← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 123

Sashe 44

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da rana mai aiki ne ta kawo masu lunch, Abuturrab ya karba yana kallonta yace "Hajiya na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Ta fita aiki tun safe" yace "Alryt" Da yamma bayan la'asar yana zaune bakin gate tare da mai gadin gidan Hajiya Hajarah ta dawo, gaisheta yayi ta amsa da murmushi tace "Ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mami ya aiki?" Tace "Alhmdllh, ina Samha?" Yace "Tana ciki" tace "Toh a gaisheta" yace "Mami mun gode for the food" tace "Ohh it's nothing Boy" daga haka ta ja motar ta ta shiga gidan.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
35....

Yau kwana goma sha hudu da xuwan su Gombe, yana xaune parlor laptop a gabansa sae dai gaba daya hankalinsa baya kan abinda yake, damuwarsa daya yanda yake cire kudi a account gashi ba shigowa wasu ke yi ba, at all shi bai iya sana'a ba bae ma san yanda ake yi ba, he don't want to run short of money, ya lumshe ido ya rike kai yana tunanin mafita, dago kai yayi bayan kusan minti goma jin fitowar Samha daga kitchen, kallonta yake har ta karaso parlor ta xauna, ya sakar mata murmushi yace "Weldone" jin bata ce komai ba yace "Dear!" Ta kallesa ya ce "An fara Reg din Jamb, gobe sae mu je ki yi koh?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Yeah gobe da safe in shaa Allah" daga haka ya mike ya shiga daki.

Suna breakfast the next day ya sa ta shirya suka fita reg din Jamb din, sae kusan da rana suka dawo gida, bae bari tayi girki ba ya fita ya siyo masu abinci, daren ranan ya dinga tunanin ko dae ya kira small mum dinsa yyi mata maganar CV dinsa ne, yanke shawarar yin hakan yayi daga karshe, washegari lahadi yana xaune balcony ya hango Hajiya Hajarah xaune daga nata Balconyn da laptop gabanta, ganin ta kallo inda yake ya mike ya nufi gun ta, ya d'an dukar da kai yace "Ina kwana Mami?" Tana murmushi tace "Lafiya lau Boy, ya gidan?" Yace "Alhmdllh..." Tace "Ina Samha?" Yace "Tana ciki Mami" tace "Alryt wai in tambaye ka boy..." Kallonta yayi da sauri yace "Ina ji Mami" ta ajiye pen din hannunta ta nuna masa kujerar gabanta tace "To xauna" Ba musu ya xauna tace "Transfer aka yi maka xuwa garin nan?" Ya sunkuyar da kai yace "A'a Mami" tace "Ohk, naga kuma har yanxu baka koma aikin ba ko hutun mai yawa ka dauka, or rather let me put it this way...." Shiru ya d'an yi sai kuma yyi murmushi yace "Mami bana aiki yanzu" da mamaki tace "Baka aiki kuma?" Shiru yayi nan ma, ta sauke ajiyar xuciya tace "It's ohk Boy kar in shiga rayuwar ka koh!" Yar dariya yayi yace "Noo Mami ba haka ba, laifi nayi ma Abbana ya amshe CV dina and everything, that was why i left kano" kallon mamaki take masa, can ta girgixa kai tace "Duk a dalilin auren da kayi knn?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "Toh ba a son yarinyar ne a gidan ku" nan ma ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa, sosai ta ji tausayinsa, can tace "But me yasa ka xabi aurenta da kayi ma iyayenka biyayya" A hankali yace "Mami haka Allah ya so" tace "Toh iyayenta fa?" Yace "Su ba ruwansu" Tace "Satin ku nawa da auren yau?" Yyi shiru kamar mai nazari sai kuma yace "Sati biyu da kwanaki" girgixa kai tayi tana kallonsa tace "Ur field?" Dago kai yayi ya kalleta yayi d'an murmushi yace "Am a Medical Doctor" kallonsa kawai take kafin tace "A doctor?" Yace "Yes Ma'am" ta cire glass din idonta tace "Where did you schl?" Yace "Uk nayi karatu Mami!" Tace "Ina matakin karatun naka?" Yace "Nayi degree, snn nayi masters duk a fannin medicine..." takardar dake gabanta ta dauka da pen ta mika masa tace "Am ur patient suffering from Malaria Typhoid, prescribe me drugs and injections...." Yar dariya yayi ya karbi takardar yace "Alryt Ma'am" ya gama rubuce rubucensa bayan kusan minti shidda sannan ya mika mata takardar ta karba ta sa glass dinta tana kallo, gyada kai ta shiga yi, sai kuma ta mika masa wani takardan tace "Prescribe for someone suffering from chronic stomach ulcer!" Karba yayi ya kuma rubuce rubucensa ya mika mata, ta karba tana dubawa tace "Um!

