← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 123

Sashe 123

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Gun da har muka samu shelter for good two days ba wajen rainawa bane madam" ta xaro ido tace "No don't misunderstand me dear, i mean they r nt familiar with place like dat" yace "Yea, experience is the best teacher, let dem go nd learn, beside tun da mum dinsu ta hakura da rice during that time su ma xa su hakura ne ynxu" murmushi kawai tayi bata ce komai ba, ya kashe mata ido yana kwaikwayon muryarta yace "Baxan iya ci ba Dr..." Hararansa tayi ta rufe fuskarta, yyi dariya sosai yace "Eh mana, then na tambaye ki to me xa ki ci wai wani *Rice* ke ga baturiya" bata san lkcn da ta fashe da dariyar ba itama tace "Wayyo bana so dear ka bari plsssss" ya wara mata ido yace "Ae sae ma yaran ki sun girma na basu lbrin" kallon kids din nata dake ta playing game tayi tana murmushi.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
106.....

Har mamakin ynda Abuturrab bai mance hanyar garin Noor ta dinga yi, suna isa Rugar dai dai kofar gidansu Alto Abuturrab yyi parking, ya fito daga motar yana kare ma gidan kallo, Arshaq sai damun Ummun sa yake ina ne nn Abbu ya kawo su tace "We came for visit son" Noor ta fito motar rike da little Noor, twins din suka ki fitowa motar ko wannensu ya tsuke fuska, Noor ce tayi sallama kofar gidan taji muryar Mama Hansai na amsawa daga ciki, a hankali ta sa kafa ta shiga gidan, Hansai dake sauke sanwan rana na dumamen tuwo daga kan wuta ta mike da sauri tana kallonta, murmushi Noor tayi ta isa kusa da ita ta durkusa tace "Sannu mama" Hansai ta saki salati tana tafe hannu tace "Wa xan gani haka, yar nan kuna duniya ashe, Allah mai girma sannun ki da xuwa, sannu da xuwa" da sauri ta shimfida mata tabarma tana yi mata sannu da xuwa cike da farin ciki ta karbi Noorul Huda snn Noor ta xauna tace "Mama bani daya bace yana waje" Hansai tace "Wai yayan ki?

