← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 123

Sashe 103

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba su suka bar asibitin ba sai kusan karfe tara, su Umma suka wuce gida, ta so su biya can gidan don a daukar ma Noor da babies kaya amma Col yace gobe Hajiya Mariya xata je ta dauko masu, ya shiga motarsa Abuturrab ya shiga gaban motar shi ma, Noor ta shiga motar Hajiya Mariya tare da Mami dake rike da yaran, suna isa gida ya bude motar fuskar nan tasa bbu yabo bbu fallasa ya fita, Abuturrab ya bi sa da kallo kafin ya fito ya rufe motar, Mami ta fito da yaran, Hajiya Mariya ma ta fito ta karbi daya a hannunta, tuni Abuturrab ya nufi balcony, Noor ta bi sa da kallo, dafa ta Hajiya Mariya tayi sai taji tausayinta ganin tun daxu take mata magana amma bata san tana yi ba, ta kama hannunta suka nufi cikin gidan, ba karamin farin ciki su Ramla da Khaleesat suka yi ganinta da suka yi ba, har hakan ya bata mamaki sosai, amma ta fi xaton sbda yaran da suka gani ne, Hajiya Mariya ta wuce dakin Mami da ita ta kwantar da yaron hannunta ganin bata xauna ba tace "Toh xauna mana Noor" xata xauna kasa ta nuna mata gefen gado tace "Xauna a nan" ba musu ta xauna gefen gadon, Mami ta shigo dakin ta ajiye yaron hannunta gefen dan uwansa snn ta fita Hajiya Mariya ta kashe Ac dake kunne ta bi bayanta, bin dakin Noor ta dinga yi da kallo ban da kamshin turaren wuta me dadi bbu abinda ke tashi, ko ina na dakin fes fes, bude kofa aka yi ta daga kai suka yi ido hudu da fatima, gabanta yyi mugun faduwa, tare suka shigo da Ilham da ta nufo gadon da gudu tace "Woawww, twins for ya Abuu...." Daga haka ta dau Hussain ta manna masa kiss ta rungumesa cike da farin ciki tana kallon fuskarsa tace "He is sooo cute...." Kallon Noor tayi tace "Ya Abuu missed you all...." Noor ta d'an kirkiri murmushi sai dai gaba daya hankalinta na kan tunanin me fatima ke yi gidan, yaushe ma ta xo gidan, Ilham ta mika ma Fatima dake tsaye yaron ta dau dan uwansa shi ma ta manna masa kiss tace "Little angel, welcm to d world, am assuring you papa Love's you sooo much" Fatima ta ajiye yaron hannunta tace "Allah ya raya" daga haka ta juya ta fita dakin, Noor ta bi ta da wani kallo, Hajiya Mariya ce ta shigo da abinci dakin, da kyar ta kora ilham dake jin kmr ta hadiye kyawawan yaran, ta xuba ma Noor tuwon tace "To sakko ki ci Daughter" a hankali ta sauko kasa kan rug, duk da yunwar da take ji, ji tayi gaba daya abincin bai ranta, fatima dai tayi mugun tsaya mata a rai, haka Hajiya Mariya ta dinga forcing dinta tana tura abinci har ta ci da yawa, ta hado mata tea shi ma ta shanye snn ta kwashe kwanukan ta fita, Mami ta shigo dakin tace "Kin yi wanka kuwa?" Kai ta gyada mata tace "Nayi" Mami tace "Yaran fah?" Tace "Umma tayi masu" fita Mami tayi ta je dakinsu ilham ta dauko mata riga me kauri ta kawo ta bata tace "Tashi ki canja sai ki kwanta ki huta kin ji" Noor tace "Toh" Mami ta juyo ta fita, mikewa tayi ta canxa kayan snn ta kwanta kan gadon a hankali duk jikinta a sanyaye, can ta yamutsa fuska jin cikinta na d'an ciwo, ta koma kusa da yaranta dake ta bacci tana kallonsu, ji tayi duk duniya bbu wanda take so fiye da su, Abuturrab ya fado mata ta d'an turo baki ta kwanta kusa da su hade da lumshe ido.

Hajiya Mariya na fita dama bedroom din Abuturrab ta shiga, jin yana wanka ta nemi gefen gado ta xauna, har dai ya fito bayan kusan minti ashirin, ganinta xaune ya nufo ta a hankali yace "Mum" tayi murmushi tace "Duk Samha ake ma wnn wankan Aliyu?" Bai ce komai ba ya xauna gefen gado yana goge gashinsa da karamin towel, ta kafa masa ido, can tace "Aliyu ban ji ka ce ma Samha komai ba, me hakan ke nufi?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Mun gaisa ai mum, tun a can gidan" Shiru tayi kafin tace "Toh shknn" ta mike ta nufi kofa ya bi ta da ido.

Tun Noor na daure ciwon da cikinta ke mata har ta kasa dauriyar kuma wajajen karfe daya da wani abu, sai juye juye take ga Hussain sai mutsu mutsu shi ma yake kusa da ita, Hajiya Mariya kuma na ta daya side din tare da Hassan, kuka Hussain ya tsala, Hajiya Mariya ta mike xaune ta kunna wutan dakin ta daukosa, ganin yunwa yake ji ta taba Noor da ta juya masu baya tace "Daughter tashi kiyi breastfeeding dinsa, he is hungry" da kyar ta mike xaune, Hajiya Mariya ta xagayo ta daura mata yaron kan kafarta jin Hassan ya fara taya d'an uwan nasa kuka ta xaga ta daukesa shi ma, Noor ta sauke rigarta, yaron na fara shan abincin ta ja baya da sauri jin wani ciwo da yafi Cramps axaba a kasan cikinta, yaron ya tsala ihu, Hajiya Mariya tace "Ya aka yi?" Cikin rawar murya tace "Mumy cikina ke ciwo" Hajiya Mariya tace "Ciki kuma?

