← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 123

Sashe 111

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiya Mariya ta kwankwasa kofar dakin Abuturrab dake xaune tare da Noor a dakin yyi lallashin har ya gaji ya xauna yana kallonta shi dai yasan sai in Yakumbo bata je gidan ba amma ko da tsiya sai ta dawo tare da yaran, mikewa yyi ya bude kofar yaga Hajiya Mariya tsaye da Sadeeq hannunta ta mika masa shi tace "Bata yaron ta" d'an murmushi yyi ya karbi yaron bai dai tambayeta d'an uwansa ba ya juya ya koma dakin, ajiye ma Noor yyi a jikinta, ta kallesa tace "Dayan fa?" Yace "Yana gun su" cikin rawar murya tace "Kila baya wajen su" Dago kanta yyi yana kallon kwayar idonta, can ya langwabar da kai yace "Baby shknn yanxu duk son da kike min kin kwashe kin mayar kan twins, to ni meye tawa makomar, naga kamar ta babies kadai kike yi ynxu" dauke kanta tayi bata ce komai ba, aka bubbuga kofar dakin ya mike yace "Toh ga shi nn shima an kawo maki" bude kofar yyi yaga yakumbo ce ta shigo dakin rike da Abubakar ta kwantar da shi tace "Aliyu, toh dai a ynxu Ahmad bai da babban makiya kamar wa ennan 'ya yan naka, idan xaka ji ta nawa ka tattara ina ka ina ka, suma ka tattara masu ina su ina su ku bar masa gidan sa, ranan da Allah yasa suka girma sai su tako da kansu su xo su gaishesa, ni ba ma wnn ba, gani nake kamar bak'in cikin rahamar Allah yake masu, to banda haka ta ya xai bar mata me xuwa coci ta shigo masa har gida ta kwashe su ta tafi dasu, kasan matar har ta rataya masu sarkan coci fa a wuya Aliyu" Noor dai sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsunta, shi kam Abuturrab bai iya yace komai ba sai kallonta yake, Yakumbo ta tabe baki tace "Toh dai Allah yyi mana tsari kwashi yaran ka ka bar masa gidansa da wuri wuri, yara maa sha Allah haka" kallon Noor tayi tace "Ke kam kinyi sa'ar uwa, toh ke ma har yanxu kina xuwa cocin kenan koh?" Abuturrab yace "A'a ita musulma ce..." Ta d'an yo waje da ido tace "Tohhh ta musulunta knn, amma dai da xa ka ji ta nawa ka samu yar uwarka musulma warce xata sa ta da 'ya yanta a hanya ka aura kwanan nn..." Sai a snn Noor ta dago manyan idonta tana kallonta, Yakumbo tace "Atoh, ni bayin Allah nake ji ma kar wataran ta mayar da su ruwa, ita ma ai tasan irin musuluntar da suke yi, bari in samu Hajarah in ji ynda xa ayi" daga haka ta fice daga dakin tana cewa "Mu muka ga kaddara, mun kuma gode Allah da ya ba mu ikon daukarta a ynda ta xo mana amma dole ya kara aure don daidaituwar gidansa" Abuturrab ya d'an kirkiri murmushi ya kamo hannun Noor ganin mood dinta cikin sanyin murya yace "You are the 1st nd the last in shaa Allah wife, no amount of talks will make me change my mind" ita dai bata ce komai ba sai hawaye da ya sakko idonta, rungumeta yyi ya lumshe ido yace "Believe me mum twins" Yakumbo na fita ta bude dakin su Ramla, Khaleesat da fatima ne a dakin, Khaleesat ta taso ta rungumeta tace "Umma yaushe kika xo" Yakumbo tace "Tun daxu fa, sai na tarar an dauke yaran da na xo gani shine na tafi karbo su, wacece wancan kuma" Fatima ta ajiye wayar hannunta tace "Ina yini" Yakumbo tace "Lfya lau" Khaleesat tace "Bakuwa ce Umma" Yakumbo tace "Ayyo, sannun ki toh" daga haka ta yi gaba, dakin Mami ta shiga, ta kalli su Ummi dake xaxxaune dakin da Hajiya Mariya tace "Toh dai Hajarah mijin ki ya nuna baro baro bai son xaman Aliyu gidan nn tunda har ya fara barin kafura na kwashe yara, don haka nace Aliyu ya lallaba ya bar gidan ko ko ya kika ga?" Hajiya Mariya tace "Gaskiya ne yaya, kuma tun da har taji ddin shigowa gidan gobe ma sai ta iya xuwa tace xata dauke su" Yakumbo tace "Wayyoo Allah Mariya, ke da kika san komai...." Xaunawa Yakumbo tayi tace "Abu na biyu kuma, Hajarah cewa nayi ya kamata Aliyu ya kara aure kwanan nn, ya auri musulma yar uwarsa warce xata sa ma 'ya yansa ido, Allah na tuba tubabbiya bbu wani tarbiyar arxiki da xata iya ba ma yaran nn biyu abun tausayi" tun da ta fara Hajiya Mariya da su Ummi ke kallonta, ta ci gaba "Shine nace in fara shawara da ke kafin in koma gun Ahmad, ko ya kika ga, ita wnn din ba wai ba ma sonta bane, a'a kawai jikokinmu muke ji ma, gwara ya auro cikakkiyar musulma yar uwarsa ta xo su hadu a ba yaran tarbiya, to ni da nake son su xama manyan malamai ma...." Mami tace "Toh, idan hakan ne mafi alkhairi Allah ya tabbatar...." Mikewa Hajiya Mariya tayi a fusace tace "Amma yaya baki kyauta ba in har kika fadi hakan gaskiya" Yakumbo ta yo waje da ido tace "Bata kyauta ba?