Allah sarki ce mashi ya shigo maxa maxa, Alto ma na kewaye Allah ya rufa asiri bai fita ba, ce ya shigo" Noor tace "Toh mama" ta mike ta fita waje, Abuturrab na tsaye jikin mota ya rungume hannayensa tace "Ku shigo dear" daga haka ta juya ta koma ciki, ya bude bayan motar yana kallon su Ashraf yace "Come down" Arshaq ya girgixa kai da sauri yace "Noo Abbu we will wait for you here plss" hade rai yayi yace "I will knock you both, get down immediately now" fitowa suka yi da sauri yace "It's a promise, here will be ur next place for holiday" duk kallonsa kawai suke basu ce komai ba, ya shiga gidan suka bi bayansa, Hansai ta rasa inda xa ta sa su gaba daya don farin ciki ta ciko masu kwarya da ruwa ta kawo tana ta yi masu sannu da xuwa, Alto ma ya fito bayi ya dinga masu lale marhaba yana washe baki, ya rungumo su Arshaq yana masu fillanci duk suka tsura masa ido, yayi dariya sosai yace "Ga shi dai da ganin ku an ga fulanawa amma bakwa ji" Murmushi Abuturrab yyi a xuciyarsa kuwa yace dole ma ya fara yi masu yaren, Alto yace "Toh Maa sha Allah, Allahu ya raya ku 'yan samari, ashe dai da rabon xa mu sake saduwa Ali, Allah mai girma" Abuturrab yace "Wllh kuwa Baffa, da fatan mun same ku lafiya" Baffa yace "Alhmdllh, Alhmdllh mun gode Allah, duk lfya lau muke wllh" yana son tambayar Binta amma shakkar Noor ya hana yyi hkn, yana ta jiran ita tayi tambayar amma ta ki, Hansai ta dauko kwano tana cewa "Wllh gashi ynxu na sauke dumamem tuwo da miyar kuka sai dai ko k'ashi bbu a miyar sai waran mu ta fulani da na jefa ciki, kuyi hakuri don Allah" Noor tace "Haba Mama ba komai mun ma ci abinci fa kafin mu fito" Hansai tace "A'a ni dae bara in xubo ku ci don Allah" daga haka ta xuba masu tuwon da miya a kai ta ajiye ma Noor da su Arshaq, Abuturrab ma ta xuba masa ta kai masa, murmushi yyi yace "Godiya muke mama" Wata kyakkyawar yarinya ce da baxa ta wuce shekaru 5 ba ta shigo gidan da 'yar karamar tulu a kanta, fara ce sosai gashinta har kusan gadon bayanta, ta ajiye ruwan kanta tace "Inno gashi na debo" Sai a snn Noor tace "Mama Binta fa?" Hansai ta kalleta sai dai bata ce komai ba, Alto dake xaune kusa da Abuturrab yace "Ae Binta Allah ya mata rasuwa shekaru biyar kenan" Noor taji xancen nasa har xuciyarta ta kasa cewa komai sai kallonsa take a sanyaye, Abuturrab ne yyi karfin halin cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ta rasu Baffa, Bata da lafiya ne?" Alto yace "A'a ko daya, wajen haihuwar 'yar can dai ne Allah ya karba abarsa" ya fadi yana nuna yar yarinyar dake tsaye kusa da Hansai dake matsar kwalla, Tuni Noor ta fara hawaye lkci daya jikinta yyi sanyi sosai, shi kam Abuturrab bai iya ya kara cewa komai ba sai dai tuna irin ynda ta dinga hawaye ranan da xa su bar kauyen yasa jikinsa yin sanyi sosai, bai mance alkawarin da yyi mata na cewa xa su dawo su tafi da ita birni ba, murya Hansai ya katse masa tunaninsa cikin sanyin murya take cewa "Binta ta dde bata yi aure ba bayan tafiyar ku, kullum ba dare ba rana jira take ku dawo ku kai ta birni tayi karatu kamar yanda ta ce kayi mata alkawari, da kyar dangin mahaifinta suka yi mata auren nan, ashe ta ajali ce" ta karashe maganar tana kuka sosai, Alto yace "Ka ji ta kuma...." Cikin kuka tace "To ya kake son in ce Alto" yace "Dama can wa'adin da Allah ya debar mata kenan duniya, kiyi ta mata addu'a don shi kadai take bukata gun ki" Hansai bata kuma cewa komai ba sai share hawayen da ta dinga yi, Kallon yar yarinyar dake gefenta Abuturrab yyi, a hankali yace "Allah ya ji kanta, ya rahama mata, ya kyautata na mu" Alto yace "Amin" Noor kam kasa daina kuka tayi ta rasa dalili, da ta tuna ynda ta dinga kulawa da ita taki sake mata fuska tana basar da ita sai taji duk bata kyauta ba, kukan da take yasa su Arshaq suka fara taya ta su ma, Hansai tace "Hakuri xa mu yi 'yar nn, kiyi shiru don Allah ga shi kin sa 'yan yaran nn kuka su ma, tuni na bar ma Allah komai, Binta ita kadai ya bani kuma ya karbe kayansa ba don bai so na