← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 123

Sashe 34

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai baka jin kunyan karya ne, ina ce jiya birthday ka ja ta ku ka je, ina ce jiya ka bata zobe wae zaka aureta, ka mance hanyar jirgi daban ta mota daban, meye ya hada warce ta fito from a very good Christian home da musulmi, bbu hadin ku don haka ka fito min da 'ya ta idan ba haka ba in kashe ka har lahira!" Wani kallo Abuturrab yyi mata yace "Ni xa ki kashe kuma?" Girgiza kai yayi yana kallon 'yan sandan dake tsatstsaye yace "Ko da maganar nan xae kai mu kotu ku xaku xame min shaida kashe ni tace xata yi." Abba ya kalli sojoji uku dake tsaye gun yace "Ku saka min shi a guard room, ko ba shi ya dauketa ba sai ya fadi inda take, idan kuma yaki ba sae ta kashe sa ba ni xan harbe sa...." Ta gefen ido Abuturrab ya kalle sojojin kawai ya tafi kai kansa Guard room din kafin ma su nufo sa, Cikin tsawa Abba yace "Ku bi sa ku sa shi nace" Daga haka ya nufi yan sandan dake gun, Mumy ta watsa ma Mami wani kallo tana hawaye tace "Amma kin haifa ma kanki jaraba, don wnn d'an naki annoba ne a gari...." Vivian ta ja hannunta suka yi waje tana rusa kuka.

Har bayan azahar Abuturrab na guardroom daga shi sae singlet da dogon wando, bai wani damu ba don sbda shi ma aka yi guard room din a gidan, don haka inda sabo yaci ace ya saba, ko d'an shekara 15 aka saka a gun sae yaji jiki tsabar k'ankantar gun ga uban zafi, ko kwakkwaran motsi bae iya yi, a takure yake waje daya kansa ma baya iya dagawa straight sae a duke, tun bai kai sha biyar ba Abba ke jefasa nn idan yayi laifi kuma sae yafi awa biyar a haka, rabonsa da guard room tun yana 27 yrs wato 3yrs back da ya dauko wani maganan, karfe uku yaji an bude kofa daga waje, ko ba a gaya masa ba yasan Mami ce don ita kadae ke xuwa idan aka kullesa, ae ko ita ce, ta durkusa ta bude karamin kofar da yake ciki da aka sa ma uban kwado, da ganinta kasan ta ci kuka, kamar jira yake tana budesa ya fito duk ya jike jagab da gumi, kasa kallon idonta yayi, ya dafa gwiwansa kansa a sunkuye don gaba daya jikinsa yayi tsami, ga wuyarsa da ya rike, muryarta yaji tace "Aliyu ina 'yar mutane" bai d'ago ba kuma bai ce komai ba, can dai ya dago da kyar jin tayi shiru, tausayinta yaji sosai shi dai yasan tun da kwakwalwarsa ta fara aiki irin na mutane rabon Mami da samun kwanciyar hankali, ko da yaushe cikin dauko magana yake ba babba ba ba karami ba kuma a kanta komai ke karewa don Abba cewa yake ita ta 6ata shi, kwanan nan ne ma abun ya lafa bayan ya fara aiki don ko lkcn yana sch hankalin iyayensa ba a kwance yake ba, kamar xae yi kuka yace "Mami ni fa ban san komai kan maganar nan ba sae xalina ake ci kawai!" Hawaye ya gani idonta ya xube nan kasa yace "Noo Mami don Allah kiyi hakuri...." Dakewa tayi tace "Ina yar mutane take Ali?" Shiru yayi kafin ya dago a hankali ya goge xufar dake fuskarsa yace "Mami...." Sai kuma yayi shiru, sauke idonsa kasa yayi yace "Tana nan!" Mami ta durkusa gabansa ta dago kansa tace "A ina?" Kallonta yayi murya can kasa yace "Mami....

