← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 123

Sashe 55

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yanxu ina muka nufa?" Sai a snn ta kallesa kmr xata yi kuka tace "Da baka san inda xa mu ba muka taho nan?" Yace "Noo mana baby, yanxu dai mu fara xuwa gun aunt da kika ce tana nan garin koh..." Kallonsa tayi da sauri tace "Da gaske?" Yace "Yea mana, a wani anguwa take?" Tace "Familyn mijinta na can mararraba, lkcn can Abbana ke kai ni, amma wani lkcn suna xama Makera" yace "But mun wuce mararraba ai" shiru tayi bata ce komai ba, can yace "Toh mu je makeran ne ynxu?" Kai ta gyada masa, ya tsayar masu da Napep suka wuce Makera, amma cikin rashin sa'a yan gidan suka ce ai sun ma saki gidan sun koma can maraba, bbu yanda suka iya haka suka fito, Abuturrab na kallonta yace "ki xauna dakalin can dear, xan yi sllh in sama maki abinda xa ki ci sai mu tafi can maraban" xama tayi ta jira yyi sllh masallacin dake layin, ya fito ya nemi shago ya siya mata soft drink da snacks shi ya siya Malt, kallon mutumin dake xaune bakin shagon yana ta xukar taba yake, tunani ya shiga yi me ma yasa ya daina shan abun nn, sai yaji kmr ana tempting dinsa ya siya ya juya kawai ya bar wajen da sauri, taxi ya samu drop da xai kai su har maraban, ba su suka isa ba sai kusan biyar da wani abu, tana gaba yana biye da ita a baya yana kare ma garin da baxa a kira da kauye gaba daya ba kallo, Ita ce ta fara shiga d'an gate din gidan da Sallama ganin ya ki shigowa ta juyo tana kallonsa tace "Come in mana" Murmushi yyi ya bi bayanta, tsakar gida ne madaidaici me dauke da dakuna hudu a jere sai bandaki da kewaye a gefe daya, bbu kowa tsakar gidan sai murhu me dauke da tukunyar shinkafa a kai, kallonsa tayi ya wara mata ido a hankali yace "Shiga mana baby" kallon bangaren bayi tayi jin kmr akwai mutum a ciki sai kuma ta karasa bakin kofar daya daga dakunan dake a matsayin parlor ta bude labulen xaune taga Anty Maryam tana yankan alaiyahu sai wata mata dake kwance tana bacci ta juya baya, sake wukan hannunta tayi ta bude baki tana kallonta, can ta kalli matar dake kwance da Samha ma ke kallo ganin kamar Anty Sarah, mikewa Anty maryam tayi da hanxari ta karasa bakin kofar kawai ta kama hannunta suka fito, turus tayi ganin Abuturrab, ae yana ganin reaction dinta ya gane ba lafiya, murya kasa kasa tace "Ku taho...." Bude wani kofa tayi, dai dai lkcn da Samha taji muryar Mahaifiyarta daga cikin bandaki tana kwalo ma Anty Maryam kira wai ta miko mata zani, ai samha bata jira ta gama bude kofar ba ta shige a mugun tsorace, shi kansa Abuturrab ya rikice ba kadan ba, xae fito da ita daga dakin tun kan ta karasa shiga Anty Maryam da ita kanta a gigice take murya can kasa tace "Ku shiga i will close the door now" hakan yasa Abuturrab ya shiga dakin Anty Maryam ta garkame da makulli ta juya da sauri ta koma parlor tana amsa kiranta.

Kuka Samha ta dinga yi tana cewa Abuturrab kashe ta mumy xata yi, bbu irin lallashin da bai yi ba amma kamar yana da da tunxurata duk tayi mugun tsorata gani take kmr Mumy xata fado dakin, shi kansa Abuturrab kansa ya daure ae da kawai Anty Maryam ta bari su fita kawai.

Kin koma parlor Anty Maryam tayi don gani take kmr Rachael mahaifiyar Samantha xata ce xata shiga dakin da ta rufe, ai ko tana fitowa tace "Ki duba min kaya a jaka ki kawo min dakin can..." Daga haka ta nufi dakin da su Samha suke, Anty Maryam da gabanta yayi mugun faduwa tace "Anty dakin a kulle yake ai, baban su Asiya ne...

