← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 123

Sashe 86

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ni ynxu idan ba Jesus Christ xae sakko ya dakatar da ni ba bbu uban da ya isa hanani abinda ke raina" daga haka ta nufi kofa kamar xata tashi sama tana cewa "Ni naga kamar ma da hadin bakin ka a lamarin nn David, uban waye bai san fulani da shegen mugunta ba dama, ga kuma abinda priest yace har da sa hannun yan uwanka kuma nasan ba kowa bane kilan matsiyaciyar Maryam din nn ce, in kuma na gano itan ce wllh sai na daureta an bi min hakki na" daga haka ta fita ta banko masa kofa, wayarsa ya dauka ya nemo number kanwarsa Maryam ya kira ya kai kunne, yana fara ringing ta daga tace "An tashi lafiya yaya?" Yace "Lafiya Maryam ya gida da yaran?" Tace "Alhmdllh, jiya kuwa nake ta xuci xucin kiran ka Allah bai yi ba, Husnah tace min baka ji dadi ba, ya sis Rachael?" Lumshe ido yyi ya bude yace "Kar ki boye min komai Maryam, duk tambayar da xan maki ki bani amsata tsakanin ki da Allahn da ya halicce ki" Shiru tayi gabanta na faduwa, ya nisa yace "Maryam kinsan inda Samantha take ko baki sani ba?" Xuciyarta ya dinga bugawa da sauri cikin dakiya tace "Ban gane ba yaya, nasan inda take kamar ya?" Ya girgixa kai yana murmushin karfin hali yace "Nace ki fada min gaskiya yar uwa, kar ki ji komai" Hawaye ya cika idonta ita dai tasan har ynxu bata ci karo da mai hakuri da kawaicin yayanta ba, ba lallai ya ji haushinta ba ko da xata fada masa gaskiya amma ai da kunya ace tasan inda yar dan uwan nata uwa daya uba daya take, yar da ita ke nan masa duniya amma tayi shiru taki nunawa, muryarsa ya katse mata tunaninta yace "Ina sauraren ki Maryam" tayo gathering courage tana share idonta tace "Na sani yaya, amma ba don in cuce ka nayi shiru ba, ka yafe min yaya, kasan baxan yrda da duk abinda xai hallaka Samantha ba, just that komai ya faru a duniyar nn tsararre ne daga Allah, it's already written, kayi hakuri yayana" kuka ta fara yi, ya dafe kansa yace "Ya isa haka Maryam,ban ce ki min kuka ba," da kyar ta tsayar da kukan yace "Toh a ina take?" Tana share fuskarta tace "Samantha na gombe yaya...." Ya dago kansa yace "Toh shknn, dama sun kira ni daxu ita da yaron" Anty Maryam ta mike da sauri tace "Sun kira ka yaya?" Yace "Eh" D'an murmushin farin ciki tayi tace "Amma sis Rachael bata sani ba koh?" Yace "Bata sani ba" Ajiyar xuciya ta sauke tace "Toh naji dadi yaya, don Allah kar ka fadi mata" murmushi kawai yyi bai ce komai ba, murya can kasa tace "Sai dai fa yaya Samantha tayi aure, a nan maraban jos aka daura auren" bai iya yace mata komai ba, tasan bai ji ddi bne, ta kwantar da murya tace "Kayi hakuri yaya ka kwantar da hankalin ka, you know God plans best, irin ta mu kaddarar knn, sannan yaya Musulmi ba a abun ki bane a gun ka, don't forget our father was a muslim till death, so are his relatives, Beside ni naga yaron nn na yaba da hankalinsa kuma kasan daga irin gidan da ya fito, bbu wanda ya isa ya tsallake kaddararsa, shi ma nasan bai taba tunanim xae auri warce ba musulma ba, kuma wllh yaya yana sonta fiye da yanda kake tunani ita ma kuma tana son sa...." Shiru tayi jin shi ma yyi shiru, ya gyada kai yace "Shknn we will talk some other time Maryam" Tausayinsa taji sosai, hawaye ya xubo idonta tace "Amma xaka je gun nasu a gombe yaya" Yace "Xan je" tayi murmushi tace "Toh shknn yayana Allah yyi mana mai kyau" yace "Amin" daga haka ya katse wayar, tayi tagumi a xuciyarta tana roka ma yayan nata rahama a gun Allah.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
78.....

Da kyar Abuturrab ya samu ya lallashi Samha ta tsayar da kukan da take, cikin kwantar da murya yace "Beside Abba fa yace xai xo soon baby" a hankali ta dago tana kallonsa tace "Yaushe?" Yana share mata hawayen idonta yace "Soon yace min" daga haka ya rungumeta.