Shi addu'ar da tayi ne bata kyauta ba Mariya?" juyawa Hajiya Mariya tayi ta fice daga dakin, Yakumbo tace "Ji sha sha sha kamar ba da ita muka je muka yi cacan baki aka bamu yara ba, Mariya fa ba cikakken hankali ke gareta ba, ko don bata san xafin haihuwar bane oho, banda haka yaya ana nema ma yaro abun alkhairi ta hayyako mana haka, so take 'ya yan sa su tashi bbu addini ne ko yaya, ai ni Aliyu ya gama cutar mu" Hajiya Rahina tace "Ae kam maganar ki na kan hanya Hajiya, uwa fa ke ba yara tarbiya ba uba ba...." Ummi ta katse ta tace "Amma ita ma ba jahila bace totally a islam kakanta musulmi ne, haka kuma kanwar mahaifinta, baka taba cewa ba musulma bace ita idan ba kun xauna tare bane" Mami tace "Ae ba don a walakantata ba Yakumbo ta fadi haka" Yakumbo tace "Atoh fada masu dai, kin san idan jika ba naka bane" daga haka ta fice daga dakin tana cewa "K'arin Auren Aliyu ba fashi wllh" Hajiya Mariya da ranta ya gama baci ta sauka kitchen ta ci gaba da taya Anty Maryam gyare gyaren da take da yaran frnds din Mami.

Mami tayi murmushi tace "Shknn kinga sai a hada su da fatima Hajiya" Ummi tace "Wace fatiman?" Mami tace "daughter nah mana" Ummi ta girgixa kai tace "Allah ya kiyaye, Aliyu da matarsa sun wuce haka a gu na" Mami tace "Kamar ya Allah ya kiyaye, Hajiya idan kika duba maganan da Yakumbo tayi xa ki ga gaskiya take fadi wllh, ni ba wai bana son matar nn tasa bace kawai dai makomar yaran nake jimami, kinga shi kansa Aliyun ban da yyi sllh kan lkci sai kauce ma sa6o bbu abinda yake na addininsa, Idan ba kwanan nn da naga Aliyu ya fara tsayuwar dare ba shi ba gwanin yin hakan bane, Azkar idan yyi na safe a da can toh bbu xancen na yamma, Karatun qur'aninsa ganin dama ne, to ina gida a nn don Allah, me xata gani a gunsa da har xata yi koyi da shi ita matar?

Amma kinga idan ya aure wata daban sai ta sa su kan hanya gaba daya" Ummi ta tabe baki tace "Toh Allah ya basa wata daban din" Mami tayi murmushi tace "Fatima ce ba wata daban ba" Ummi tace "Ita Fatimar ca aka maki rike take da addini banda sllh da take?" Dariya Hajiya Rahina tayi, Ummi tace "Atoh, barin yaran ynxu da bnda kishin hauka da bala'i bbu abinda suka sa gaba, ke a tunaninki xa ki nemo mai addini ki hada su amma karshensa xamar kishiya xata yi da ita ayi ta kishin hauka mara amfani, am nt in support of this gaskya Mum Aliyu, ita kuma sai aka ce a haka xata yi ta xama baxa ta nemi ilimin sabon addinin nata ba, ina ce a nan su
Hajiyar Shagari qtrs take gaya mana tayi converting a gun su....

Ayi mata adalci, da rashin yan uwanta xata dinga ji ko kuma da kishiyar da ake shirin laka6a mata, bata da kowa da tafi kusanci da a yanxu ban da mu, kar a canxa mata view dinta a kan islam, in her case yi mata kishiya is totally out of the point, snn kun san duk namiji idan ya kara aure irin rawan kan da yake, Aliyu won't be exceptional, ko da kuwa ya nuna baya so to fa wataran xai so ne, For the sake of her conversion a cire maganan kishiya pls, ko da xai yi ya bari sai sun dade tare idan da rai da lafiya ta cika masa gida da 'ya ya...." Hajiya Amina dake ta jin su ta sauke ajiyar xuciya tace "Haka ne Hajiya you have a point, yakumbo tayi hakuri da wnn xancen, ke Mami ki nuna baki amince ba kawai" Mami bata ce komai, Ummi ta mike ta fita daga dakin, Ko da yakumbo ta kai ma Col xancen karin auren Abuturrab shiru yyi yana saurarenta, can ya gyada kai bayan ta kai aya yace "Kina da point a nan yaya"
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
98.....
Chapter 111 · 0% Book details