← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 123

Sashe 19

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daren ranan Abuturrab ya tafi gidan kanwar Maminsa Hajiya Mariya, tayi murnan ganinsa sosai bayan sun gaisa tace "Anya Abuturrab ba wajen wani ko wata ka xo a anguwar nan ba kayi branching din nn" Dariya yayi yace "Mumy wajen ki fa na xo da gaske" tace "Ikon Allah, to ka kyauta ya gida da su ilham?" Yace "Lafiya lau Mumy" tace "Toh yaya fa?" Yace "Ta ma ce a gaishe ki" Tace "ina amsawa, xan ma kira ta" Abinci ta xubo masa duk da yace ya koshi, haka dai ya dauka ya fara ci suna ta hira, jin gidan shiru yace "Bbu kowa Kenan gidan yau Mumy?" Tayi murmushi tace "Kasan an koma boko duk suna gun iyayensu..." Yace "Toh bari kawai in kwaso kayana in dawo taya ki xama tunda ilham ta guje ki" dariya tayi tace "Da ka kyauta mun Aliyu" shi ma yyi dariyar yace "Kar ki damu xan dawo Mumy" Hajiya Mariya bata taba haihuwa ba, sai dai 'ya 'yan mai gidanta kuma duk manya ne, sosai take da son yara, hakan yasa gidanta bai rabo da yara kanana ko da yaushe sai dai in sch period ne, ita ta raini ilham har tayi wayo tayi shekara goma a wajenta, daga baya yakumbo tasa Abba ya karbo ta ba tare da wani dalili ba.

Karfe goma da kusan Rabi Abuturrab yace mata xai tafi, nan ta damu wae sai ya kwana, yace "Toh in har kina son in kwana Mumy sai in kin amince xa ki samo min solution din wata matsala da ta sha min kai" Mumy tace "Ae wnn abu me sauki ne son...." Murmushi yayi yace "to xan kwana...." Sai kusan sha biyu Abuturrab ya fadi ma Small mum din tasa damuwarsa, shiru tayi tana kallonsa, can tayi murmushi tace "Toh kai yanxu matar ce baka samu ba tukun ko ya?" Ya shafa kai bai ce komai ba, can yace "Ehh" tace "Ae ko akwai wata 'yar makwabciyar mu a nan layin yarinyar me kyau da ita, ga hankali ga ilimi ga nutsuwa, in dai Alhaji bai nan ita ke xuwa taya ni kwana, ni dai na yaba da hankalinta, yau ma kanwarsu na asibiti ne shi yasa baka ganta ba amma da tana nan yanxu haka" Tun da ta fara magana ya saki baki yana kallonta har ta kai karshe, tace "Ya na ji kayi shiru" hade rai yayi yana girgixa kai yace "Another solution plss...." Dariya tayi tace "Kai fa ba mutunci ne da kai ba Abuturrab" ya langwabar da kai yace "Ni dai bana son auren hadi Mumy samo wani solution" tace "To ka ce kai baka da wacce kake so fa" ya shafa sajensa a hankali yace "Mumy akwae wata da nake son halayenta, she's nyc, uhm I like her mum" ta gyara xama tace "Ikon Allah to ita a ina take?" Kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "A unguwar mu" Mumy tace "Au abu me sauki, kayi ma Abba magana sai a tura gidansu mana" kamar bae gane abinda take nufi ba ya tsaya kallonta, tace "Kayi shiru kuma" lumshe ido yayi ya bude murya can ciki yace "She's a Christian Mum" xaro ido tayi tace "Christian kuma, ko dai ka ta6u ne Abuturrab, ana maganar arxiki ka sakko wannan..." Kamar xai yi kuka yace "Allah Mumy burgeni take.....

I like her" ta hade rai tace "Kai bana son shashanci fa, me xai hadaka da arniya duk ilimin ka Aliyu" a hankali yace "A'a ba arniya bace Mumy, she have her religion, she's a Christian!" Da wani irin mamaki take kallonsa baki bude, tana girgixa kai tace "Ka fi karfina Aliyu, tashi ka tafi gidanku ka kwana, I don't think you are on ur right senses" saukowa kasa yayi yace "No Mumy, wllh nasan abinda nake, shawara fa na xo ki bani...." Da mamaki tace "Yau naga ikon Allah, wace shawara xan baka a kan kafura ni Mariya?" Shiru yayi yana kallonta, tayi tagumi tace "Yau ni nake ganin ikon Allah, are you okay Aliyu, Christian fa kace?" Sauke idonsa yayi daga kallonta yace "There's nothing wrong with this mum, ko an rufe shiga Islamic religion ne?" Kallonsa kawai take ta kasa cewa komai, murya can kasa yace "I can convert her Mum, baki son in samu wannan ladan..." Da damuwa tace "No son, meye makomar kids din ka, kar ka manta ita xa kayi converting ba family dinta ba, sannan Kasan baxa ta taba rabuwa da family dinta ba, Aliyu keep everything aside and think reality, this is the biggest mistake you are to make in ur life, that aside Kasan in dai yakumbo na da rai abinda baxae taba yiwuwa ba knn, ko Abbanka baxae yarda ba not to talk of ur mum bare a xo ga families wnn abun kunya ne Ali.....

