← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 123

Sashe 46

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

He said nothing, for the past 3yrs aunt dina bata xo gun mu ba..." Abuturrab yyi murmushi yace "Za mu kai mata ziyara knn" da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yeah sweety, amma ba yanxu ba" daga haka ya mike yace "let me Ablute..." Washegari kamar yanda Hajiya tace da wuri Abuturrab ya shirya yana 'yan dube dube a laptop, aka danna bell, Samha dake goge gogen parlon ta mike ta isa gun kofar ta bude, khadija ce tsaye tayi murmushi ganinta khadija tace "Ina kwana Anty Samha" Samha tayi murmushi tace "Lafiya lau khadija" khadija tace "Ki ce ma Uncle Ummi tace tana jiransa fa" Samha tace "To" snn ta juya ta koma parlon tana kallonsa tace "Wae Ummi na jiran ka" mikewa yayi ya rufe laptop din ya langwabar da kai yace "Ko mu je tare ne baby, ke fa kadai zaki xauna gida" murmushi tayi tace "It's nothing ai na saba..." Yace "Alryt da wuri xan dawo kin ji?" Kai ta gyada masa ta rakasa har bakin kofa yayi peck din goshinta, ta juya da sauri ta koma parlon ya wuce yana murmushi, A parking space ya tad
da ta tana jiransa, ya gaisheta ta mika masa car key din ya karba a xuciyarsa yace to da bai iya tukin ba fa, yana gama warming motar ta zaga ta shiga, duk wnn abun fatima na kallonsu ta window a daki, Ummi tace "Samhar fa?" Yace "Tana ciki Mami..." Tace "Duk xata ji bbu dadi ita kadae ga su fatima duk makaranta za su..." Murmushi yyi yace "Ae ta saba Mami" Sae da suka fita compound din tace "Ina matakin karatun ta ya tsaya?" Yace "Waec ta gama recently, but na kai ta tayi jamb registration nn garin" Mami tace "Good..." Daga haka ta dinga nuna masa inda xai bi har suka iso Clinic din, babba ne sosai asibitin, yana gama parking a space din da aka tanada don haka ta fito snn shi ma ya fita, ya bi bayanta xuwa reception, gaisheta nurses din dake gun suka dinga yi ta amsa ta nufi stairs xuwa office dinta, shi dai yana biye da ita har suka iso, Hadadden office ta shiga da shi, ta kunna Ac, ta yaye curtain snn ta xauna ta nuna masa kujera shi ma ya xauna, wayarta ta dauka ta kira wani likita, ba a dau lkci ba wani da baxae wuce Abuturrab ya shigo, ya gaisheta da ladabi ta amsa tace "A new doctor here, xa ayi employing dinsa a nn" Likitan me suna Shareef yace "Alryt, his qualificatios...." Ta girgixa kai tace "Forget that" ya gyada kai, snn ya juya ga Abuturrab ya basa hannu yace "Am Dr Shareef" Abuturrab ya karba hade da murmushi yace "Dr Aliyu" Dr shareef yace "Welcome to our clinic" Ummi tace "Office din kusa da naka xa ka bashi, idan Bashir ya dawo sai ya koma second flour" Dr Shareef yace "Alryt" daga haka ya kalli Abuturrab yace "Mu je Doctor" mikewa Abuturrab yayi yana kallon Ummi, ta dau makullin mota ta basa tace "Ba da dadewa ba xan fita meeting, when it's four sai kayi wucewar ka gida" yace "Toh ke fa Mami" tace "Akwai wani mota a nan xan fita da shi" yace "To nagode Mami" daga haka ya bi bayan Dr shareef suka fita, office din nasa madaidaici ne me dauke da table da office chair, snn da kujeru, sai show glass mai dauke da magunguna da injections a ciki sae gadon Anti Natal, da dai abubuwan da office din likita ke bukata, Dr Shareef yace "Hope you will like it here" Abuturrab yyi murmushi yace "In shaa Allah" Dr Shareef yace "Toh na bar ka lafiya" daga haka ya fita Abuturrab ya xauna kan kujera hade da lumshe ido.

Kafin karfe daya patient din da yyi attending ma sun kusa goma, ana bude kofa ya hade rai, nurse din dai ce ta shigo da wani file kafin ta karaso yace "Ke doctors nawa ne a asibitin nn" kallonsa take bata ce komai ba, ya lura she derives pleasure looking at him, ya wani mugun hade rai yace "r you Daft?" Da sauri tace "Sir?" Kin cewa komai yyi yana kallonta fuskar nn tasa kamar hadari, tace "Amm, amm Doctors shidda ne sir...." Yace "Toh kar ki sake shigo min da file....

Fita" juyawa tayi ta fita, ya ja tsaki shi haushin irin kallon da take masa ma yake kawai.

