← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 123

Sashe 53

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me ya faru?" Sharesa Ummi tayi ta kunna computern gabanta, Samha kam bata dago kanta ba, can Ummi ta kallesa da yaren ita ma tace "You leave now...." Da damuwa yace "But Mum she is crying...." Hade rai Ummi tayi hakan yasa ya juya ya fita kawai, Ummi ta kalleta ganin kukan gaba yake karawa cikin sanyin murya tace "Tashi ki je Samha we'll talk later" kamar jira take ta mike da sauri don da alama bata son xancen ta fita daga dakin Ummi ta bi ta da kallo cike da tausayinta.

Daki ta koma tayi kwanciyarta, tayi kukanta me isarta snn bacci ya dauketa.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
45.....

Sai bayan Khadija ta dawo daga islamiyya Ummi ta wuce clinic don bata son barin Samha ita kadai, karfe uku saura Abuturrab na xaune office yana attending ma patient kiran Ummi ya shigo wayarsa, dauka yyi ya kai kunne hade da yi mata sallama, Ummi ta amsa tace "Kana office boy?" Abuturrab yace "Ehh Mami..." Tace "Toh ina jiran ka" daga haka ta katse wayar, yana sallaman patient din ya mike ya fita xuwa office dinta, sai da tayi masa izinin shigowa bayan ya kwankwaso kofar snn ya shiga da sallama, kallonsa take ganin yanda ya rame sai taji tausayinsa ba kadan ba, ya karaso kansa a kasa ya xauna kujera yace "Gani Mami" ajiyar xuciya ta sauke tana kallonsa har lkcn tace "You will think i'm mean ko boy, ko daya wllh am only trying to put u on d right way ne, kaga yarinyar nn ba muharramar ka bace, it's nt decent it's nt proper ku xauna roof daya da ita...

Kasan da haka kuma, ni ban ga laifin ku ba Aliyu, nasan soyayya gaskiya ce amma tunda har ka buda min cikin ka i can't continue watching u disobey Allah, ina son ka tamkar d'an da na haifa a cikina right frm d time i saw u...

Yanxu kai ka gaya min me xuciyar ka ke raya maka a kan yarinyar nan...

What's d next step u wanted taking kafin abinda ya faru ranan da daddare" bai iya ya dago kansa ba cikin sanyin murya yace "Mami ni bani da niyyar cutar ta aurenta nake son yi...." Ummi tace "Aure?

Ta ya amma" ya langwabar da kai yace "Kin ga idan na aureta conversion dinta xuwa islam baxai dau lkci ba..." Murmushi Ummi tayi tana girgixa kai tace "Na xaunar da ita mun yi magana daxu kasan abinda tace min?" Girgixa kai yayi, Ummi ta ci gaba "She said she don't have interest for islam boy, haka tace min, na kuma yi mamakin jin hakan" Da sauri Abuturrab yace "Noo Mami, she's just confuse ne wllh, buh wanda bai da interest ae baxai dinga sllh ba, kinsan Mami tun da dadewa fa na rabata da duk wani abu da xai dinga kusantarta da Christianity, kuma duk ta hakura ta bari" Ummi tace "That's because she love's you, soyayya yasa ta biye maka boy" yace "No Mami baya ga soyayya ma idan mutum har xuciya yake abun sa ai bbu abinda ya isa raba sa da shi..

Her dad was a muslim then fa, kakanta ma Musulmi ne har ya rasu, kawai mahaifinta bai da rabo ne, amma in shaa Allah shi ma xai dawo hanya madaidaiciya, uwar ta kam dama ba a magana tayi nisa sosai" Ummi dake ta kallonsa ta gyada kai cike da gamsuwa tace "Haka ne boy, na kuma lura abinda yasa ta fara loosing interest sbda nisanta ku da juna da nayi ne, buh i have no other alternative kada in xamo uwar banxa, abinda baxan bar d'a na yayi ba to d'an wani ma baxan bari yayi ba....

Kuma xancen xaka aureta ynxu bai taso ba boy, ka bari sai ta amshi islam don kanta ba don auren ka ba...

Xaka aureta amma not so soon, ynxu dai ka dinga yawan shigowa a kai a kai ta daina jin kadai cin da take ji, komawanta can ne dai baxae taba yiwuwa ba, kai da Yusuf kuyi xaman ku a can tunda xai jima sosai a nan, one more thing boy pls pls ka daure kaje gida ko don mahaifiyar ka..." Kallonta yayi da sauri yace "Sai ince Samha tana ina, baxa ki gane ba Mami ai ina kai kaina gida yanxu ni nasan kano yayi ma Abbana kadan yyi min hukunci sae dai Abuja, xan je gida amma ba yanxu ba" kallonsa kawai Ummi take, can ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn boy, kai ma ka rage ma kanka damuwa bana son kana raman nn, Samha dai ba rabaka nayi da ita ba, duk lkcn da kake son ganinta sai ka shiga har hira ma kuyi, i won't stop that" ya d'an yi shiru sai kuma yace "Toh Mami nagode, amma plss let this continue to be a secret btwn us bana son a san she's nt my wife" da damuwa ya kare maganar, Ummi ta gyada kai tace "Alryt boy" a hankali cikin sanyin murya yace "Mami... mami ko yusuf ma fa kar ki ce masa ba matata bace...." Shiru Ummi tayi tana kallonsa, Gabansa ne ya fadi sosai ganin kallon da take masa, sai kuma tayi saurin gyada kai tana murmushi tace "Aiit, u can leave now boy....