ba, kinga ko dole in ta gode masa, ga 'yar ta nn an maida mata sunan, muna kiranta da Fatima ita na kan gani in ji ddi" Abuturrab yace "Haka ne Baaba addu'ar mu kadai take bukata, Allah ya gafarta mata" Duk suka ce Amin, Abuturrab yace "Amma ina neman wata alfarma gun ku Baffa" Alto yace "To ina sauraren ka Ali, ta me kenan?" Yace "So nake ku koma can cikin Birni da xama don Allah, xan samar maku waje, idan ya so ko wace irin sana'a kke son yi sai in taimaka maka Baffa" Murmushi Alto yyi sosai yace "Allah sarki, ban ki ta taka ba Ali, amma gaskiya ni ko kadan ban sha'awar rayuwar birni na fi son xama a ruga" Hansai tace "Haka ne Ali, ni kai na nafi son nn baxan iya xaman birni ba" Abuturrab yace "Toh shknn, Alfarma ta biyu kuma don Allah baffa kada kace a'a, so nake ka ban Fatima in hada in rike da yarana, ina son ta samu ilimi ynda ya kamata" Hansai ta d'an yo waje da ido, Alto kam murmushi yyi yace "Wani hanxari ba gudu ba Ali, kada ka mance ba mu da iko kan yarinyar nn..." Abuturrab ya katse sa yace "Mahaifinta fa?" Alto yace "Yauwa ynxu kayi magana, bayan rasuwar binta da shekara biyu shi ma ya rasu bayan yyi fama da ciwon daji" Hansai ta tabe baki tace "Dangin sa kuwa duk gantalallu ne, tun bayan rasuwar sa bbu wanda ya tako ganin halin da fatima take ciki, basu san cin ta ba basu san shanta ba, mu kadai ne gatan ta" ta karashe maganar tana matsar kwalla, Abuturrab yace "Toh don Allah ku rabu da su Baffa ku ban yarinyar nn na maku alkawarin xan dinga kawota tana maku hutu, xa ku ji dadin ta nan gaba, kar ku manta muhimmancin ilimin muhammadiyya da boko a xamanin nn da muke ciki" Baffa yyi shiru haka Hansai da ta xuba tagumi, Hansai da wasu sabbin hawayen suka xubo idonta tace "Ita daya nake gani in ji dadi ynxu Ali, idan kuka rabani da ita ya xan yi da raina?" Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya yace "Baaba sai ki samu ko d'an 'yan uwa ne ki rike don Allah, ni dai a gaskiya ina son in ma 'yar nn abinda ke ran uwarta har ta bar duniya ku yi hakuri don Allah, sai ma mu iya xuwa da ku ku ga inda muke don lallai duniyar nn ba abun yrda bane tunda ba wai sanin mu ku ka yi sosai ba" Alto yace "A'a ni na yadda da kai Ali, Allah ya shige mana gaba, gata nan ni dai banda abun cewa kuma" ya fadi hakan yana kallon Hansai dake share hawaye tace "Ae shknn, Allah yasa mu dace" Abuturrab yaji dadin hakan yace "Yauwa baaba, in sha Allah xata dinga xuwa maku hutu har ma da yaran gaba daya" Baffa yace "Maa sha Allah, Allah ya taya ku riko" Sai kusan la'asar suka fara shirin barin gidan bayan Abuturrab ya tabbatar su Arshaq sun cinye tuwon tas, amma fa da kyar, Hansae na kwalla ta gama hada ma fatima 'yan tsummokaranta, Dubu talatin Abuturrab ya ba Alto dake ta masa godiya yana sa masa albarka, ita kuma Noor ta ba Hansai dubu goma ta kuma cire layinta dake karamar wayar hannunta ta rubuta masu number Abuturrab a takarda ta mika mata tace "Sai Baffa ya siyo layi a sa a wayar ga Numbersa nan da kun kira xa ku samu" Har bakin mota suka rakosu sai a snn fatima ta fara kuka da Fillanci take tambayar Hansai inda xa a kai ta wanda hakan yasa Hansan kuka sosai, A haka Abuturrab ya ja motar suka bar kofar gidan Noor na daga masu hannu, rarrashin Fatima Noor ta dinga yi da fillanci, Arshaq da kukan ya ishesa yace "Ohh Goodness, Ummu why are we leaving with someone's Child for god's sake?

It will look as if we kidnapped her..." Hararansa Abuturrab ya dinga yi ta madubi hakan yasa yayi shiru bai kara cewa komai ba, kafin su shiga kano har tayi bacci, suna isa gida Abuturrab yyi parking ya fito, Noor ma ta fito da little Noor a hannu, su Arshaq suka fito su ma, Abuturrab ya dau fatima dake ta bacci suka shiga cikin gida.
*Haske writers asso*
07087865788 for Comment nd corrections!!!

You re welcm.

SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Times New Roman
Times New Roman
Calibri
Calibri
!%),.:;>?]}
$([{
e1919b343271447e9ca6b9ca9bc022af
Chapter 123 · 0% Book details