Sashe 37
Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daren ranan Abuturrab bai rintsa ba, har asuba yana rungume da ita, gari na fara haske ya kare ma dajin kallo, sai yaga ashe gona ce gun gaba daya, bishiyoyin mangoes da lemo ne yasa gun ya xama kamar daji da daddare, ya kalli wani tabarma dake can nesa da su a shimfide da wani sanda, da alamar dae mutane na xuwa gun, butoci har biyu ya gani bayan wanda ya samu ruwa a ciki jiya, kwance dankwalinta dake daure kafarsa yayi ya shimfida nan kasa snn ya kwantar da ita a hankali ya mike, wani mugun ciwon kai ya dinga ji ya taka a hankali har ya isa inda butan yake ya ga cike yake da ruwa ya dauka ya xaga ya daura alwala snn ya dawo, ya kalli gabas ya tada sllh, bai idar ba samantha ta farka, mikewa xaune tayi da sauri tana kare ma gun kallo, a hankali ta mike ta karasa gun butan da ya ajiye ta dauka, kallonta kawae yake bayan ya idar, ta juyo ya sakar mata murmushi cikin sanyin murya tace "I want to ease my self" yace "In raka ki?" Da sauri ta girgixa masa kai yana murmushi yace "Ohk" ya nuna mata inda xata tafi, ta juya ta wuce, ko da ta dawo bata gansa ba, ta fara kalle kalle da manyan idonta, muryarta na rawa tace "Doctorrr" tim taji fadowar mango a sama, ta koma baya a tsorace tana kallon sama ta gansa samar bishiyar yana tsinkar nunannun mangoes, ya kashe mata ido yace "Breakfast...." Daga haka ya ci gaba da tsinkar mangoes din masu kyau har ya tsinko fiye da ashirin, ji tayi ya diro kasa, ya karasa ya dauko dankwalinta ya dawo ya durkusa ya kwashesu, ta karasa inda yake ta durkusa gabansa a hankali ta shiga taya sa kwashewa, ya sakar mata murmushi yace "Bari toh in kara plucking din pawpaw ae kina so" bata ce komai ba ya mike ya isa inda sanda ke ajiye ya tafi gun bishiyoyin gwandan, can ya koma baya ita dae kallonsa kawae take, taku daya biyu yayi ya buga uban tsalle ya doki ripe pawpaw guda daya da sandar hannunsa ya fado, murmushi tayi ta dauke kanta ya dawo rike da pawpaw din yana murmushi ya ajiye mata, xaunawa yayi yace "Tunda bbu ruwa haka xa mu sha mangoes din..." Daga haka ya dau mango daya ya kai baki, dauka ita ma tayi ta kai baki a hankali, biyu kawae ta sha tace ta koshi, yace "Efizzy xa ki min" murmushi tayi ta girgixa kai kawai, duk yanda yayi da ita tasha kin sha tayi wai ta koshi, pawpaw din ma shi kadae ya sha kayansa wai bata sha, yana gamawa yace "We will leave yanxu...." Mikewa yayi ya dau sauran mangoes din da sanda yana rike da hannunta suka fara tafiya can gaba, da sandar ya dinga clearing masu daji don duk a tsorace take duk da kana ganin hanyar ma kasan ana bi sae dai ba sosai ba, tafiya kawae suke har kusan karfe tara ganin ta gaji sosai ya langwabar da kai yace "Ko in goya ki baby" kamar xata yi kuka tace "Doctor wae ina xa mu...." Yace "In da Allah ya kai mu" bata kuma cewa komai ba suna ta tafiya ga uban rana me xafin gaske har sha daya tayi, ta durkusa tana haki tace "Wayyo doctor i can't go futher am very thirsty" durkusawa shi ma yayi cike da tausayinta, ta fada kansa hawaye cike idonta tace "Na gaji, yunwa nake ji" ya rungume ta yace "Kiyi hakuri plss, so nake mu fita dajin nan ne so i will find you something to eat..." murya suka ji bayansu, ta kankamesa a tsorace ya juya yaga wani tsohon bafullatani sanye da katon hat wanda hakan yasa ba sosai yake yake hango fuskarsa ba, hannunsa rike da sanda cikin hausan sa da bai fitowa irin ta fulani yace ma Abuturrab "yarinya me ya kawo ku nan" Abuturrab da yaji sanyi sosai a ransa yace "Mun yi 6atan hanya ne Baffa!" Bafulatanin yace "Subhanallahi....
