← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 123

Sashe 17

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lumshe ido yayi ya bude shi ma ya fita, main house ya nufa fuskarsa daure, Ramlah kadai ce xaune parlor tana assignment fuskarsa daure yace "Ina su Rabi'ah?" Sama ta kalla tace "Suna sama" sama ya nufa ya bude dakinsu bbu su, ya bude na Mami ya gansu xaxxaune gefen ta.
_Khaleesat Haiydar_ hope this is enough
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
12___13
Hade rai yayi ya xauna Mami dake kallonsa tace "Ya aka yi Aliyu?" Kin cewa komai yayi Ilham da khaleesat suka yi lamo jikinta, lkci daya duk ya jefa masu wani arnen kallo ya mike kamar wanda aka tsikara ya fice daga dakin kamar xae tashi sama, Mami ta kallesu tace "Kun nemi tsokanarsa koh?" Ilham ta turo baki tace "Ba abinda muka yi masa" har magrib su ilham basu yarda sun bar dakin Mami ba, nan ta tabbatar ba karamin laifi suka yi ma yayan nasu
ba, bbu yanda bata yi da su ba su fadi me suka yi masa suka ki magana, har part dinsa Mami taje bayan Isha ta shiga har bedroom dinsa ganin baya parlor ta gansa xaune gefen gado hannunsa rike da waya, karasawa tayi tana kallon kofar bathroom jin k'aran washing machine, ya ajiye wayar hannunsa yace "Mamina...." Mami tace "dama akwai washing machine a nan?" Yace "Ehh akwai...." Tace "Wanki kake?" Yace "No, just singlets..." Xaunawa tayi tace "Laifin me su ilham suka maka ne wai?" Ya shafa kansa yace "Ya wuce Mami...." Mami ta tabe baki tace "Toh ku kuka sani, naga tun daxu baka shigo ba" yace "Ehh Mami dama yanxu xan shigo" tace "Ohk, toh xan samu a d'an siyo min fruit?" Ya kalleta yace "Toh Mami" mikewa tayi tace "kar ka siyo lemo just apples, grapes and watermelon" yace "Toh Mami, yaushe Abba xai dawo" tace "Baka da numbersa ne?" Murmushi yayi tace "Atoh" daga haka ta nufi kofa ta fita, mikewa yayi ya shiga bathroom ya kashe machine din ya fito da har xai dau makulin mota ya fasa don bbu wani nisa ya dau kudi kawai ya fita, kamar bai son tafiyar yake yi, duk bai da sukuni, yana isa bakin hanya dai dai gun masu saida fruits yayi xaman sa har sai da aka tambayesa mai xai siya, ya kalli mutumin ya gaya masa, wata mota ce tayi parking dai dai gun, ya dinga kallon motar har aka bude, gabansa ya fadi ganinta ta fito, bata ko lura da shi ba ta taho gun mai sayar da fruits din, mikewa yayi yana kallon cikin motar yana son sanin ita da waye, ido hudu yayi da Mum dinta da ta hakikince bayan mota, da ganinta kasan daga church suke, dauke kai yayi ya taka xuwa gun mai fruit din da har ya gama xuba masa nasa a leda yana xuba mata nata, kallonta kawae Abuturrab yake ganin mood dinta kamar mara lafiya yasan kuma tun abun da ya faru daxu ne, lkci daya kamar ance ta juyo ta juyo, kasa daina kallonsa tayi sae shi ne ya dauke ido sanin uwarta baxa ta rasa kallon su ba, ai ko kamar ya sani kallon nasu take kamar idanuwanta xa suyi magana, xagawa yayi ya dau ledan fruits dinsa ya sa hannu aljihu ya ciro kudi hade da wayarsa ya d'an saci kallon uwar ta yaga fa har lkcn kallon direction dinsu take, yi yayi kamar xai mika ma mai fruits kudi, ya tsaya daga bayanta cikin dubara ya kamo hannunta ya saka mata wayarsa a ciki, snn yayi saurin mika ma mai fruits kudinsa ya juya ya bar wajen, ita kanta jikinta ya bata mum dinta na kallon gun duk ta tsorata kada ace taga sanda ya bata waya, tana karban ledan fruits din tayi saurin jefa wayar a ciki ta basa kudinsa sannan ta juyo ta nufi gun mota, tana shiga motar mumy ta jefo mata tambayar da ya tsorata, "Samantha kin san wannan mutumin ne?" Cewar mumy kenan tana kallonta ido a zare, Samantha da Gabanta ya shiga faduwa tace "Wani mutum mumy?" Uwar tace "Wanda ya siya fruits yanxu" Samantha ta girgixa kai da sauri amma bata ce komai ba don bata iya karya ba, cike da masifa uwar tace "Karya kike, I saw the way he was looking at you, ina raba ki da non believers din nan baki ji ko, meye hadin ki da musulmi?" Hawaye cike idonta tace "Kiyi hakuri Mumy...." Wani tsawa tayi mata tace "Sorry for ur self, stupid girl kawai, ina cross din wuyar ki, Kin kara cirewa koh?" Hawaye cike idonta tace "Na mance shi gaban mirror" har suka isa gida masifa Mumy ke mata, Ta kankame ledan fruits din Don tasan kashinta ya bushe idan ta karbi ledan ta ga waya, a dinning ta ajiye ledan tayi saurin ciro wayar ta boye a rigarta ta wuce sama da sauri.

