Dagota yayi ya xaunar da ita gefensa yace "Kinsan me Baby?" Ta girgixa kai yace "Hajiya ta ban aiki...." Samha tace "Aiki kuma?" Yyi murmushi yace "Yeah she's also a medical doc...." Tace "Uhm hw did she know you re a doc?" Yar dariya yyi yace "Taga bana xuwa aiki shine ta tambaya nd i told her nayi ma Abbana laifi shi yasa na bar kano..." Xaro ido tayi tace "You told her everything??" Kamo hannunta yayi yace "No i didn't love!" Sunkuyar da kanta tayi, ya daura hannunsa kan dogon gashinta murya can kasa yace "Haka xa ki haifa min yara masu irin gashin nn kin ji" da sauri ta fara kkrin sauka daga kan gadon yaki saketa, kmr xata yi kuka tace "Doctor baka yi sllh ba fa..." Dariya yayi yace "Sai in tare xa mu yi bby" ta kallesa tace "Uhm ae yau na yi!" Yace "Dagaske?" Tayi murmushi tace "Yeah nayi Zuhur a saloon, nayi Asr a gun su Ummi" ya wara ido yace "Don Allah da gaske Baby, toh me da me kika ce a sllhn" wara ido tayi tace "Na fa ce maka ina yi a kaduna, rayuwar da nayi a kd a da yafi wanda nayi a kano da parent dina, am still missing my aunt, amma Mum dita ta rabamu wai she's putting me in the islamic way..." Abuturrab da ke ta kallonta yace "Toh me Abba yace?" Ta wara ido tace "Toh me xai ce?
Chapter 45 · 0% Book details