← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 123

Sashe 107

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka Noor ta dinga samun kulawa yanda ya kamata gidansu Abuturrab, babu abinda aka raga mata ita da yaranta biyu, shi dai Col har lkcn an kasa gane inda ya dosa don haka yake bbu yabo bbu fallasa, ana gobe suna Anty Maryam ta dawo gidan da sassafe, irin shirye shiryen da ake yi gidan sai ka rantse biki xa ayi, bikin ma mai aji, da rana misalin karfe biyu Ahmad ya aiko da raguna biyu, hakan ya ba Abuturrab mamaki har su Mami, nan Mami ta kira Ummarsa tayi mata godiya sosai, a ranan da yamma Abban Noor shi ma ya aika nasa ragunan biyu, Abuturrab na waje tare da old time frnds dinsa da suka xo ganin babies kiran Sadeeq ya shigo wayarsa, ya dauka suka gaisa Sadeeq yace "Ya boys dina?" Abuturrab yace "Sunan nn, growing fast, suna kuma missing rugged dad nasu Sadeeq" Sadeeq yyi dariya yace "Awwwnn, am missing dem more, in'sha Allah gobe xan shigo Nigeria just because of them, xan ma transfer ynxu ka tashi ka shiga kasuwa ka samo masu biggest of rams biyu plss...." Abuturrab yace "Ohh i knw they will be grateful Abbakar, buh an siyo masu raguna da yawa, just get dem something different" Sadeeq yace "Alryt then, till i cum, a shafa min kansu, a kuma gaida min mai jego" Abuturrab yace "Alryt frnd, thanks much" karfe shidda na yamma Ummi ta iso a ranan, Mami ta ji dadin ganinta don abubuwa sun fara shan kansu, aiki yyi yawa sosai, lafiyayyen dinkin atamfar English biyu tayi ma Noor sai jewelries masu kyau, su Mami suka dinga godiya, ta bude jakarta ta fiddo wani box din earrings ta bude ta ciro dankunnen zinari me kyau a ciki ta mika ma Noor tace "Gashi daughter naki ne wnn" ta kalli su Mami dake kallonta da mamaki tayi dariya tace "A'a ba ni na siya mata ba, sadakinta ne dubu hamsin da Aliyu ya ban da dadewa, naga wnn xai fi dacewa shi yasa na siyo mata" Mami tayi murmushi tace "Allah sarki, to mun gode Hajiya, Allahu ya bar xumunci" ita ma tana murmushin tace "Amin" bayan Magrib aka shigo da babban cow gidan da kayan abinci me yawa, Abuturrab ya riga ya san Abbansa ne ya siya kuma hakan ne shi ya siya, sai bayan da ya bari ya tafi part dinsa
snn ya bi sa, xaunawa yyi a kasa yana kallonsa a hankali yace "Abba Allah kara budi, mun gode sosai" Hade rai yyi yace "Godiya na me?" D'an murmushi Abuturrab yyi bai ce komai ba, Abba yace "Leave now before i kick you outttt" mikewa yyi yana murmushi ya fita daga dakin, Abba ya ciro wayarsa ya nemo number yayarsa, a hankali yyi dialing number tana dagawa tace "Ahmad" yayi kasa da kai yace "Na'am yaya kuna lafiya" tace "Toh lafiya lau kenan xa ace, ya gidan, da yara?" Yace "Alhmdllh" tace "Toh Allah yyi albarka, har yau Ali shiru ko Ahmad!" Shiru yyi don ko yaushe xai kirata sai tayi maganan Abuturrab, tace "Kana ji na Ahmad" yace "Ina ji yaya, Aliyu ya dawo" da karfi tace "Ya dawo??" Yace "Ehh" wani kabbara tayi tace "Yaushe?" Col yace "Kwanan nn" tace "Toh madallah, gari na wayewa xan dau hanyar kano idan Allah ya yrda," yace "Ba shi daya ya dawo ba yaya" ta tsuke fuska tace "Shi da wa?" Yace "Shi da yarinyar da yan biyu maza, gobe ne sunan yaran ma" bude baki tayi tace "Har da 'ya ya?

Wato aurenta dai yyi koh Ahmad" yace "Ehh yaya" tace "Toh xa mu gani, ina nan xuwa jibi da sassafe in sha Allah ayi ta ta kare" daga haka ta katse wayar, ya mike ya isa window yana kallon waje ya rungume hannayensa.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
94.....

