← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 123

Sashe 83

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Am feeling sleepy" Murmushin da ya bayyana fararen hakoransa yyi yace "Koh?" Kmr warce ta tuno abu ta wara ido ta mike tsaye da sauri tana kallon pan din dake kan gas, kallonsa tayi kmr xata yi kuka tace "Doctor ya kone, i don't knw...." Rufe bakinta yyi ya ja ta suka fita daga kitchen din ya kaita daki ya xaunar da ita gefen gado, ya kanne mata ido yace "Ke fa kika hanani bacci daren jiya da shagwaban ki baby, ni ban yi bacci a bathroom ba da naje wanka sai kece xaki je kitchen kina bacci ki kona mana abinci?" Kallonsa take kamar xata yi kuka, yayi dariya ya shafa fuskarta a hankali yace "Toh yi hakuri wife, bari in shirya sai in fita in siyo mana breakfast, go nd take ur bath" turo baki tayi ta mike ta nufi bathroom ya bi ta da kallo yana murmushi, har ya gama shiryawa ya fita nearest fast food ya siyo abinda xae siyo ya dawo bata fito daga wanka ba, mamaki ne ya cika sa, ya ajiye ledojin hannunsa ya bude kofar bathroom din, kwance ya ganta cikin bathtub ta tara ruwa tana ta bacci ciki abunta, xaro ido yyi ya karasa wajen ya durkusa ya kashe ruwan yana kallonta murya can kasa yace "Toh fah" hancinta ya ja ta bude ido da sauri yace "Nan din ma baccin kika xo kina yi baby?" Kalle kalle ta fara yi, ya girgixa kai ya jawo sponge tana nonnokewa har ya gama ya fito da ita daki, gaba yasa ta har ta gama shiryawa kar ta kuma yin baccin, yana kallon lumsassun idonta yace "Har ynxu baccin kike ji koh?" Kai ta gyada masa yace "Toh bari kiyi breakfast sai ki kwanta" ta girgixa kai tace "Bana jin yunwa ynxu" shiru yyi yana kallonta, can yace "Alryt kwanta baby" kwanciya tayi kan gadon yyi murmushi ya mike ya fita don hado coffee, ko kafin ya dawo har tayi bacci, haka ya xauna kusa da ita ya tsura mata ido yana kallo, wani kyau na musamman yaga ta kara da haske, can underneath his breathe yace "Waow!" Juyawa yyi jin ringing din wayarsa ya mike ya isa gaban mirror ya dauka ya ga Ummi ce ke kiransa, ya langwabar da kai yace "Oops" bai yi budgeting fita da safe yau ba, a hankali ya daga wayar ya kai kunnensa ya amsa sallamarta snn ya gaisheta, tace "Kun tashi lfya boy?" Yace "Alhmdllh Mami" tace "To Madallah, hope baxan takura ka ba boy xan sa ka aiki coz m nt around...." Yace "Not at all Mami" tace "Alryt, fatima nake son ka dauko daga makaranta, Asthman ta ne ya tashi, xan baka number kawarta ku dinga communicate har ka je can...." Yace "Subhanallah, suna lectures weekend ne?" Tace "Not at all, ae tafi sati biyu a schl, a hostel take" yace "Alryt mami, buh is she with her inhaler?" Tace "They can't find it, daga can kawai ka wuce clinic da ita ko allura ne ayi mata" yace "Toh Mami bari in tafi ynxu" daga haka ya katse wayar ya mike yana kallon Samha, lullubeta yyi da bargo, ya kashe Acn dakin ya sake mata curtains, ya daura lips dinsa kan forehead dinta yace "I wil be right back wife" daga haka ya dau makullin mota da wayarsa ya fita, yana warming motar message ya shigo wayar yaga Ummi ce ta turo masa number kawar fatima Salima, sai da ya bar compound snn ya kira number, ba a jima yana ringing ba aka dauka yyi sallama, daga daya bangaren aka amsa, yace "Salima ce?" Tace "Yea..." Yace "Ya jikin fatiman?" Tace "To ga ta nan dai" yace "Kuna hostel din ne?" Tace "Ehh wai da clinic xamu wuce ynxu it's getting worst" yace "Noo kar ku je ina hanya ynxu" daga haka ya katse wayar, yana isa makarantar ya kuma kiranta tayi masa kwatancen inda hostel din nasu yake, ya jira su har suka fito su uku da Fatiman, Fitowa yyi ya bude back seat yana kallonta yace "Sorry," sai da ta shiga motar snn ya kalli frnds dinta yace "Thanks much, xa mu tafi hospital da ita ynxu" Salima tace "Toh ba sai mun bi ku ba knn" yace "Noo kawai ku koma ciki nasan kila ma karatu ku ke" daga haka yyi masu sallama ya xaga ya bude driver seat ya shiga duk suka bi sa da ido, ya rufe motar ya tada ya dau hanyar gate, ta madubi yake kallonta jefi jefi, sai yaji tausayinta ganin tana jin jiki, yace "Fatima" da kyar ta dago don dama kife kanta tayi, yace "You sit upright, kar ki sake dukawa" mayar da kanta tayi, bai kuma cewa komai ba ya d'an kara speed, suna isa clinic, yyi parking ya fito ya xaga ya bude mata motar ya dagota, hijab din jikinta ya cire ganin rigar dake jikinta ya d'an kamata, ya kai hannu bayanta ya d'an bude zip din ya mayar mata da hijab dinta ya fito da ita daga motar suka shiga asibitin, dai dai sakkowar Dr Shariff daga sama, yana ganinsu ya nufo su yace "Subhanallah" Nurses biyu dake wajen su ma suka yo kansu suna mata sannu, Abuturrab ya mika masu ita yace ku shiga da ita wancan ward din Shariff ya bi bayansu, Pharmacy Abuturrab ya shiga ya karbi alluran da xai mata snn ya fito ya wuce ward din, har Dr Shariff ya cire mata hijab din jikinta ya xaunar da ita ta jingina da bango kan gadon, shi dai Abuturrab kallonsa kawai yake ganin ynda ya wani daga hankali, kawai ya mika masa alluran yace "Gashi kayi mata" Dr Shariff yace "Inhaler dinta fa wai" Abuturrab ya bude hannu alamar bai sani ba, daga haka ya juya ya fita don basa waje yyi mata alluran, ba a dau lkci ba Shariff ya fito yana kallon Abuturrab yace "Let me get her another a office din Dr" daga haka ya wuce sama xuwa office din Ummi, murmushi Abuturrab yyi, bayan yan mintuna sai ga shi ya sakko da sabon inhaler ya shiga ward din, Abuturrab ya bi sa yace "Tunda kayi mata injection kawai ka bar inhaler din, she will be fine soon" Dr shariff yace "Ohh, exactly" murmushi Abuturrab yyi ya juya ya fita, ba a dau lkci ba bacci ya dauke fatima bayan numfashinta ya fara yin dai dai sai a snn Shariff ya fito, shi dai Abuturrab na xaune duk hankalinsa yyi kan Samha, ya mike yana kallon Shariff yace "In tafi kawai xaka mayar da ita gida Dr?" Shariff yace "Am attending to patient ae, sae dai idan xaka tsaya sai in mayar da ita gida,n" Abuturrab yyi dariya yace "Nima matata na can gida na baro ta ba lfya" Shariff yace "Alryt then, ka jira ka mayar da ita kawai" Sai bayan kusan minti talatin fatima ta dawo dai dai, Abuturrab dai na ta xaune duk hankalinsa na kan wife dinsa, karfe sha daya ta fito daga ward din, Abuturrab ya kalleta ya mike yace "How you feeling now" ba tare da ta kallesa ba murya can ciki tace "Fyn" bai kara minti biyar clinic din ba suka wuce gida tare.