Washegarin ranan da rana kiran Anty Maryam ya shigo wayar Abuturrab, ajiye drip din da yake hadawa xai sa ma Samha yyi, ya daga kiran suka gaisa, tace "Ashe kun yi magana da Abban Samha jiya?" Yace "Ehh Anty Mun kirasa" tace "Toh maa shaa Allah, naji dadi da kuka yi hakan, amma ya ku ka yi da shi?" Yace "He said he will be coming to gombe" Shiru tayi kafin tace "Toh shknn, Allah kai mu, ina babyna?" Kallon Samha dake kwance ta lullube da blanket har kanta yyi, yace "Ga ta Anty, bata da lafiya ne" Anty Maryam tace "Subhanallah, me ya sameta, tun yaushe?" Ya rasa abin cewa, can dai yace "Kwanan nan, bari in bata wayar" Anty Maryam da lkci daya ta gano dalilin ciwon tace "Toh bata wayar" karasawa yyi kusa da ita ya yaye bargon, ta bude idanuwanta a hankali, Ya kai mata wayar kunne yace "Anty xata maki magana wife" Cike da karfin hali Samha ta amsa kiran da Anty Maryam ke yi mata, Anty Maryam tace "Sannu Daughter, ya jikin" a hankali tace "Da sauki" Anty Maryam tace "Tun yaushe ne baki da lafiya?" Bata iya tace komai ba don ita ynxu magana ma burden yake xamar mata, hakan yasa Abuturrab ya mayar da wayar kunnensa, Anty Maryam tace "Ikon Allah, haka take jin jiki?" Yace "Da sauki Anty" Anty Maryam tace "Toh Allah ya sauwake, in shaa Allah ina nn xuwa dubata wnn karan" yace "Toh Anty, Allah ya kai mu" daga haka suka yi sallama ya ajiye wayar ya ci gaba da abinda yake.

Bayan sati biyu ta ishesa ya kira mata Abbanta, bbu musu ya dau wayar ya nemo number ya kira, yana fara ring ya kai mata kunne ta karba, yayi tagumi yana kallonta don ramar tayi yawa, abu kusan wata uku amma ba sauki, "Hello, you call back ltr, he's nt around...." Muryar mum dinta ya d'aki kunnenta, a mugun tsorace ta sake wayar, yayi saurin dauka ya kai kunne shi ma yaji muryar ya katse kawai, ya mike ya ajiye wayar, can ya kalleta ya sakar mata murmushi ganin kuka take son yi, ya koma ya xauna yana shafa gefen fuskarta yace "Xaki fara aikin naki?" Ko tanka sa bata yi ba, yace "Xa mu je asibiti gobe baby...." Washegari da ya kasance Sunday yana xaune parlor kan laptop ita kuma tana daki as usual a kwance tana fama, bbu ynda bai yi da ita ba su tafi asibiti don yana son a mata scan amma taki wai bacci xata yi, fitowarsa knn daga dakin bayan ya tabbatar tayi baccin, danna bell aka yi ya mike ya isa kofar a tunaninsa khadija ce don ita kan xo a lkcn, Fatima ce tsaye bakin kofar, suna hada ido tace "Good afternoon" yace "Afternoon..." Tana jujjuya textbook din hannunta da handouts ba tare da ta kallesa ba tace "Pls idan baxan takura ka ba i need more explanation on this, am having test on it 2marrow in d morning, na samu Ummi tace min she's busy, Colleagues dina sun yi kkrin koya min but i seem nt to get it, and that's as a result of nayi missing lecture din ne shi yasa har ynxu ban gane ba, I've......" Katse ta yyi don surutun ya fara isar sa yace "What course?" Tace "Surg!" Juyawa yyi ya koma parlon ta bi bayansa, ya isa inda yake ya xauna yace "Me yasa baki kira Dr Shariff ba, nasan yana gida nd he will gladly come to assist you, ni gashi xa ki katse min aikin da nake yi" tace "I don't believe he even knows it" tabe baki yyo ya mika mata hannu ta basa litattafen hannunta, ya jawo table ya daura su kai yana dubawa, d'an xaro ido yyi tunawa da Samha da yyi ya kalli hanyar daki, can yace "Ohk, you sit let me make it fast xan fita ne" ta karasa ta xauna gefensa, nan ya fara koya mata course din yanda yasan xata fahimta, sai dai he's making it brief don Allah Allah yake ya kai karshe ta wuce sbda Samha, bai san tun da bell yyi ring ta farka ba, ita dai idonta na kan handout din tana saurarensa, Can yace "Wait!
Chapter 86 · 0% Book details