Ina ne xa ku?" Abuturrab ya sake samantha ya mike yana kallon dattijon cikin harshen fillanci yace "Daga kano muke xa mu kaduna barayi suka biyo mu tun jiya da daddare shine muka yo dajin nan" tsohon ya washe hakoronsa da goro yayi masa destroying da fillanci yace "Dama ina ganin ka nasan kai namu ne, ashe d'an uwana ne, barka da arxiki da barayin basu cutar da ku ba" Abuturrab murmushi kawae yake yana gyada kai, dattijon ya kalli Samantha da yaren yace "Sannu yarinya ta barka da arxiki" Kanta a kasa tace masa sun gode da harshen fillanci ita ma wanda hakan yayi mugun daure ma Abuturrab kai ya tsaya kallonta kamar idanuwansa xasu fito, dattijon yace "Rigar mu na nan kusa ku taso mu je ku huta, tafiyar minti talatin ne xae kai mu can, na fito kiwo ne dama na hango ku nayi xaton barayin daji ne, ga can inda na boye shanaye na" dariya Abuturrab yayi tsohon ma yayi dariya yace "Toh muje..." Abuturrab ya kalli samantha ya kama hannunta suka bi bayansa, ya matsa hannunta a hankali yace "Dama kina jin fulfulde shine ko sau daya baki taba gaya min ba" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, haka suka dinga bin dattijon da shanayensa kusan ashirin, su sha wancan kwanan su fito ta wani su kuma shan wata kai hanyar dai gashi nan gashi nan, Abuturrab yasan ko kashe sa xa ayi kila baxae iya gane hanyar ba.
Suna isa Rigar dattijon ya juya yana kallonsu da fulfulde yace "Ga 'yar rigar mu nan, da fatan xaku ji dadin xama a ciki na yau dai" murmushi kawai Abuturrab yayi, tafiyar minti goma suka yi suka iso wani gida dake xagaye da kara, Dattijon ya shiga hade da sallama suka bi bayansa, bukkoki hudu ne a xagaye a d'an karamin tsakar gidan, wata mata dake daka tsakar gidan tayi masa sannu da xuwa da yare tana kallonsu Abuturrab, ya amsa yace "Kin ganni da baki 'yan uwanmu koh?" Mikewa tayi ta dauko tabarma ta shimfida tana masu lale, Yace "debo masu nono kafin ki xauna Hansai" wani bukka ta shiga sae ga ta ta fito da kwarya cike da nono ta ajiye masu, Dattijon da ake kira da Alto yace "Ina yarinyar nan ta shiga?" Hansai tace "Taje kai fura gidan tuwaru nasan duk inda take ta kusa gida yanxu" Malam Alto yace "Toh akwae ruwa gidan koh?
Allah ne yayi masu katanga da barayi suka afko daji shine fa muka hadu da su...." Girgixa kai Hansai ta dinga yi tana cewa "Allah yayi mana tsari" Wata yarinya da baxa wuce Samantha ba ta shigo gidan kanta dauke da icce, ta karaso ta durkusa ta sauke tace "Inna bak'i muka yi" Malam Alto yace "Ehh wllh gasu nan daga birni suke" ta kalli Samantha tace "Sannu da xuwa..." Hansai tace "Tashi ki shiga da ita ciki ki bata zani ta daura tayi wanka" Mikewa tayi samantha ta tashi ita ma suka shiga wani bukka, bbu komai ciki sae yar katifa da xani a kai, sae jakar gari yayi xafi guda biyu, cement din dakin duk ya farfashe, Samantha ta xauna kasa yarinyar da hausarta na fulani tace "Ki xauna kan katifa" samantha tayi yanda tace, yarinyar ta bude jaka ta fito da wani xanin kayan fulani a linke ta ajiye mata tace "Gashi ki daura" Samantha ta kalleta a hankali tace "ina son in huta ne" yarinyar tace "Toh ki huta" daga haka ta fita, Hansai tace "Kin bata xanin Binta?" Binta tace "Eh ta kwanta wai tana son ta huta" Hansai tace "Toh shknn, maxa ki xo ki hura wuta in daura sanwa tunda mun yi bak'i" Wani sabulu babba me kamshi Alto ya dauko a dakinsa ya mika ma Abuturrab yace "Aminina Hammadu ne da yaje birni ya kawo mun sabulun nn har uku...
Gashi ka shiga wanka da shi xaka fi jin dadinsa" Abuturrab ya mike yana murmushi ya karba yace "Toh nagode Baffa" daga haka ya nufi 'yar kewayan dake tsakar gidan don Baffa ya kai masa ruwa Binta ta bi sa da kallo, ko da ya fito Baffa ya kai sa Bukkarsa ya dauko masa wani tsaftatattcen rigarsa irin ta fulani ya basa, Abuturrab ya karba hade da godiya Alto ya juya ya fita, yana gama shiryawa ya fada d'an gadon dake bukkar lkci daya bacci ya daukesa.