Ina jin ajiya yyi" Rachael ta juyo tana kallonta sai kuma tace "Ina ce a bude naga dakin daxu kuma ai Aminu bai dawo gidan nn ba" Tabe baki tayi tace "Toh muje nan din, nagansa very untidy ne" Xaune tayi parlon tana shafa mai tace "Ai Maryam tunda pastor din nan na celestial church jiya yace min ina xaune xan ga Rebecca da musulmin nan very soon hankalina ya kwanta, idan kin kula jiya baccin da nayi har da minshari, rabona da bacci haka fa tun daren da Rebecca ta gudu..." Ta girgixa kai tana wani murmushi tace "Yesu ka ga irin tarbiyar da nayi ma yarinyar nn, yesu nasan baxa ka kamani da laifi ba, Toh kayi gaggawan bayyana min ita!" Ita dai Anty Maryam cukuikuye Alaiyahu kawai take duk hankalinta bai gun, Rachael tace "Ya kina ma alaiyahun haka, tunanin me kike" Da sauri Anty Maryam ta xubar a cikin farantin gabanta tace "Babu komai Anty...." Rachael ta gama xura rigarta ta dau Bible ta fita, Anty Maryam ta bi ta da ido xuciyarta na bugawa.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
48.....

Xama tayi tsakar gidan ta bude Bible din hannunta tana dubawa, Anty Maryam ta mike da kyar ta fita tsakar gidan, ta ja kujerar tsugunno ta xauna tana ci gaba da aikin da take, can ta sace kallon Mumy tace "Hayakin nn bai damun ki Anty?" Rachael ta kalleta snn ta kalli Murhun tace "Yo ba gwara ya dame ni ba da xafi ya kasheni a d'an akurkin parlon nn naki Mary....

Ai dai kinga ribar musulunci da auren Musulmi" Anty Maryam ta hade rai tace "Don't start that again aunt, shi da ma Christianityn forcing mutane ake yi su yi?" Tsaki Rachael tayi tace "Mu dama bama bukatar irin ku, ku kare rayuwar ku a musulunci don yesu bai so ku da rahama ba" Tsaki Anty Maryam tayi ta mike ta bar gun ta koma can gaban murhu, Rachael ta tabe baki tace "What a pity" Tunani Maryam ta dinga yi abinda xata ma Mumy taji haushi ta bar gidan ko ma ta wuce church kawai, can dai tace "Ga ku abun tausayi amma ku wani ce kuna tausayin mutum, Astagfirullah... shi Annabi Isan da ku ke bautawa ku ke kiransa da d'an Allah ance maki......" Tsam Mumy ta mike a fusace tana huci tace "Kee Maryam kar ki kai aya, maxa ki tofe yawun bakin ki kan fushin Jehovah ya sakko ya same ki ynzun nn, shi d'an nasa kike xancensa cike da izgilanci??" Maryam ta tabe baki tace "Ni na isa in ma Annabin Allah, ma'aikin Allah izgilanci, ni dai nasan Allahu bai haifa ba ba'a haifesa ba, Annabi Isa kuma messenger dinsa ne haka zalika Annabi Muhammad...." A mugun fusace Mumy ta katse tana hakki tace "Toh kuwa Allah ya tsine maki da wnn furucin, a kan ke musulma ce xa ki dinga fadin wa ennan maganganu, waye kuma Muhammad?" Mikewa Maryam tayi "Annabin Allah ne shi ma, kuma comforter din da Annabi Isa A.S ya gaya maku xai xo, if am nt mistaken bible ne a hannunki, idan kuma baki mance ba nima fa kusan nasan komai a Christianity din nn naku, Anty ki bude john 16:5-8....." Ganin Mumy ba budewa zata yi ba sai kumfar baki take ita a dole an tabo Yesu ta karasa ta karbe bible din ta bude, sai da ta duba tas snn ta rufe bible din tace "Let me make it short, the verse goes thus 'For if i go not away, the comforter will not come unto you, but if i depart, i will send him unto you, and when he comes, he will reprove d world of sin, and approve righteousness nd Judgement..." Murmushi tayi tana kallon Mumy tace "And who is Isa A.S referring to you all as a comforter??

That's prophet Muhammad S.A.W, he is the comforter" Mumy tace "Jehovah ya dawwamar dake cikin duhu, kada ya taba baki ikon gane gaskiya, sha sha sha kawai, talauci kadai ma da ya bar ku da shi ai ya ishe ku" Mai Abuturrab xai yi bnda dariya, sosai Mumy ta basa dariya, ya rike kai ya dinga yi, Samha ta rikesa a tsorace tace "Noo Doctor xa ta ji plss ka dainaaa" hadiye dariyar yayi ya rike baki, Maryam ta tabe baki tace "Ae ba don Allah bai sonmu bane ya bar mu a haka, sai ki ga mu samu in the world here after" Mumy tace "Inaaa ai kwalelanku ku da arziki, baku yrda da d'an sa ba ku ke zaton xai maku arxiki...
Chapter 55 · 0% Book details