← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 123

Sashe 68

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takwas da rabi ya isa maraba, har parlor Anty Maryam ta shigar da shi suka gaisa snn ta dauko kudi ta mika masa tace "Dubu hamsin ne nn, ka bata bride price dinta ta siya duk abinda take so" Kansa a kasa ya karbi kudin yace "In shaa Allah Anty" Kunu da kosai ta kawo masa, bai mata musu ba ya ci, da xai tafi ya ba yaranta dubu biyu ya kuma yi mata godiya snn ya bar gidan, yayi niyyar karasawa kd gun Sadeeq amma ya kira number sa bai shiga ba hakan yasa ya koma Zaria, Samha na kwance idonta lumshe duk da ba bacci take ba, ya karasa ya durkusa gabanta yana kallonta, a hankali ta bude ido, murmushi ya sakar mata yace "Love" mikewa xaune tayi ya kamo hannunta yace "Kin yi break din kuwa?" Kai ta gyada masa ya fiddo kudin aljihunsa ya sa mata a hannu, tace "Na mene?" Ya wara mata ido yace "Ur pride price, Anty tace in kawo maki ki siya duk abinda kike so" shiru tayi tana kallon kudin, can ta girgixa kai tace "Na baka" hade rai yayi yace "Kin ban kuma?

It's urs baby, me kike son in siya maki" ta kallesa tace "Ni ba abinda nake so ai, kawai kayi amfani da shi" Shafa gashin kanta yayi yace "No dear, i will get you something with it" bata kuma cewa komai ba, yyi mata light kiss ya mike yana murmushi yace "Do you still want us to go to gombe?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kuma xaunawa ya kamo hannunta yace "Kinyi shiru Pearl" tace "Duk yanda ka ce" ya dagota suka mike yace "To nace mu je can, it's more safe there" karfe sha daya saura suka bar Zaria suka dau hanyar gombe.

Sai kusan La'asar suka shigo gombe, sai a snn Abuturrab ya fara tunanin da idon da xai kalli Mami, gashi ranan lahadi ce yasan tana ma gida, har suka isa gida tunani kawai yake, mai adai daitan na tsayawa kofar gidan ya kalli Samha, a hankali tace "Toh me xaka ce ma Ummi?" Fitowa yyi ya ba mai adai daitan kudinsa ita ma ta fito, murmushi yyi yana shafa kai yace "I don't know wht to say, ko xaki fadi min abinda xan ce" ta tabe baki tace "Ni ba ruwana" yar dariya yyi ya kama hannunta suka shiga compound din bayan ya amsa gaisuwar mai gadi, kamar ynda yyi tunanin hakan ne don Ummi na xaune balcony tana aiki, Samha ta xame hannunta daga nasa, a hankali yake tafiya har ya isa Balcony din, Ummi kam tun da tayi masa kallo daya dama ta ci gaba da abinda take, durkusawa yyi nan gabanta sai kuma ya rasa abun cewa, kallon Samha dake tsaye gefe tana wasa da yatsunta tayi ta girgixa kai ta mayar da dubanta kan laptop dinta, da kyar Abuturrab yyi gathering courage yace "Mami ina yini?" Kallonsa tayi kafin tace "Lafiya lau" Samha ta d'an risina ta gaisheta ita ma ta amsa snn ta ci gaba da abinda take, ganin ba magana Ummi xata yi ba ya mike, har xai bar gun tace ya dawo, dawowa yayi ta kalli Samha tace "Ki shiga bedroom dina akwai makulli a kan study table ki dauka" shiga parlon Samha tayi, Ummi na kallonsa tace "Sai da kaje ka lalata masu rayuwar ya snn ka dawo knn, i never knew takura ka nake Aliyu amma it's a promise am making now baxan sake shiga rayuwar ku ba" da sauri yace "Wllh ba haka bane Mami, gun kanwar Abbanta na kai ta kaduna, she's a muslim nd....

Mami basu bari muka bar garin ba sai da suka tabbatar na aureta, am saying nothing but d truth, kuma sai da naje kano gun Mum dina, I begged her for forgiveness, i knw i failed u Mami amma don Allah kiyi hakuri kar ki hukunta ni...." Ummi dake ta kallonsa tace "Did i deserve u going without telling me Aliyu, xan hanaka don kace min xa ku gun aunt dinta?

Ni baxan hana ka ba sai dai ko in hada ku da wani ku je tare, haka kke abun ka bbu reasoning Ali?" Sunkuyar da kansa yyi kasa yace "Am so sorry Mami nasan ban kyauta ba ki yafe min" Samha na fitowa daga parlor rike da makullin Ummi tace mata taje ta bude kofa a can, tana barin gun ta girgixa kai tace "Idan ma kun tafi without knowledge dina baka da wayar da xaka kira ni daga baya?" Shiru yyi bai ce komai ba, can ta girgixa kai tace "Gaskiya i was so surprise at you, you failed my trust for you" a hankali yace "Kiyi hakuri Mami..." Tace "Anyway, tashi kaje, Allah rufa asiri, it's good she's now ur wife" bai iya ya mike ba, can ya ciro kudin aljihunsa ya mika mata yace "Aunt dinta tace in bata sadakinta, ko xa ki siya mata abu Mami" ba musu Ummi ta karbi kudin ta ajiye a gefenta, ya mike da kyar ya bar gun.