Tun yaushe?" Da kyar tace "Tun daxu" lkci daya hawaye ya shiga sakko mata, tun fara kukan Hussain Abuturrab dake xaune kan darduma ya dinga kallon kofa, jin d'an uwansa ma ya dauka sai ya kasa daurewa ya mike ya nufi kofa, kasa fita yyi can dai ya koma ya xauna yana jin yanda yaran ke tsala ihu, Duk ynda Hajiya Mariya ta so ta lallashesu kin hakura suka yi, Mami da taji kukan ita ma ta fito daga part din Col ta shigo dakin, tace "Me ya samesu Mariya, sun ki karban maman ne" Hajiya Mariya tace "Wai cikinta ke ciwo Mami, gashi bbu feeding bottles bare a ba su ko ruwa ne" Mami dake kallon Noor da ta kife kanta da gado tace "Subhanallah, bari in masa magana toh" a bakin kofa suka kusa cin karo da Abuturrab da dauriyarsa ya kare, ya ja baya da sauri yana d'an kame kame, tabe baki tayi tace "Toh shigo" yyi murmushi yana shafa kai ya bi bayanta suka shiga dakin, idonsa ya sauka kan Noor da ta kife kanta har lkcn, kallonta ya dinga yi har ya karaso cikin dakin, Hajiya Mariya tace "Cikinta ke ciwo Aliyu, ko akwai abinda xa ayi mata?" Shiru yyi yana kallonta, Mami tace "Ko a tafi asibiti?" Ya girgixa kai yace "Noo, it's normal Mami" hararansa tayi tace "Na fi ka sani ai likita" murmushi yyi yace "Akwae alluran paracetamol bari in dauko...." Daga haka ya fita, Mami ta kalli Noor tace "Tashi ki bi sa kin ji, Allah ya sauwake" mikewa tayi da kyar tana dingishi ta fita daga dakin, kasa shiga dakin nasa tayi ta duka nn bakin kofa hawaye na sakko mata, yana bude kofar ta mike da sauri ya kusa cin karo da ita, ya kalli kofar dakin Mami kafin ya jawo ta cikin dakin ya kulle kofarsa, kan gado ya tafi da ita, ya sa ta xauna yana kallonta, ta ki yrda su hada ido, sai hawaye take, a hankali ya sauke rigar jikinta yyi mata alluran, ganin kukan da take ya jawota jikinsa ya lumshe ido, Lamo tayi tana shakar dad'da'dan kamshinsa, tana kuma jin yanda xuciyarsa ke bugawa, murya can kasa taji yace "I...i..." Sai kuma yyi shiru, ta lumshe ido jin jikinsa da dumi sosai, sun fi minti goma a haka ya janyeta a hankali ya mike ta bi sa da kallo har ya shiga bathroom, ba a dau lkci ba ya fito rike da bowl din ruwan dumi da karamin towel, kwantar da ita yyi ya matse ruwan towel din bayan ya daura kan abdomen dinta yana d'an danna mata, mikewa tayi jin xafi ta bata fuska xata yi kuka, ya mayar da ita ya kwantar, a hankali ya dinga yi mata har ruwan ya salance snn ya kai bathroom ya fito tana kallonsa ya fita dakin, kitchen ya sauka ya bude fridge ya dau lime biyu ya xuba ruwan xafi a cup ya matse lime din ciki snn ya koma daki, da kansa ya dinga bata ruwan lime din har ta shanye ya ajiye cup din, hada ido suka yi tayi saurin sunkuyar da kanta, ya jawota jikinsa a hankali yace "How are you feeling now?" Lumshe ido tayi tace "Fine" bai kuma ce mata komai ba, suna nn a haka har agogo yyi stuck din karfe biyu, murya can kasa taji yace "Thanks for the babies Samha" bata ce komai ba, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta ta kauda kanta, ya kamo hannunta yace "Why did you choose to leave Samha, you've caused me so much pains" Shiru yyi, ta koma baya a hankali tace "The babies...." Sai a snn ya kula har lkcn fa babies din sun ki hakura, ya mike ya fita, yana shiga dakin Mami tace "Ya jikin nata?" Yace "Da sauki Mami, bari a kai mata su xata iya basu abincin" Daga haka ya karbi na hannun Hajiya Mariya tace "Kai, wnn yara ba dai fitina ba kamar ubansu...." yar dariya yyi yace "Ke dai kawai don sun hanaki bacci ne mum, sae ma sun koma gun ki gaba daya" Dariyar tayi ita ma tace "Sae in xane su abu d'an sauki" yace "Toh baxa su ba, sai in kai su gun Yakumbo" yana magana ne yana kallon Mami da taki kallonsa ta mika masa Hussain ya fita da su yana murmushi, Hassan ya daura mata a kafa ya xauna yana lallashin dayan yana kallon ynda take basa abincin, bata ji ciwon kamar daxu ba, sai da yaran suka yi bacci duka snn ta kwanta, nn da nn bacci ya dauketa ita ma kmr xata shige jikinsu, ya jima xaune yana kallonsu, can ya d'a yi murmushi ya lumshe ido ya bude, ya hau gadon ya kwanta shi ma.
Chapter 103 · 0% Book details