I will let no one know" Mikewa yayi ya mata sallama ya fita, for the 1st time tun bayan faruwan incident din ranan yaji hankalinsa ya kwanta sosai.

Fatima ce xauna balcony da kawayenta biyu handouts a gabansu Khadija da Samha suka fito, Khadija tace "Sister xa mu je siyo airtime..." Fatima tace "Ohk" Bin su da kallo fatima tayi suna yin nisa billy tace "Kin ki gaya min dalilin dawowar yarinyar nn part din ku..." Fatima tace "How many times do i have to tell you nima ban sani ba kuma ban san ta yanda xan sani ba Billy, I've snooped, I've put an eye all to no avail..

Ummi ba gaya min xata yi ba, that silly khadijah of a being ma ko da tasan abu she won't tell me" farida tace "Buh guy din ya fara sake maki kuwa?" Fatima bata ce komai ba ta dau handout din gabanta, Billy tace "i have a plan for you teemah..." Yusuf na xaune karkashin artificial tree dake compound din gidan yana waya amma idonsa da hankalinsa na kan Samha da khadijah dake tahowa, Samha ta saci kallonsa suka hada ido ta dauke nata da sauri, khadija tace "Yaya xa mu je siyo card..." Yace "Card?" Tace "Eh, airtime" yace "Ohk, taho in maki transfer" Tace "Toh yayana thank you..." Daga haka ta kama hannun samha suka nufi inda yake, kujera ta ja ta xauna tana kallon Samha ta dauko mata wani kujerar tace "Sit" Samha ta kirkiri murmushi ta girgixa kai tace "Thank you" Yusuf dake kallonta yace "Why?" Bata ce komai ba kuma bata kallesa ba, yace "Ki xauna" bbu yanda ta iya haka ta xauna kan kujerar, yana danna waya yace "1000 ya maki yawa koh?" Ta xaro ido tace "Noo yaya, ya isa fah" yayi murmushi yace "Tohm!

Waec bai fito ba har ynxu koh" tace "Ehh muna ta jira..." Samha dai kallonsa kawai take, height dinsu xae xo daya da Abuturrab haka ma haskensu, tana kkrin tantance wanda ya fi kyau cikinsu ya dago kai ya ga tana kallonsa, mikewa tayi da sauri tana kallon khadija tace "Amm, xan... bari in shiga ciki in taya usaina..." Daga haka ta bar wajen kmr warce aka kora ya bi ta da ido yana murmushi, Khadija tayi tagumi tana kallonsa, can dai tace "Big bro....

She's someone's else property fah?" Kallonta yayi da sauri yace "Whose?" Ta hade rai tace "Ba na gaya maka ba Dr Aliyun nn mana...." Yusuf yace "Hmm yeah...

Amma yaushe suka xo gidan nan?" Khadija tace "Xa su kusa 5 weeks fa" yace "Ohk, but why is she staying a part dinmu?" Ta bude ido tace "Nima ban sani ba wllh, at 1st nayi tunanin ko bata da lafiya ne ma" yace "Ohk, a ina Aliyun yake aiki?" Khadija tace "A clinic din Ummi..." Kallonta kawai yake can yace "Ohk, da suka xo garin nn baya aiki ne?" Khadija tace "Toh, nima dai bn sani ba amma Ummi dae ta basa aiki a clinic" Yusuf na gyada kai yace "Ohkk, daga wani gari suke?" Tace "Kano wai..." Yace "Ohk, amma bata gaya maki komai a kan ita da Aliyun ba, i mean ko a hira bata gaya maki san da suka yi auren ba...." Khadija da ta fara isa da tambayoyin tace "A'a ni fa ban taba tambayarta komai ba" Yace "Ohk, but is dis their 1st time in Gombe?" Mikewa khadija tayi don tasan in ta ci gaba da basa amsa sae su kai dare a gun, ta turo baki tace "Kai yaya, sai kace ka samu case....

Wnn ko a court sai haka ae ta ya ni xan yi in san ko sun taba xuwa gombe, ni dai tnx for d airtime xan je mu ci gaba da girki..." Daga haka ta kara gaba ya bi ta da kallo yana murmushi.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
46....

Karfe shidda saura Abuturrab ya dawo daga gun aiki, yana gama parking ya fito yana kallon Yusuf dake compound din har lkcn, karasawa yyi ya basa hannu suka gaisa, Yusuf yace "Welcome back..." Abuturrab yace "Thank you, iska kke sha knn" Yusuf ya shafa kai yace "Not really am making a call...." Abuturrab yace "Aiit" daga haka ya wuce part dinsa, har aka kira Magrib Yusuf na xaune waje, sai da ya ga fitan Abuturrab masallaci snn ya tashi ya karasa tap din dake compound din yyi alwala ya bi bayansa.
Chapter 53 · 0% Book details