← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 123

Sashe 13

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Juyawa tayi, tayi wucewarta ta bar sa gun a tsaye, ya bi ta da wani mugun kallo, can yyi kwafa ya juya ya koma parlor, wayam yaga parlon ya kalli gun da takalmanta suke ya ga ba su wato ta wuce, da sauri ya fita ya bi bayanta, can ya hango ta xata main road sai tafiya take da sauri da sauri, bata san yana bin ta ba har sai da ya isa dab da ita ya fixgo hannunta, ta juyo a tsorace tana kallonsa, kamar xata yi kuka tace "Doctor church xan wuce am almost late" ya mata wani kallo yace "Toh baxa ki ba, uwar me ake k'ara ki da sh
i a church din?" Shiru tayi tana masa kallo irin ta mamaki, ya ja hannunta ta dinga bin sa har suka iso gida ya kulle kofarsa, breakfast ya nuna mata ya wuce daki, a hankali ta xauna kasa hawaye cike idonta sai kuma ta fara kuka a hankali, sai kusan Karfe goma ya fito shirye cikin kananun kaya as usual, bai ko kalleta ba ya nufi gun breakfast din dake ajiye har lkcn ya xauna ya shiga hada tea, ya debi potatoe da egg kawai ya fara ci, kin dago kanta tayi don har lkcn hawaye take, ya gama cin abinda xai ci ya mike yyi kwanciyarsa kan dogon kujera, ko kukan jini xaki yi baxa ki Church din nn yau ba, ya fadi hakan a xuciyarsa tare da jan tsaki a fili, Har sha biyu da rabi tana wajen a xaune shi ko yyi bacci abun sa hankali kwance, kiran sllh ya sa shi tashi ya mike xaune yana kallon agogo, ga mamakinsa har lkcn tana nan a yanda yake, ya mike bai ko kalleta ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito ya jima bedroom kafin ya fito don tafiya masallaci, bin sa da kallo tayi har ya fita sai kuma ta fashe da kuka. yana fita ya kulle kofar ta waje yayi tafiyarsa, ana idar da sllh main house ya shiga ya tadda Mumy a bedroom da sistern ta Mariya, ya xauna murmushi dauke fuskarsa yace "Mumy yaushe kika xo?" Tace "Tun daxu, nayi xaton baka ma gidan ne, baka je aiki yau ba knn?" Ya shafa kansa yace "Sae da yamma nake tafiya da week end" tace "Toh Allah ya taimaka, kwana biyu ka guje ni Aliyu" yar dariya yayi yace "Mumy aiki ne ya sha min kai wllh...." Hajiya Mariya tace "Toh Allah rufa asiri...." Mikewa yayi yace "Amma sai da dare xaki wuce koh?" Tace "Anything for me?" Dariya yayi yace "in dai da nyt xaki tafi nasan na dawo daga aiki then sai in maida ki gida" tace "Toh shknn xan jira har ka dawo" daga haka yayi masu sallama ya fita, dakin sisters dinsa ya leka ya gansu suna kallo a system, tsaye yyi bakin kofa ya rungume hannayensa yace "Ba islamiyya yau?" Ramlah tace "Sae anjima" kallon ilham da taki kallonsa yake, ganin yanda ta hade rai tana kallon ya karasa dakin ya dagota, kwace kanta take son yi tana tura hannunsa ya dauketa cak suka fita daga dakin, Khaleesat ta kalli Ramlah suka tabe baki a tare, a downstairs ya direta xata gudu ya fixgota yace "Haba my Lil sis baki son abinda nake so kenan?" Kallon mamaki take masa sai kuma tace "Son ta kake yaya?" Da sauri ya girgixa kai yace "Noo ba haka nake nufi ba, I thought you will also buy the idea of being her frnd too, bata da matsala ko kadan, assignment take kawo min in mata, her home is just few houses away from ours, she's nyc....." Tabe baki ilham tayi tace "Ni dai bana son tana xuwa har cikin parlor da bedroom din ka, baka san shaidan is real ba koh?" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, ya danne dariyarsa yace "Na sani mana lil sis....

Amma kinsan ur brother is decent, he can't do anything silly...." Tabe baki tayi tace "Ni dai ina gaya maka" ya ja hancinta yace "Ohk naji my sis, but ki daina daure mata fuska plss kin ji" tace "Na ji" daga haka ya saketa yace "Good of u, kar kuma kice ma su Ramla komai, more especially that stupid Leesat" bai jira cewarta ba ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita.

Yana isa part dinsa ya ganta xaune har time din tana hawaye, da kamar baxae ce komai ba ya nufi bedroom sae kuma ya dawo yana kallonta ya rungume hannu yace "When ake tashi a church din" kallonsa tayi bata ce komai ba tana share hawayen ta, yace "Answer me!" A hankali tace "Karfe daya" kallon agogo yayi yaga dayan ya wuce, ya koma kofa ya bude yana kallonta yace "Ohk tashi ki tafi, a gaida mutan church!!" Mikewa tayi ta dau jakarta da books ta nufi kofar ta fita snn ta juya tana kallonsa, rufe kofarsa yayi, ta juya a sanyaye ta tafi xuwa gate ta bude a hankali ta fita, gida ta nufa don ta san an tashi a church din, tana isa ta shiga kitchen don yunwa ba kadan ba take ji, doya ta fere ta soya da kwai ta hada tea rabin cup ta dawo parlor ta ci, tana gama ci ta kwanta sai bacci.