Kamar yanda Mami tace ana Asr yyi ma Dr shareef sallama, har ya kai bakin kofa ganin kallon da nurses din ke masa gaba daya ya juyo ya dawo, yace "I am Dr Aliyu, am gonna work here with you all for the mean time, yeah am very free nd friendly amma bana son kallo don Allah..." Daga haka ya juya yayi ficewarsa, wasu suka bi sa da harara, wasu kuma kamar idanuwansu xa su rakasu har gun motar. kusan a tare suka shiga compound da fatima a tata motar, yana gama parking a space dinsu ya kashe motar ya fito, ita ma ta fito da kawayenta biyu, ko kallon inda suke bai yi ba ya juya ya nufi part dinsa, duk suka bi sa da ido, Salima tace "Kaddai ku ce min shi ne" Fatima bata ce komai ba ta dau hanyar balcony dinsu, Billy ta sauke ajiyar xuciya tace "Shine mana" daga haka suka bi bayan fatima Salima na ta waigan Abuturrab da har ya isa part dinsa.

Khadija dake parlor da Samha ta mike da sauri ganinsa tace "Sannu da dawowa Uncle" yayi murmushi yace "Yauwa khadija, how you?" Tace "Fine," Daga haka ta nufi kofa yace "Ina xa ki kuma" tace "Dama xan wuce ne" yace "A'a xo kiyi xaman ki" Shiru tayi bata ce komai ba ya kalli Samha yace "Ina yini Ma" murmushi tayi tace "Sannu da dawowa" yace "Thanks dear" daga haka ya shiga Bedroom, khadija ta dawo tayi xamanta parlon tana ci gaba da ba Samha lbrin da take bata.

Kwance Abuturrab yyi Maminsa a ransa, haka kawai ya tashi da ita yau yaji ganinta kawai yake son yi, can ya mike xaune ya dau wayarsa, yyi jim kmr me nazari kafin yayi dialing numberta, yana fara ring gabansa ya shiga faduwa, Mami dake parlor ta rungume hannaye tana sauraren tijaran yakumbo, ba ayi ranan da xae wuce bata xo ta xaxxaga mata tsiyar ta fito da Aliyu ba, a da tana addu'ar Allah ya karkato hankalinsa ya dawo gida ko don xarginta da ake a kan tasan inda yake, amma yanxu kam addu'a ma take kar ya dawo don tasan duk inda yake he is fine don ya saba irin haka, matsalar daya ynxu da yar mutane da ya tafi banda haka ya shekara ma bai dawo ba in dai yana lfya ko a jikinta, dai dai nn wayarta ya shiga ring ta jawo da yake neman hanyar da xata bar parlon take duk da bakuwar number ne hakan bai hanata dauka ba upon maganar da yakumbo take cikin dag'a murya, Abba dai sai operating laptop yake, sallama Mami tayi Aliyu yyi shiru jin muryarta, har sai da ta sake maimaita sallaman, da kyar yyi gathering courage yace "Mami..." Sosai gabanta ya fadi jin muryarsa, ta mike ta kuma yin sallama kamar bata ji sa ba ta nufi stairs, a fusace yakumbo tace "Ahmad dubi ni ta tsallake ta wuce ina mata magana...." Abba ya kalli Mami da har ta kai stairs yace "Hajarah!" Ba tare da ta kallesu ba tace "Ina xuwa, Gwaggo na ce ke kira" daga haka ta wuce sama, Abba ya d'an kalli Yakumbo yace "Tana xuwa yaya..." Tabe baki tayi tace "Ta matse mata can, wato Ahmad ynxu shknn haka xa mu xuba ido an kasa sanin inda Aliyu yake, ni tsorona daya fa kar yaje masallaci a aura masa kafura mu shiga uku..." Sai ta fashe da kuka tace "Wllh Ahmad kaf xuri'ar mu kai ma kasan bbu tubabbe, wnn wace irin kaddara ce haka, mu Aliyu xae xuba ma duwatsu a ido, mu xae kunyata, mu xai toxarta?? toh wllh yyi kadan ko da ya auri yarinyar nn ko bayan raina sai an raba auren, mu xai haifa ma jikokin jaraba?

Matsawar ina numfashi wllh wllh bbu aure tsakaninsa da tsinanniyar, ko ya aureta kuwa sae ya saketa, bare kullum axumi nake ina roko kada Allah ya basa ikon aurenta...."
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
Tohm where r u my Fertymerh Zahrah and Ummi Aysha.... ku ma ga naku shuwagabannin Haske, Allah ya kara mana basira baki daya
38.....

Tun da ta fara Abba ya tsaida abinda yake yana saurarenta, tana kai wa aya kuwa tace "Ko ya ka ga?" Ya gyada kai yace "Haka ne!" Mami na shiga dakinta ta rufe kofar tace "Aliyu!!" Ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Forgive me plss Mami, i know i disappointed you, ki yafe min don Allah..." Tace "Kana ina yanxu?" Shiru yyi, a fusace tace "Baka ji na ne?" Yace "Mami don Allah kiyi hakuri, ina...
Chapter 46 · 0% Book details