Mami ita nake so and i want to convert her...." Komawa baya Mami tayi da mugun mamaki tana kallonsa kamar idanuwanta xa su fito, cikin rawar murya tace "Aliyuu!" Marairaice mata yayi yace "Mami ni idan ban aureta ba Allah xan iya mutuwa wllh, i will be nothing without her" hawaye ne ya cika idonsa, wanda rabon ta da ganin hakan tun yana d'an shekara goma, ko me xaka yi masa baxa ka taba ganin hawayensa ba sai dai idonsa yayi jajir kirjinsa yayi ta sama da kasa tsabar dacin rai da rashin ji irin nasa, ya daura kansa a jikinta muryarsa na rawa yace "First love support me plss, i love her, ni baxan iya rabuwa da ita ba, kuma Mami idan na musuluntar da ita lada xan samu fah..." Hawaye kawae Mami take duk jikinta yayi sanyi, ita kam tana ganin jarabawa tun da ta haifi Aliyu, ta saita kanta cikin sanyin murya tace "Toh tana ina?" Da kamar baxae ce komai ba sai kuma yace "Tana gidan Mumy!" Da mugun mamaki tace "Mariya?" Yayi shiru bai ce komai ba, ta sauke ajiyar xuciya a hankali, jin tayi shiru ya dago da sauri yace "Mami plss kar fa ki ce ma kowa haka, don Allah kar ki fadi Mami...." A rude ya kare maganar, cikin kwantar da murya tace "Ka gwammace kayi ta shan wahala knn, to ai shknn, shiru xan yi da baki na idan ma ya kashe ka kai ka ja ma kanka, tashi ka shiga ciki kafin a ganmu dama cewa yake ni ke supporting din ka" kallon d'an kurkukun yayi kafin ya marairaice yace "Mami k'ishi nake ji sosai wllh" mikewa tayi tace tana xuwa snn ta fita, ya fi kowa sanin halin Mami yasan wannan duk pretending take masa, ya kalli bunch of keys din da ta ajiye nan kasa bayan ta bude sa, ya dauka da sauri ya cire biyu ya tona kasa ya boye a cikin d'an room din, yana nan durkushe yana yi yana lekan sojoji biyun dake tsaye waje har ta dawo ya sunkuyar da kansa da sauri, Ruwan babban gora me sanyi ta kawo masa da Hollandia yoghurt, sae dambun nama cike a plate tace toh tashi ka shiga kafin ya yo nan, karban ruwan yayi ya sha kusan rabi, Key din dake ajiye kawae take kallo can ta dauka tana weighing dinsa ta kallesa strictly tace "Ka cire key a nan bani!" Da sauri yace "Key kuma Mami" wani kallo tayi masa tace "mike tsaye" yana tashi ta sa hannu aljihunsa ta dudduba taga babu, ta leka guard room din ma bata ga alamar key ba tace "Toh shiga ciki" ya ajiye ruwan hannunsa fuskar nan tasa kamar xae yi kuka ya durkusa ya shiga ta tura masa abubuwan da ta kawo snn ta rufe gun da kwado ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo yana murmushi har ta fita.

Ko minti goma ba ayi da fitarta ba yasa key ya bude gun a hankali ya fito, ya dau shirt dinsa dake rataye gun ya kakkabe ya saka snn ya saka takalmansa ya nufi kofa da sauri, lkci daya ya banke kofar ya fice a dari da sittin kafin sojojin su ankara, ae ko suka bi sa da gudu, gudu yake kamar jirgi xae tashi sama, wani soldier ya ciro whistle a aljihunsa ya dinga hurawa, ae ko sae ga sojoji har uku sun fito, Abba ma ya fito balconynsa a sama ya rungume hannu da mugun mamaki yana kallon Abuturrab, komawa yayi don dauko bindigarsa amma kafin ya dawo tuni ya isa gate da karfi ya finciko mai gadin sojan dake bakin gate yana kkrin datse gate din ya wani wurgar da shi ya fixgo gate din ya fice, gudu kawai yake kamar xae tashi sama, wanda hakan ya tsorata mutane duk suka fara gudu su ma, ko kallonsu bai yi ba har ya iso titi ya tsayar da mai adai daita bai jira ya tsaya ba ya afka ciki yace "Mu je muje da sauri....." Mai adai daita ya ja machine dinsa da sauri don shi ma ya tsorata, Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya ya share xufar fuskarsa ya bude button din riga.
*Haske writers asso*
It's Khaleesat Haiydar
*Noorul Huda*
27.....

Gani yake kamar ba tafiya mai adai daitan yake ba duk da yasan yayi escaping don baxa ma su san inda ya bi ba, yayi tsaki yace "Malam ajiye ni nan dan Allah" Mai adai daitan yayi parking Abuturrab ya fito yace "Sae dai kayi hakuri bani da kudi" daga haka ya yi gaba da sauri, mai adai daitan ya bi sa da kallo, yanxu kawae so yake ya gansa gidan Hajiya Mariya yasan tun da ya fadi ma Mami kamar an je an dauko Samantha an ba iyayenta ne, makullin motarsa dama tun da aka sa shi guardroom Abba ya karbe da wayoyinsa, wani bike ya tsayar yana kallon mutumin dake kai yace "Ehrm Don Allah malam ka goya ni xuwa Kofar Nasarawa idan ba damuwa..." Mutumin yace "Ba can nayi ba, nama kawo gida ka ga inda xan shiga..." Abuturrab yace "Toh don Allah ara min bike din...

Xan dawo maka da shi" wani kallo mutumin ke ma Abuturrab daga sama har kasa baki bude, Abuturrab ya dafa sa yace "Na maka kama da barawo???" Shi dai mutumin kallonsa kawai yake, Abuturrab ya fixge key din yace "Nafi karfin satan machine, kuma i think da wuya a ga barawo Aliyu Haiydar!

Sauka ka ban machine malam" kamar soko haka mutumin ya sauka, Abuturrab ya hau ya tada machine din ya figa da gudu ya hau kan titin, alarm mutumin ya saki bayan Abuturrab ya bace masa yana cewa ya hadu da d'an rufa ido.
Chapter 34 · 0% Book details