Sashe 110
Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Toh Allah ya fika" Bata jira cewarsa ba ta fice parlorn ta dawo kasa, tana kallonsu Hajiya Mariya da har lkcn suka kasa xaune, Noor kuma sai rusa kuka take, a fusace tace "Amma ku dai anyi gayyar yu yu yu, yanxu duk yawan ku a parlorn nn ku ka bar figaggiyar mata ta fice da 'ya ya har biyu?" Hajiya Mariya tace "A'a Col ne yasa ta fita da su, shi ya hanamu aikata komai wllh" a mugun fusace Yakumbo tace "Yo dama sai ku kula wnn da ya baro hankalinsa gaba daya a yak'in biafra?" Hajiya Mariya ta tabe baki tace "To ina mu ina ja da shi yaya?" Yakumbo tayi wani shewa tace "xata san jikokina ta fita da yau, kin dai san gidan koh?" Hajiya Mariya tace "Na sani" Yakumbo tayi kofa da sauri tace "Mu je" Hajiya Mariya ta dau Hijab din ilham ta bi bayanta, tun da suka dau hanya Yakumbo ke bala'i uwa xata tashi sama, col kam ya sha xagi har da na sayarwa, Hajiya Mariya dai sai bin ta take don tana da assurance baxa su fito gidan ba sai tare da yan biyu, suna isa gidansu Noor yakumbo bata saurari mai gadi dake neman sanin wanda suke nema ba ta bangajesa ta shige gate tana cewa "Kaji min mai gadin gidan bala'i" Hajiya Mariya ta bi bayanta, tsaye suka ga Mr David a balcony abun duniya ya ishesa, Yakumbo ta kalli Hajiya Mariya tace "Ita ce wnn" Hajiya Mariya na kkrin danne dariyarta tace "A'a ba ita bace" Yakumbo bata kuma kallonsa ba ta shige parlorn, bbu kowa ciki, Yakumbo ta haura sama Hajiya Mariya na biye da ita, dakuna suka dinga bubbudewa har suka bude wani wanda da alamar na Rachael ne, kwance suka ga yaran duk biyu a kan gado, Rachael na tsaye a press din kayanta xata fiddo xani da xata goya daya, ta rike daya su tafi church, duk a tunaninta David ne ya shigo shi yasa ko kallon inda kofar yake bata yi, Yakumbo ta karasa a hankali ta kinkimi yaro daya tace "Toh Wllh wllh na sake ganin sheggun kafafuwan ki a gidan K'ani na sai na ari bindigarsa na harbe su" A firgice Rachael ta juyo, Hajiya Mariya ta dau daya yaron da sauri, Rachael tace "Jesus Christ me ya kawo ku gidana?" Yakumbo na nuna ta da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Abinda ya kai ki gidanmu daxu" Tuni Hajiya Mariya tayi waje da Sadeeq, Rachael ta bi ta da sauri tana cewa "Ki dawo da yaran nn kar a ji mu a police station, ki dawo ki ajiye min jika na...." Yakumbo ta bi bayanta tana cewa "Aji mu a bariki karewar station, kin yi kadan ki shigo har gida ki kwashe ma mutane yara yar banxa kawai, ke kika yi cikin da aka haifesu xaki kawo mana rainin wayo" ai tuni Hajiya Mariya ta fice parlon gidan, Rachael dake ta vibrate ta juyo tana kallon Yakumbo tace "Amma ai 'ya ta ce ta haifesu ba wani ya haifa mata su ba, i swear to God of Jacob baxa ki fitar da yaron nn gidan nn ba yau sai dai duk abinda xai faru ya faru" Yakumbo tayi shewa tace "Dambe xa mu yi knn, to tsaya" cire mayafin kanta tayi ta goya jaririn da ya fara kuka tsabar wujjigasa da take, ta daure sa tamau a baya snn tace "Toh taho" David ya shigo parlon yana kallonsu, a tsawace Yakumbo ta kuma cewa "Ki taho nace ki karbesa, ban da raini har kya je gidan mutane ki kwaso yara, yo ai yar ki ya kamata ki kwasa ba su ba, su da suke gidan Ubansu" David yace "Kiyi hakuri don Allah" wani kallo ta jefa masa tace "Da xata can baka bata hakuri ba sai ni da na xo daukansu xaka ba hakuri" daga haka tayi hanyar kofa tace "Ashe dai karamar hauka ke kanta, nayi xaton sai mun dambatu xan bar gidan" ko rufe masu kofar bata yi ba ta kara gaba abunta, Rachael ta fashe da kuka tana kallon David yace "Serves you right" daga haka shi ma ya bar mata parlorn, yakumbo ta dinga masifa ita kadai a hanya ga yaro sai tsala kuka yake a bayan ta, ta kai masa duka a baya tace "Kai don mahaifinka rufe min baki kar in ajiye ka a nan inyi wucewata, baka gode Allah naje na amso ku a hannun kafura ba, in dan ta kakan ka ne ai sai dai kayi ta xama a gidan, mata yar banxa kawai ta xo ta kwashe ku, ita Hajarah ta tsaya tana kukan makirci ta kasa kullala komai" Hajiya Mariya na shigowa parlor Hajiya Rahina tace "Alhmdllh, har naji sanyi, amma wnn fitina da me yyi kama" Ummi ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah ya kyauta" Mami kam kasa cewa komai tayi, Hajiya Mariya na bude yaron da ta lullube da xani sbda sanyin waje sai da tayi shock ganin Rosary a wuyarsa, bakinta a leko ta cire ta ajiye a kasa, sai ga Yakumbo ta shigo goye da Abbakar dake tsala kuka, sauke sa tayi tace "Da alama yaran nn yafi son can ne, bnda munafurci muna baro gidan ya dingi tsala min ihu har na iso nn, to tsaye xa mu yi a kansa don abun kunya daya ya ishe mu ba sai an mana k'ari ba" salati ta xabga bayan ta saukesa tace "Mayya, har ta rataya masu sarkan coci a wuya" sai kuma ta fashe da kuka tace "Duk Ahmad ne ya ja maku, bbu dole sai Aliyu ya tattara ya bar gidan tunda tun yanxu ya fara nuna masa bai son 'ya yansa, to ni idan ban so 'ya yan Aliyu ba 'ya 'yan wa xan so, dubi fa yaran kyawawa da su kamar larabawa..." Mami ta mike ta bar parlon, Yakumbo ta cire Rosary din ta jefar tace "Allah ya raya min ku a tafarkin islama, yasa ku xama manyan malaman islama irinsu Isma'il Mufti Menk a can waje da kuma fantami a nan Nigeria" murmushi Ummi tayi tace "Ameen" Yakumbo ta nufi sama tana cewa "Kuma Allah ya raba ku da hali irin na Aliyu, kwakwalwarsa kawai nake son ku dauko" parlon Col ta shiga tace "Toh naje na karbo su Ahmad, gari na wayewa kuma xa su bar maka gidan ka tunda ba son su kke ba, kai da ganinsu kuma kila sai dai girmansu" tana magana ne hawaye cike idonta.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
97.....
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
97.....