Sashe 105
Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Noor Al-Hudah" kallon fuskarta yyi dai dai lkcn da aka bude kofar dakin ya janye jikinsa da sauri, fatima ta shigo rike da Hassan ta karasa kusa da shi ta mika masa, karban yaron yyi, Noor dama kallo daya tayi mata ta dauke kai, fatima ta juya ta fita, kasa kallon Noor yyi ya buge da kallon yaron dake ta mutsu mutsu da baki yana neman abinci, sai ga ta ta kuma dawowa da dayan shi ma ta mika masa ta fita, mikewa Noor tayi ta haye kan gado, ya bi ta da kallon gefen ido, jin yaran xa su fara kuka ya mike ya isa kan gadon ya xauna kusa da ita a hankali yace "Wife they are hungry" jin bata ce komai ba ya bude xip din rigarta, ta mike a d'an fusace, suna hada ido ta kasa cewa komai, ya sauke rigar kasa yana kallon kwayar idonta, a hankali ta shiga breastfeeding yaron da ya daura mata a kafa yana rike da dan uwansa, bayan minti sha biyar Hajiya Mariya ta shigo dakin tana tsaye daga bakin kofa tace "Aliyu idan kun gama ku je can gun Abban ku da yaran ku gaida sa" daga haka ta fita, haka kawai yaji gabansa na faduwa, Hijab din Ramla Noor ta sa, shi ya rike duk yaran biyu, yana gaba tana biye da shi har suka isa part din Abba, yana xaune hannunsa rike da newspaper idonsa sanye da Glass, kallo daya yyi masu ya ci gaba da karatun da yake, Abuturrab ya karasa kansa a kasa ya mika masa yaran, d'an jim yyi kafin ya ajiye takardan hannunsa ya karbesu gaba daya, ita kam Noor k'asan parlorn ta nemi waje ta xauna, ya kalleta ya nuna mata kujera, sunkuyar da kai tayi bata tashi ba yace "Xauna a sama" bata tashi ba still har sai da ya maimaita snn ta mike ta xauna, Abuturrab ya xauna nn kasa kusa da shi cikin sanyin murya yace "Good morning Abba" ba tare da Abba ya kallesa ba bbu yabo bbu fallasa yace "Morning!" Noor ma ta gaishesa kanta a kasa, ya kalleta yace "Morning, ya jiki" tace "Da sauki" kallon babies din hannunsa yyi, lkci daya yyi masu addu'a gaba daya ya mika ma ubansu, Abuturrab ya karbesu gaba daya, Abba ya jawo takardarsa ya ci gaba da karatun da yake, Hajiya Mariya ce ta shigo parlon da sallama, ganin ynda suke xaune shiru, shi kuma yana ta karatunsa ta kalli Noor tace "Tashi ki je Mami na kiran ki kin ji" kallon Abba tayi ta mike a hankali tace "Sai anjima" yace "Alryt" daga haka ta fita, Hajiya Mariya ta d'an tabe baki tace "Col tun asuba baka gama da jaridar nn ba" bai ko kalleta ba, Abuturrab ya mike yace "Sai anjima Abba" Ba tare da ya dago ba still yace "Ohk" Hajiya Mariya ta karbi yaran hannunsa tace "Ka karbi car key gun Mami ka jira ni xa mu fita" yace "to" daga haka ya fita duk jikinsa a sanyaye, Hajiya Mariya ta kuma kyabe baki ta karasa gun Col tace "Toh Abban Abuturrab Atm card xaka bamu mu je siyo ma jikokin ka kaya, bbu komai nasu a gidan nn" tana magana ne tana kallonsa, can ya dago ya kalleta yace "Ni xan bada Atm card?" Tace "Kwarai kuwa Sir, idan baka bayar ba waye xai bada Col" ya girgixa kai yace "Ki je dai ki karbi na uwarsa, bn yi budgeting siyan kayan yara ba wnn watan" dariya ma ya bata, ta ajiye yaran gefensa tace "Suna dai jin ka kar wataran su ce basa yi da kai kaji haushi, kuma kaya ne dai sae granny ya siya masu" daga haka ta nufi gun da ya ajiye makullin mota don ta hango Atm card din ta dauka tayi hanyar kofa ya bi ta da kallo har ta fita, can ya kalli yaran dake ajiye gefensa, ni dai har na bar dakin da takardata da biro bai daina kallon cute angels din gefensa ba.