Yana gama parking ta bude motar ta fita gabansa ya dinga faduwa kar Samha ta ganta ya shiga uku, sai da yaga tayi nisa ta kusa part dinsu snn ya fito daga motar, sae a snn ya tuna ko godiya bata yi masa ba, ya bi ta da wani irin kallo, dai dai lkcn da ta juyo ta kallesa suka hada ido, murmushi yaga tayi ta yi gaba abun ta, ya d'an yi tsaki ya wuce ciki, ga mamakinsa har lkcn bacci Samha take, ya xauna gefenta ya langwabar da kai yace "Wnn wani irin baby ne xai dinga sa min wife dita bacci haka" ji yyi kmr ya tasheta tunawa da yyi bata karya ba har lkcn, ya dai kyaleta kawai ya mike, ana kiran sllhn zuhr ya tasheta, ya kai ta bathroom ta wanke bakinta ya wanke mata fuska ya fito da ita sai layi take masa, da kansa ya dinga bata tea din da ya hada mata, ta sha me yawa kafin tace ta koshi, xata kwanta yace "Baby baccin ya isa haka plss, mu je in kai ki yawo ki ga gari" kmr xata yi kuka tace "Kawai kwanciya xanyi baxan yi bacci ba" xai yi magana wayarsa ya fara ring yana ganin Ummi ce ta langwabar da kai, can dai ya daga tace "Boy sannu da kkri fa, Allah yyi albarka" yace "Amin Mami" tace "Ka turo min Samha ynxu" ya kalli Samha da ta kwanta ta lumshe ido, yace "Toh Mami" yana katse wayar ya dagota yace "Baxa fa ki kara wani baccin ba" kwace kanta tayi a fusace tace "Did i tell you am sleeping??" sai da ya runtse ido jin tsawan da ta daka masa, can ya bude idon a hankali yace "Ohk am sorry wife, dama Mami ce tace ki je" ta kallesa da sauri tace "In je?" Yace "Yes she just called" a hankali tace "Amma sai anjima koh?

I dnt feel like going out" Yace "Noo, ki je ynxu baby kilan jira take" da kansa ya dauko mata hijab ya mika mata ta karba ta sa, ta mike ya rakata har balcony, a hankali tayi sallama ta bude kofar parlon ta shiga, ji tayi kanta na juya mata kamshin miyan da ake a kitchen, ta karasa ta xauna da kyar tana kallon Ummi ta gaisheta, Ummi dake ta kallonta tace "Bacci kike ne daughter" a hankali tace "Na tashi Ummi" Ummi dai sai kallon kwayar idonta take, can tace "Alryt, ki gaya min ko da abinda kike bukata, i mean anything...
Chapter 83 · 0% Book details