A daren ranan Abuturrab ya ishi Noor ta fadi sunan da take son a sa ma babies din tace ita bata sani ba, ya langwabar da kai yace "You mean baki da sunan da kike so a ran ki?" Nan ma ta girgixa masa kai, murmushi yyi yace "Toh shknn" gun Maminsa ya tafi yyi shawara da ita sunan da yake son rada ma babies din tace Allah ya raya su amma ya samu Abbansa dai tukun, ko da ya sanar da Abbansa xai yi masa takwara girgixa kai yyi yace "A'a na yafe" Abuturrab yyi shiru yana kallonsa, can Abba yace "Yea sbda mahaifinta hakan baxai yiwu ba, ka rada masu wani sunan daban, there is next time" Daga haka Abba ya mike ya dau wayarsa dake ring ya nufi kofa, Abuturrab bai iya yace komai ba don shi ma da farko yyi wnn tunanin bai mata adalci ba idan yasa nasa mahaifin, an dai san baxai kama ya sa ma d'ansa David ba, Washegari da ya kama friday aka rada ma twins sunansu, Hassan ya ci sunan Ahmad d'an Umma, Hussain kuma aka rada masa Abbakar Sadeeq, ya ci sunan Sadeeq, don wa ennan mutanen ne Abuturrab bai jin xai iya mance su a rayuwa, duk da ba wai Ahmad ya taka wani rawa bane amma tunda har shi ya kuma hada sa da Noor dinsa baxai mance sa ba, wannan suna dai ya samu halartar mutane da dama har da abokan col, har hakan ya dinga ba Hajiya Mariya da Mami mamaki, idan ka ga Noor a wnn rana sai kayi xaton amarya ce tsabar kyau da haduwar da tayi, sosai Mami suka kashe kudi gun ganin sun fito da ita, irin yanda mutane daga nisa da kusa suka cika gidan Col bbu masaka tsinke abun ba a magana, da gani kasan Abuturrab ba karamin d'an gata bane ko daga kan cimar da aka yi domin sunan, ni kam nace to da an gaya maku baban nawa na wasa ne ko don kun gansa a banxa yana wantagalili a gombe da maraba? to dai tillon d'a ne ga Colonel guda, sake baki da idanuwa nayi ganin members na Khaleesat Haiydar Novels su Maman Shakur, Ummu ilham, chamo, Anty Fyn, Ashmaad, Fiddo s dangi, Mimic, Fa'ee, Zuhoorah, Ummu Zainab, Ummu Amana, Humainah, Jamila.... kaiiii ni kam ina xan iya lissafo su... zaxxaune na hangosu kan kujeru ko wannensu ya cakare cikin ankon da suka yi na wani ubansun lace kalan sea green sai head jaa, sai daukar ido suke, ga abinci kala kala an ajiye ma kowa a kan table din gabansa daga gefensu kuma tulin gifts din yan biyu da suka yi wrapping a wrapping paper iri daya ne, Hajiya Mariya da Anty Maryam suka dinga bi suna gaisawa da su, ni ko na rike baki nace "Ohhhh wa yaga gayyar sodi
" don ni dai nasan banda phatiemarkh bbu warce na gayyata wnn sunan, ae fa ban sake bakin da na rike ba na hango wata tawagar guda na 'yan haske writers
su ma suna xaxxaune nace "Toh fahhh" su Ummy Shatu ne, Fatyma Zahrah, sweet sis Asmy B Aliyu, Billy Galadanci, Mom Ihsaan, faxy, Safiyya Huguma, Ayusher, feedohm.... kai gaskiya suna da yawa, su ma sun cakare cikin ankonsu na holland da suka yi ko wannensu sanye da siririn glass na 'yan gayu su ma ga uban gifts dinsu ajiye a gefe, Ummi sai bi take tana gaisawa da su, cannnn cikin jama'ar asali da aka gayyata aka basu pass din shigowa gate din Colonel na hango Iqram Mujaheed tana ta rawan kan kwaso drinks da ruwa tana raba ma mutane uwa an sa ta, ita a dole k'anwar khaleesat Haiydar bakin nn yaki rufuwa, na kyabe baki nace wa yaga karere
, kai na bai gama daurewa ba sai da nasamu lbrin ae fa akwai wani canopy da aka kafa a waje na gayun
Khlst Hydr Nvls su ma sun sha anko cikin shadda fari tas irin na Abuturrab da Sadeeq dake bi yana gaisawa da su, nace cabdi abun na yi ne oo....

Noor kam duk wnn budurin da ake bata da walwala, da ta tuna Anty Maryam da yaranta kadai ne nata a gidan sai hawaye ya cika idonta, ko ba a fadi ma Anty Maryam ba tasan me ke damun yar tata, ita ma duk sai ta ji wani iri.
Chapter 107 · 0% Book details