Bayan kusan awa daya Noor na kwance dakin Mami, sai dai gaba daya hankalinta bai jikinta don bata san inda yaran suke ba, gashi ta kasa tambaya, Ramla dai na ta gyaran press don a xuba kayan babies idan su Hajiya Mariya suka dawo, Mami na taimaka mata, Abba ne yyi sallama bakin kofa, Mami ta amsa sallamar ta karasa kofar da mamaki don ba haka nn yake tahowa bangarenta ba, bude kofar tayi ta gansa tsaye da yan biyu hannunsa yace "A basu abinci" karban yaran tayi tana kallon yanda suka yi da baki wai yunwa, tayi murmushi ya juya ya bar gun, ta shigo ciki ta ajiye su gefen Uwarsu tace "Tashi ki ba basu abinci Daughter" mikewa xaune Noor tayi tana kallonsu har bata san lkcn da tayi murmushi ba.
Karfe sha daya na safiyar ranan Ummi ta iso gidan, ba karamin farin ciki tayi ba ganin twins din, ta rungume Noor da ta kasa kallonta tace "Samha kin bamu wahala da yawa" ita dai Noor bata ce komai ba, kaya ba kadan ba ita ma ta taho ma da twins, ganin bata ga Abuturrab ba tace "Ina Aliyun kuwa?" Mami tace "Sun fita da Mariya" Ummi tace "No more sickness knn koh" Mami tayi murmushi bata ce komai ba, Fatima ta shigo tare da su Ilham ta gaida Umminta suka fita, Ummi bata yi minti sha biyar gidan ba Umma da su Maryam da farida suka shigo, Mami taji dadin ganinsu ta tarbesu da fara'a suka shigo har bedroom ganin Noor, ba kaya na wasa ba suma suka taho ma da yan biyu, Mami tace "Amma ya ku ka gane gidan?" Umma tace "Ahmad ne ya kawo mu yana waje" Mami tace "Gashi Abuturrab din sun fita daxu wllh" bata rufe baki ba sai ga shi sun shigo da Hajiya Mariya, kansa a kasa duk ya gaida su, Ummi dai sai kallonsa take kamar tayi dariya ganin ynda yake sinne kai, a xuciyarta kuwa mamaki take duk irin gata irin tasa ya gwammace yyi ta wahala a kan so, Mami tace "Wai kun hadu da Ahmad?" Yace "Eh tare muka shigo yana parlor, na xo gaishesu ne" Mami tace "Ohk, kace ma su Ilham su kai masa ruwa" juyawa yyi ya fita, Noor dai duk a takure take a dakin, Mami na lura da ita tace "Ki je can dakin ki kwanta kin ji" a hankali tace "Toh" kallon yaran tayi ta mike ta fita, tunani ta dinga yi ynxu fa da xata fita gate bai fi tayi taku kadan ba xata isa gidansu, taga mumynta ta ga Abbanta, hawaye ne ya cika idonta tunanin hakan da tayi, ta shiga dakin Abuturrab a sanyaye ta kwanta.
Karfe daya da kusan rabi Anty Maryam ta iso gidan, uhm duk ta fi kowa murnar ganin 'yar ta, duk ta rasa inda xata sa ta, ko ta kan yan biyu bata bi ba, Hajiya Mariya dai sai kallonsu take da tausayi haka ma Ummi, Noor na jikinta tace "Anty me yasa baki xo da Ihsan ba" Anty Maryam tace "Xa a kawo su daughter" can a hankali Noor tace "Anty baki tambayi babies dina ba" xaro ido Anty Maryam tayi haka ma Ummi, Hajiya Mariya tayi murmushi tana gyada kai, Anty Maryam ta ja hancinta tace "Amma baki da kunya daughter" shiru Noor tayi tana kallonta, can tayi murmushi ta boye fuskarta jikinta.
Sai kusan la'asar Ummi ta bar gidan, ta so su koma da Fatima don next week xa su yi resume Mami tace ta bari sai anyi suna, su Umma dama tun biyu Abuturrab ya maida su gida don Ahmad ya wuce.