Har Samha ta fara gyaran gidan kafin ya taho, yayi dusting kujera ya xauna yace "You need rest dear, drop that broom now" ba tare da ta kallesa ba tace "I can't endure resting in dirt..." Kallonta yyi sai kuma yayi murmushi yace "Toh baturiya, transform the house as you wish" kallonsa tayi ita ma tace "You watch nd see..." Kwankwasa kofa aka yi ya mike ya isa kofar ya bude, mai aikin Ummi ce tsaye ta gaishesa ya amsa snn tace "Madam tace in xo in taya ta gyaran gida" hanya ya bata yace "Alryt" bedroom ya wuce ya bar su parlon, yana sllh ya cire bedsheet yyi kwanciyarsa, kafin karfe biyar da rabi suka gyara ko ina na gidan ya rage dakin da yake ciki kawai, Samha tace "Nagode sosai xa ki iya wucewa Anty" daga haka mai aikin ta wuce ita ma ta shiga bedroom din da Abuturrab yake, karasawa tayi kansa ta ja pillon da yake kwance kai tace "You call ur self a doctor amma kuma xaka iya bacci peacefully cikin dusty room din nn?" Har lkcn bai bude ido ba, ta hade rai ta buga gadon tace "Ni ka tashi in gama gyara na, you can go to the other room and continue" bude ido yyi ya fixgota jikinsa yana kallonta yace "Ashe kin iya magana haka Samha?" Kwace kanta ta shiga yi yaki sake ta ya mike xaune yana murmushi yace "One thing about you is that, you can pretend for africa" kwace kanta tayi ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin snn ya mike ya bi bayanta.

Da magrib mai aikin ce ta kawo masu abinci duk da ya riga ya siyo masu, yana xaune shi daya parlor yana danna laptop khadija tayi sallama ta shigo, durkusawa tayi nesa da shi tace "Uncle ashe kun dawo, ya hanya?" Yana murmushi yace "Lafiya lau khadija, ya karatu?" Tace "Alhmdllh, ina sis Samha fa?" Mikewa yayi yace "Let me check her tana ciki" daga haka ya nufi bedroom, yana shiga tana fitowa daga wanka daure da towel, tayi masa kallo daya ta wuce can karshen gado ta xauna, ya bi ta da ido, satan kallonsa tayi ganin kallonta yake ta bata fuska tace "I want to dress up..." Rufe kofar dakin yayi yace "You re free" mikewa tayi xata koma bayin ya rikota, ta wani hade rai tace "Bna so, bana son haka doctor...." Shi ma ya hade giran sama da ta kasa yace "Baki son me?" Fashewa tayi da kuka, ya buda ido yace "Ehenn, me nayi maki" ganin da gaske take ya xauna gefen gado ya xaunar da ita gefensa yace "Khadija fa na jin ki a parlor, daga magana sai ki fara min kuka?" Kallon kofar dakin tayi tana share idonta, lumshe ido yyi ya rungumeta yana shafa gashinta ya kai bakinsa kunnenta yace "Hope anjima dai baxa ki ce min baki so ba don ko kukan jini xa ki yi ba wannan xancen yau..." Shiru tayi bata ce komai ba, ya saketa yana murmushi yace "Ki shirya tana jiran ki a parlor" ta gefen ido ta hararesa ta mike ta nufi press din kayanta, ya gyada kai yana murmushi har lkcn ya fita.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
63.....

Tana gama shirinta ta fita parlorn, xaune ta tadda khadija har lkcn, ta karasa tana murmushi tace "Maimakon ki shigo ciki" khadija dake kallonta ita ma tana murmushin tace "Yanxu Ummi ke ce min kun dawo sister, ya hanya" Samha ta xauna gefenta tace "Alhmdllh, ya makaranta?" Khadija tace "Lafiya lau" fruits dake cikin wani bowl Samha ta mike ta kawo ta ajiye mata tace "Rabi'ah fa?" Khadija tace "Ae har yanxu bata dawo gida ba" Samha tace "Ayya, sis fatima fah?" Khadija tace "Tana cikin gida" Apple kawai khadija ta dauka ta mike tace "Bari in je dare yyi sis Samha sai gobe" Samha ta kalli agogo tace "Da wuri haka" dariya kawai khadija tayi tace "Xan goge hijabs dina kafin in kwanta ne" daga haka ta kalli Abuturrab dake ta danna laptop tace "Uncle sai da safe" ya kalleta yace "So early Dija" murmushi tayi ta nufi kofa yace "Toh ki gayar da Mami, Yusuf na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Yana Egypt" yace "Alryt" har balcony Samha ta rakata suka yi sallama sannan ta dawo parlor ta dau bowl din sauran fruits din ta ajiye a fridge, yace "Ke baxa ki sha ba?" Girgixa kai tayi tace "Na koshi" daga haka ta wuce daki, hijab din jikinta ta cire tayi kwanciyarta ta rufa da blanket.
Chapter 68 · 0% Book details