← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 123

Sashe 84

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Samha ta kalleta, can tace "Ba abinda nake bukata Ummi" Ummi tace "A'a kar fa ki ji komai beside hakkin ki ne, sadakin ki ne...." Ta girgixa kai kawai jin cikinta na hautsinewa, cike da karfin hali tace "Ba komai Ummi" Ummi da ta lura da yanayinta tace "Are you okay?" Mikewa tayi da sauri tana toshe baki, Ummi ta mike ta kamota ta nufi toilet dake parlon da ita da sauri, kafin ta shiga ta fara kwarara aman a wajen, Ummi na tsaye sai sannu take mata, can ta duka ta riketa ganin ta galabaita, sai da aman ya tsaya mata snn ta dagata suka shiga bayin, ta taimaka mata ta wanke bakinta, ta cire hijab din jikinta ta ajiye cikin bucket dake bayin, jin temperature dinta ya d'an yi sama ta xuba mata ruwa kadan a kanta snn ta ja ta suka fita daga bayin, Samha ta toshe bakinta hade da hancinta don ko da wasa bata son ta kara jin aroman miyan, hakan yasa Ummi ta fitar da ita gaba daya daga gidan, tana rike da ita ganin duk tayi weak ta wuce part dinsu da ita.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
76.....

Yana xaune parlor ya bude laptop knn Ummi tayi sallama suka shigo parlorn, mikewa yyi ya amsa sallaman, Ummi ta xaunar da ita kan kujera tana mata sannu, bata iya ta amsa ba ta kwanta tana mayar da numfashi, Ummi ta kallesa tace "Wani taimakon ka bata?" Ya d'an sosa kai ba tare da ya kalleta ba yace "Mami... nothing yet" tace "To sbda me?" Still bai kalleta ba yace "I just saw the symptoms this morning Mami" Mami na kallonsa tace "Toh yyi, Allah ya kawo mata da sauki, naga bata ci komai ba sai ruwan shayi" yace "She have being sleeping tun da safe, sae da na dawo clinic daxu ma na bata shayin" Ummi ta kalleta ta xauna gefenta tace "Me kike son ci daughter" a hankali ta bude ido tace "Bana jin yunwa Ummi" Ummi tace "A'a you've nt taken anything today, ko a kawo maki shinkafa...." Da sauri tace "A'a..." Ummi tace "Toh me kike so" shiru tayi, sai kuma a hankali tace "Kila tuwo xan ci" Ummi tace "Tuwo?" Ta gyada kai, Ummi tace "Da wani miyar?" Tace "Miyar ganye" mikewa Ummi tayi tace "Toh bari a maki" daga haka ta fita, Abuturrab ya xauna gefenta yana shafa fuskarta yace "Amai kika yi baby?" Kmr xata yi kuka tace "Bana son kamshin miyan" ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Sorry babyna, in'sha Allah baxa mu yi wahala sosai ba" ta kallesa tace "Na mene?" Murmushi yayi ya hade goshinsa da nata, murya can kasa yace "Komai ma" Kauda kanta tayi, ya juyo da fuskarta yace "Baxa ki ce Amin ba wife" kallonsa kawai take don ko magana ma bata son yi, can ta lumshe idanuwanta, yyi murmushi ya koma kan laptop dinsa.

Bayan awa daya Usaina ta shigo parlon da sallama ta gaida Abuturrab snn ta ajiye abincin hannunta ta fita, mikewa yyi ya nufi kitchen ya dauko plate da spoon ya isa inda Samha take tana bacci ya xauna gefenta ya daura hannu fuskarta yace "Baby ga tuwon an kawo maki, tashi ki ci...." A hankali ta bude idanuwanta ya daga ta ta xauna snn ya sauka kasa ya bude warmer din tuwon ya dibar mata ya rufe, kallonta yyi yaga ta jinginar da kanta da kujera ta rufe idonta, ya bude miyan ya dibar mata a kan tuwon da nama snn ya tashi ya xauna kusa da ita yace "Gashi baby" a hankali ta bude idanuwanta, lkci daya ta kauda kai da sauri ta matsa daga gun tana girgixa masa kai tace "Zan yi amai" yace "Miyan da kika ce kina so ne ae dear" taki juyowa sai girgixa masa kai take, ya mike ya dawo kusa da ita tana ido hudu da abincin ta fara yunkurin amai, mikewa yyi ya koma baya, ta fashe da kuka tace "Bana son in ga abincin doctor amai xan yi" daga haka ta tashi ta wuce daki da sauri, ya bi ta da kallo, can ya sauke ajiyar xuciya ya ajiye abincin ya xauna gefen kujera, mikewa yyi ya bi bayanta, durkushe ya ganta cikin bayi ya isa kusa da ita, tana kallonsa da kyar tace "I want to throw up doctor, ya ki xuwa" durkusawa yyi kusa da ita yace "It's because u haven't taken anything wife" ta girgixa kai tace "Baxan iya ba" dagota yyi suka fita daga bayin ya xaunar da ita gefen gado yace "Toh in kawo maki tea xa ki sha?" Kai ta gyada masa ya kwantar da ita yace "Toh ina xuwa" daga haka ya fita ba a dau lkci ba ya dawo rike da cup din tea, ba laifi ta sha tea din kmr daxu snn ta koma ta kwanta.