Hadari ne ya tada ta, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo ganin yanda garin yyi duhu, taga karfe biyar har lkcn tafiyarta catechism ya wuce tana bacci, mikewa tsaye tayi jin iska ta hau sama ta rufe windows gaba daya, garin yyi bakikirin, tsoro ne ya kamata tunawa da tayi ita kadai ce fa yau, parlor ta dawo ta rakube jikin kujera lkci daya ruwa me karfi ya sakko, har shidda ruwa ake kamar da bakin kwarya, tsawan da ake ne ya kara rikitata don ko kadan bata son tsawa, wayarta ta dauka ta fara kiran Mumy ta kira ya kai sau biyar no answer, ta kira Abba shi ma haka, ta fashe da kuka ta kife kanta da kujera, har karfe bakwae tana nan a haka, can tayi karfin halin mikewa xata kunna wutan parlor aka yi wani tsawa ta koma da sauri ta rufe fuskarta, ganin parlon yyi bakikirin sbda duhu yasa ta mike cike da karfin hali ta karasa ta kunna sai taga bbu wutan ma, dawowa tayi ta kunna wayarta ta shiga tunanin ko ta hada kayanta ta wuce gidansu Stella kawae, bata tsaya wani tunanin ba ta wuce sama da sauri ta dauko uniform dinta da duk abinda tasan xata bukata ta xuba su jaka, ta canxa kayan jikinta snn ta dawo parlor ta shiga store don dauko umbrella, tana dauka ta fita nan taga ruwan ba na wasa bane ake yi ga iska, kin komawa parlor tayi, tayi ta tsayuwa a balcony, har takwas na dare, hawaye ne ya shiga sakko mata, can ta rufe kofar kawae ta shiga ruwan a haka da umbrella din, mai gadi ya leko daga windon dakinsa yace "Madam ina xuwa cikin ruwan nan?" Ta kallesa tace "Gidan Anty xan je...." Bata jira me xai ce ba ta fice da sauri, haka ta dinga tafiya duk a tsorace tabi ta kankame leman ganin iska na neman dauketa da shi ga walkiya dake ta haskata, ta d'an yi nisa ta ji haushin karnuka, bata kuma san ta ina ne ba, bata san lkcn da ta wurgar da lema da jakar hannunta ba, ta fasa wani ihu ta fara gudu, tun daga nesa ta hango mota na tahowa hakan bai sa ta fasa gudun da take ba, ganin an dallareta da fitila yasa ta tsaya tana rusa kuka, duk tayi jagab, ana bude motar ta ci gaba da gudunta, bin bayanta yyi da sauri har ya isketa ya fixgota, ta fasa ihu ko ina na jikinta na rawa, daga sama har kasa yake kallonta, ta rufe bakinta da hannunta, lkci daya shi ma yayi jagab, yace "Where are you coming from?" Hanyar gidansu kawai ta iya nuna masa, ya ja ta suka nufi gate ya ciro makulli ya bude yana rike da hannunta suka shiga ya bude kofar parlor ya shigar da ita snn ya bude gate ya fita ya shigo da motarsa yana gama parking ya fito ya rufe gate din ya koma parlor tana nn tsaye inda ya bar ta sai rawan sanyi take, kunna wutan parlon yyi ta sunkuyar da kanta, yace "Baki tafi church din kin tsaya can ba da kika ga hadarin kenan?" Shiru tayi bata dago kanta ba, ya tabe baki ya rufe kofarsa ya wuce bedroom ya dauko towel ya dawo ya mika mata, karba tayi ganin taki motsi yace "Go to the bathroom, take off those clothes nd stop shivering" bata ce komai ba ta nufi bedroom din nasa ta shiga bayi ta cire kayan ta daura towel din, jikin gado ta rakube don wani mugun sanyi take ji.

Fita Abuturrab yayi bayan ya dauko umbrella ya nufi main house, Mami dake bedroom dinta tare da su Ramlah tace "Har ka kai ta?" Yace "Eh Mami..." Mami tace "Toh meye na yawo da jikakkun kaya kuma..." Yace "Yanxu xan tafi in cire" bai jira tace komai ba ya fita ya shiga dakinsu Ramlah, closet dinsu ya bude yana yi yana waige waige ya dauki wani riga me kauri da yayi kama da na bacci ya rufe press din dai dai lkcn da aka bude kofa, da sauri ya boye rigar a bayansa, Khaleesat ta shigo, daga sama har kasa take kallonsa tace "What are you hiding ya Abuu?" Ya hade rai yace "Nothing"
*Haske writers association*
*Noorul Huda*
10....
Chapter 13 · 0% Book details