Ita yarinyar ance maka iyayenta xasu yarda su bar ta tayi converting?" Mikewa yayi a d'an fusace yace "Abun kunya don na auri wacce ta dawo addinin musulunci, toh ashe kuwa komai ma xae dawo abun kunya a duniya....

Mum nasan kin fi kowa tunani a parents dina, plss kiyi tunani ki ban shawarar da xae yi boosting din abinda nayi niyya, sannan in dai tana sona bbu ruwana da iyayenta, they can do what ever they wish to me" daga haka ya yi hanyar bedroom ta bi sa da kallo baki bude, kwanciya yayi kan gado ya lumshe ido, can ya bude da sauri ya dau wayarsa ya shiga kiran Samantha har ya gama ringing bata dauka ba ya kuma kira nan ma shiru sai yayi tunanin tayi bacci nan ko tana xaune tana karatun biology kawae ji tayi haushinsa take ji hakan yasa ko kallon wayar bata yi ba.

Washegari Abuturrab na idar da Sallah yace xai tafi, Hajiya Mariya tace "Da wuri haka son, ka jira kayi breakfast mana" yace "Xan yi a gida" shiru tayi tana kallonsa, can tayi murmushi tace "Toh meye kuma na fushi son, ba fa mu gama magana ba" marairaice mata yyi yace "Bayan kin ki supporting dina Mum" tace "No ba haka bane son, am trying to highlight you of the side effect of what you are trying to do, na farko ur kidz, na biyu ur image, na uku your parent, na hudu her parent will and will never agree, na biyar makiyan ka will make jest of you....." Katse ta yayi yace "Mumy naga dai uba shi ke da iko kan 'ya ya ba uwa ba, image dina kuma will never be tarnished tunda ba mugun abu nayi ba, parent dina kuma naga ni xan xauna da abata fa Mumy, parent dinta kuma can do what ever they wish I don't care, snn ni bana hango dariyar da xa a min nafi hango ladan da xan samu gun Allah" lumshe ido tayi cikin sanyin murya tace "Haka ne, Allah ya dafa maka son, yayi xabi mafi alkhairi, ya kawo sassauci kan lamarin" Abuturrab da yaji dadin furucinta yace "Nagode Mum" Sai kusan Karfe goma Abuturrab ya bar gidan bayan ta basa shawarwari masu yawa.

Har bayan kwana biyu bai ga Samantha ba gashi taki daukar kiransa, duk yaji Kamar an daura masa duniyar ne a kansa, da dadewa yasan ta daina bin inda tasan xai ganta, hakan yasa ya maida gun zamansa can gaban gate din main house dinsu, ae ko yana xaune gun ranan laraba ya hangota tana tahowa, bata lura da shi ba hakan yasa yayi saurin dauke kansa, yana ganin ta iso dai dai gate din ya mike sai a sannan ta gansa and she was very shocked, ta juya da sauri xata gudu taku daya biyu ya cafketa, tana xaro ido kamar munafuka tace "Doctor" janta yayi xuwa cikin gidan, sosai ta tsorata tana tirjewa tace "Plss ka bari mana, stop it plss, ur sisters...." bai saurareta ba har sai da suka shiga compound din, sojojin dake xaune suka bi su da kallo kamar idonsa xai yi magana, ko kallonsu Abuturrab bai yi ba, ita ko ta boye fuskarta jikinsa duk ta rikice hawaye na sakko mata, tsoronta daya kada yan gidan su gansu, bai tsaya ba sai da suka shiga parlonsa ya saka key ya jingina jikin kofar yana kallonta, kin yarda ta kallesa tayi ta hade rai tace "Let me out" fixota yayi ya hade ta da bango yace "Why ain't you picking my call?" Kasa cewa komai tayi tana kallonsa can kasar xuciyarta na bugawa ganin yanda ya hade rai, can ta sunkuyar da kai ya kuma dago
Kanta, hawaye ya cika eye balls dinta tace "Ni ka bude min kofa in fita" shiru yyi yana kallonta, can ya sa hannu ya tsinka rosary din wuyarta da cross, xaro ido tayi ta rike tsinkakken rosary din a fusace tace "Meyasa xaka dinga tsinkar min da rosaries....." Yana kallon kwayar idonta yace "Coz I don't see it use on ur neck, it's of no use..." Kallonsa take ta kasa cewa komai, yace "Why are you ignoring my calls?" Rungume hannayenta tayi tace "I see you are good at kissing girls, and my religion prohibit that, because it's almost an act of fornication that's why I decided to quit the frndship....." kallonta yake ko kiftawa bai yi, can ya fixgota yace "Fornication?

Kin san meye fornication?" Tsorata tayi ganin yanda ya rike ta amma ta dake ta tura sa tace "Let me out" k'in saketa yyi yana mata wani kallo yace "Sae kin gaya min the meaning of Fornication" Hararansa tayi tace "You check the dictionary" Dago kanta yayi yana mata wani kallo yace "Have i ever attempted having sex with you?" Kauda kanta tayi ta hade rai bata ce komai ba, yace "Alryt then, but you can't just call me a fornicator without me having sex with you, don haka let me make it happen sai ki ji ddin kirana da haka...."
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
15.....
Chapter 19 · 0% Book details