Yayi kyau, kana theatre ne?" Yace "Ina yi Mami" ta basa wani takardan tace "Rubuta min procedure din yanda xa ayi operating din patient that's suffering from Appendix...." Karba yyi cikin yan mintuna ya gama ya mika mata ta karba tana kallo, murmushi tayi tace "Alryt Doctor, am offering you work at my clinic daga gobe, sai ka shirya da safe mu fita tare..." Ya buda ido yace "Am soo grateful Mamina" tace "My pleasure, but try to reconcile with ur parent kaji boy, kar mace ta hadaka da iyayenka" a hankali yace "In shaa Allah Mami" aikin da take yi a laptop ta juya masa gabansa tace "Idan baxan takura ka ba pls go on with this it's understandable, am already exhausted dama..." Yace "Alryt Mami" daga haka ya fara duba abinda take yi, duk abun nn da suke Fatima na lekensu don tun da taji muryarsa ta taho da sauri ta labe, tana ganin uwarta ta mike ta bar gun da sauri, Hajiyar na kallonsa tace "Xaka iya tafiya da shi boy, idan ka gama sae ka kawo min" yace "Alryt Mami," daga haka ya dau system din da takardun dake ajiye yayi mata sallama ya wuce, ita kuma ta shiga ciki, shara ya tadda samha tana yi a parlor ya girgixa kai ya xauna yace "Kin san me?" Ta kallesa ta ce "Mene?" Yace "Three things you never get tired of are, bathing, cooking and sweeping i notice" dariya ya bata sae dai bata yi ba tayi murmushi ta xauna tace "Toh sae ka tashi kayi" ya wara ido yace "Haba in tashi in yi" ta hararesa tace "Ehh" mikewa yayi ya nufi gun da ta ajiye broom din ta dauke da sauri kafin ya isa, karba yake son yi taki sake masa tace "Nooo, ka kyaleni...."
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
_Hafsat Ummu Ilham, i don't dedicate pages but here is a whole page for you dear sis, Am so grateful for the visit Allah ya bar xumunci sis ya raya su Ilham da Annur, Khaleesat heart you sisto_
36.....

A can kano kuwa har gobe neman Abuturrab Abba yake, har imagining irin hukuncin da xae masa yake, Sosai Mami ta damu ganin har kusan sati bbu labari, to ina Aliyu xae kai yar mutane, kullum Hajiya Mariya sai ta xo gidan yayar tata tana kwantar mata da hankali amma ko kadan bata nuna tasan idan Aliyu yake ba duk da ta lura xargin ta yayarta take, Mahaifiyar Samantha kuwa ba don mai gidanta da ya hanata ba kotu dama tayi niyar kai karan, bata da aiki sae kuka da tsine ma Abuturrab ta kuma dau kudirin ko da ya dawo da Samantha kasheta kawai xata yi kowa ya huta don bata san mugun abinda yaje yyi mata, da dai ace ta xama musulma gwara ta kasheta a cewarta, bbu bata lkci ta shiga shirin tafiya Jerusalem don yin addu'an Allah ya dawo da Samantha tayi masa sacrifice dinta, mahaifin Samantha kam mutum ne mai saukin kai da boye damuwa baxa ka taba cewa abun na damunsa ba.

Ranar Asabar Samha na kitchen tana kkrin daura girki da yamma shi kuma Abuturrab na xaune balcony rike da sabon system din da ya siya don bai iya rayuwa bbu shi, d'aga kai yyi ganin shadow din mutum, ya ga fatima tsaye daga bakin balcony din tace "Mum tace matar ka ta xo" daga haka ta juya ya bi ta da ido, haushin ta ya ji har cikin ransa, ko kadan yarinyar bata yi masa ba, ya ga alamar bata dau hali irin na mahaifiyarta ba sai girman kai, ya tabe baki ya mike ya shiga ciki, kallonsa Samha tayi jin abinda yace, can tace "Toh girkin fa!" Yace "Don't worry ki sa hijab ki tafi" ba musu tayi yanda yace ta fita xuwa part din Hajiya, tana parlor da duk 'yan matan nata uku sai wata dake xaune tare da fatima alamar kawarta ce, Samha ta risina ta gaisheta ta amsa da fara'a tace "Kadaici bai damun ki Samha, ki dinga shigowa nan ku saba da su fatima mana" murmushi Samha tayi tana wasa da fingers dinta tace "Toh" Hajiya tace "yauwa ko ke fa, xama ke dayan nn bbu dadi, ki dinga shigowa cikin mutane" kai samha ta gyada mata, Hajiya tace "Kar fa ki daura girki xa a kai maku idan an gama a nan kin ji" murmushi Samha tayi bata ce komai ba, Mami tace "Gobe su fatima xa su saloon sai ki bi su ki ga gari idan mijin ki ya amince, ke ma sai kiyi gyaran gashin daga can" Samha tace "Uhm to Mami" Fatima ta mike ta dalilin wayarta da yayi kara ta kalli kawarta Bilkisu tace "Gashi sun kira Billy" daga haka suka fita balcony, a waje Billy tace "Teemah new tenant din gidan nan ne yarinyar nn?" Fatima ta kalleta sae ta fasa d'aga wayar tace "Ehh" Billy tace "Kai amma yarinyar is pretty...

Amarya ce koh?" Fatima tayi wani murmushi tace "Sai ma kin ga mijin xa ki san she is nt pretty...." Billy ta wara ido tace "Haba dai??" Fatima tace "Uhn He is more than cute, kin san Allah gabana faduwa yake idan muka hada ido da shi, but sai in wani daure fuska ko gaishesa bana yi" Billy tace "Waoww xan so in gansa kuwa" Fatima xata yi magana sai ga Samha ta fito ta sa takalmanta ganin yanda suke kallonta tace "Sannun ku" Billy tace "Yauwa!" Daga haka tayi wucewarta xuwa part dinsu duk suka bi ta da ido.
Chapter 44 · 0% Book details