Misalin sha daya tana durkushe gaban gadon ta hade hannayenta biyu idonta lumshe tana addu'a xata kwanta taji vibration din wayar a karkashin pillow da ta ajiye, mikewa tayi da sauri ta isa gun kofa ta sa key snn ta dawo ta dau wayar, number ne bbu suna, a hankali ya daga ta kai kunne, daga daya bangaren taji ance "Hellow frnd!" Murya can kasa tace "ina yini" yace "Lafiya lau, baki yi bacci ba?" Ta gyada kai kamar yana ganinta tace "xan yi yanxu" cikin sanyin murya yace "Ohk, am sorry dear for what happened in the afternoon, plss Kiyi hakuri...." Da sauri tace "Ae ya wuce" yace "No nasan it's still touching you, for my sake kiyi hakuri don Allah" hawaye ya cika idonta a hankali tace "I've already forgiven and forget....

My religion prohibit us from not forgiving, cause we are also being forgiven by the almighty God" ya lumshe ido yace "Ohk my dear, thanks much, ya daren?" Tace "It's nyc..." Yace "Good, gobe xa ki sch koh?" Tace "Ehh" yace "Toh sai da safe...." Da sauri tace "Toh ina xan baka phone dinka?" Yace "No, na baki so that xan dinga jin muryar ki" murmushi tayi tace "Muryata kuma?" Yace "Yeah dear, ur sweet voice..." Xaro ido tayi, tayi dariya tace "Ni ba ruwana, byee" murmushi yayi ya lumshe ido jin dariyarta, cikin sanyin murya yace "Ohk dear, sleep tighttt" a hankali tace "Thank you...." Daga haka ta katse wayar, kwanciya tayi tana kallon wayar kirar Infinix, ganin a bude yake ta shiga gallery, hotunan sisters dinsa ta fara cin karo da, gabanta ya fadi sosai tana kallonsu, A hankali ta dinga wuce su, yawanci duk hotunansu ne, sai na mami tana gani kuma ta gane mum dinsa ce sbda kamar da ta gani, wani hotonsa ta gani yana sanye da white Coat dinsu na likita, wuyarsa sakale da stethoscope fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, sosai hoton yayi kyau, pink lips dinsa ta tsura ma ido, lkci daya incident din ranan ya fado mata gabanta ya fadi sosai, da sauri ta wuce hoton, haka tayi ta kallon hotuna har suka kare, ta lumshe ido daga haka bacci ya dauketa wayar na kwance kirjinta.

Washegari da asuba vibration din wayar ne ya tada ta, mikewa xaune tayi da sauri, ta jawo wayar tana kallo taga number jiya ne, a hankali ta d'aga ta kai kunne, daga daya bangaren taji yace "still sleeping" murya can kasa tace "Na tashi" yace "Noo na tashe ki dai" murmushi tayi yace "Alryt, na dawo mosque shine nace bari in tashe ki duk da nasan bbu abinda xa ki yi....." Tace "Xan yi addu'a mana" yace "Wani addu'a?" Tace "Wanne kai kayi yanxu?" Yace "Sallah naje masallaci nayi mana" tace "Toh nima yanxu xan yi nawa addu'an" ya tabe baki yace "Toh ayi addu'a lfya" tace "Ohk thank you..." Katse wayar yayi ya ajiye yana girgixa kai.

Mikewa tayi ta durkusa jikin gadonta ta hade hannayenta ta lumshe ido, ta kusa minti goma a haka kafin ta mike ta shiga bathroom ta wanke baki ta hada ruwan wanka tayi ta fito, bata 6ata lkci gun shiryawa cikin uniform dinta ba ta fito ta shiga dakin mumy ta ganta xaune kan study table dinta idonta sanye da glass bible a gabanta, karasawa tayi tace "Ina kwana Mumy" Mumy ta rufe Bible din tace "Lafiya lau, kin yi addu'a?" Ta gyada kai tace "Nayi" Mumy tace "Yaushe ne waec din naku?" Tace "Ba na gaya maki ba, it's on Monday" Mumy tace "Good, kina karatu dai koh" tace "Ina yi Mumy" daga haka ta fita, sai kusan takwas da rabi ta bar gida don revision kawai suke a sch, a motar gidansu xa a kai ta sch din, suna isa layin gidansu Abuturrab sai ga shi shi ma ya fito da mota, bai yi gigin hawa kan titi ba ya jira su fara wucewa, gaba daya ya tsura ido ya ga Inda xai ganta cikin motar, dama ita ma tun daga nisa ta hangosa, a hankali ta sauke glass har suka iso dai dai gate din, ta wara ido hade da d'aga masa hannu, kashe mata ido daya yyi, ta xaro ido hade da toshe baki kar tayi dariya, haka ya bi motar da kallo har suka wucesa, ya lumshe ido ya karasa motarsa ya shiga ya dau hanyar gun aiki,
Tun daga ranan basu sake haduwa ba, bai kuma damu ba don ko da yaushe cikin waya suke, ita kuwa kwata kwata ta daina bin hanyar gidansu don ma kada su hadu, ta gwammace taje ta xagaya duk da nisan tafiyar don ita tsoron sisters dinsa take, a haka har suka fara waec.
Chapter 17 · 0% Book details