Tun daga wannan rana Samha tayi bankwana da lafiya, laulayi take me tsanin wanda hakan yasa ya dinga tausayinta ba kadan ba ganin shekarunta, d'an ruwan tea'n da ta ke sha da farko farko shi ma yanxu idan ta sha sai ta amayar gaba daya, bbu abinda take iya ci sai gayan shinkafa shi ma sai an ci sa'a, hakan yasa Ummi ke yi mata kunu shi ma bai fi ta sha sau daya a rana ba, duk ta rame ba kadan ba sai haske, shi kansa ya rame sai ka rantse tare suke ciwon, ko kadan bai son wnn laulayin da take, wani lkcn sai yaji xuciyarsa na urging dinsa kan ya rabata da cikin don wahalan yyi yawa, sosai Ummi ta d'aga masa kafa kan xuwa gun aiki don sai yyi kwana uku bai fita ba, Duk yamma khadija kan shigo tayi share share tayi mopping ta kuma wanke plates idan akwai used ones a kitchen, har bedroom wani lkcn ta kan gyara ta wanke bathroom, lkci lkci kuma Ummi ta kan shigo duba Samha, ita kanta bata jin ddin ynda taga tana wahala sosai, kmr
ko da yaushe yau ma da daddare Ummi ta shigo har bedroom don dubata, can dai ta kalli Abuturrab tace "Anya kana kara mata ruwa tana kuma shan drugs boy, she look so sick?" Yace "Ina dai sa mata ruwan, amma bata yrda ta sha maganin Mami, bn san ynda xan mata ba, alluran ma bata so" Ummi ta kalleta tace "Ki daure ki dinga shan drugs kin ji daughter, hakan xae sa ki dinga jin kwari a jikin ki, ko ba ki son ki samu lfya da wuri?" Samha ta girgixa mata kai kawai, Ummi ta d'an jima dakin kafin ta wuce bayan ta tilastata ta sha kunu ta kuma sha magani, ae ko minti goma Ummi bata yi da tafiya ba duk ta amayo su, kallonta kawai ya tsaya yana yi, can ya mike ya isa kofar bayin ya durkusa a hankali yace "Yanxu wife sai da kika yi aman d'an kunun nan" bata ce masa komai ba kanta a kasa, ya mike ya shiga bayin ya hada mata ruwan wanka, ya taimaka mata tayi snn ya wanke gun aman, duk da uban bargon da ya rufa mata hakan bai hanata rawan sanyi ba, ya dauko wani bargon ya kuma rufa mata ya xauna gefenta yana kallonta, sai da yaga alamar ta fara bacci snn ya mike ya fiddo mata doguwar riga ya dawo ya cire bargon, a hankali ta bude ido tana kallonsa, ya dagota ya sa mata rigar ya rungumeta yana shafa gashin kanta murya can kasa yace "Sorry wife, soon xa ki samu lfya kin ji" a hankali yaji tace "Ina son in kira Abbana" shiru yyi abinda ta fada na d'ad'a sinking a kansa, can yyi karfin halin cewa "Abban ki??" Kai ta gyada masa ya rasa abun ce mata, suna nn a haka har bayan minti kusan goma yaji saukan numfashinta a hankali, lumshe ido yyi ya bude, ya kwantar da ita yana kallonta.

Washegari da misalin goma ya tafi part din Ummi, ya ci sa'an samunta a balcony tana waya, ya xauna ya jira har ta gama sannan ya gaisheta ta amsa tace "Ya mai jikin?" Yana shafa kai yace "Alhmdllh, Mami dama...." Sai kuma yyi shiru, tace "Ya aka yi boy?" Ya kuma shafa kansa yace "Mami i think she's too young to conceive, shi yasa take wahala haka, it's just two month and..." Sai kuma yyi shiru, ta ajiye wayar hannunta tace "Yea she's young, So what's ur opinion in here?" Kallonta yyi a hankali yace "Mami kawai a cire mata, may be some other time...." Ummi na masa wani kallo tace "Really?" Sunkuyar da kai yyi bai ce komai ba, can tace "Never knew u where this stupiddd sai ynxu, to tun da kai kayi halittan dake cikin nata sai ka je ka kashe sa ai, pls get out now" bai iya ya dago kansa ba ya kuma kasa tashi, tace "Bani waje nace Aliyu" da kyar ya bude baki yace "Am sorry Mami, am just confused, bn san wani tunanin xan yi ba kuma..." Tace "In dai ka taba halittan ko da kwaro ne to kaje kayi abinda xuciyar ka ke raya ma" mikewa yyi har lkcn bai dago ba yace "Kiyi hakuri Mami" tace "Foolishness dinka dai xaka ba hakuri" murmushin karfin hali yyi ya juya ya bar gun, ko da ya koma a bathroom ya sameta a durkushe, ya tsaya bakin kofar ya rungume hannayensa yana kallonta, ta juyo da kyar ta kallesa, shiga bayin yyi ya karbi brush din hannunta ya ajiye, kullum da shi take tono ma kanta aman safe, in dai xata yi to sai tayi amai, ya debi ruwa ya xuba gun aman snn ya kama hannunta suka fita, ta kwanta tana mayar da numfashi a hankali tace "Ina son xan yi magana da Abbana"
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
77.....
Chapter 84 · 0% Book details