← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 123

Sashe 27

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

'Ya mace musulma dai da ta taso gidan tarbiya baxata bar gida xuwa makaranta ba hijab ba, ko da kuwa makarantar ba a saka hijab xata sa d'an karami idan ta isa gate ta cire..." Abuturrab da idonsa ke kan titi murya can kasa yace "But mami ae lullubi ba shine abinda xai sa ka gane mutum me addini ba, a xuci....." Tunda ya fara Mami ke masa wani kallo bata bari ya kai aya ba a tsawace tace "Meye hadin ka da yarinyar nan Aliyu, who is she?" Shiru yayi har sai da tace "Baka ji na ne?" A hankali yace "She's just a frnd Mami...." Tsaki tayi ta ci gaba da danna wayarta, bai sake cewa komai ba har ya isa inda xai ajiyeta, yayi parking ya juya yana kallonta yace "Mun kawo Mami" bude motar tayi ta fita tana kallonsa tace "Yaushe xaka koma gida?" Yace "Zan bar clinic karfe hudu" tace "Ohk...." Yace "Xan biyo in dauke ki ne?" Tace "No, kafin lkcn ni na koma gida..." Daga haka tace "Allah ya tsare" sannan ta shiga gidan, ya kusa minti uku kafin ya ja motar jiki a sanyaye ya bar wajen.

Karfe biyar da wani abu yana xaune kofar gida yana danna waya blessing ta xo wucewa, mikewa yayi da sauri ganinta yace "Hello!" Ta juya tana kallonsa sannan tace "Ina yini?" Yace "lafiya lau, plss wait in baki sako ki ba Samantha!" Da sauri ya shiga gida ba a dau lkci ba ya fito rike da takarda a linke ya mika mata tare da dubu daya yace "Ki bata pls" karba tayi tace "xan bata, nagode" daga haka ta wuce, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya xauna.

Samantha ta fito daga wanka bayan magrib blessing ta bude kofar dakinta ta karasa da sauri tace "Sister Rebecca wannan Doctor din yace in baki takardan nan..." Da sauri Samantha ta karba Blessing ta juya ta fice kafin Mumy ta fara nemanta, xaunawa tayi gaban mirror tana goge jikinta tana gamawa ta dauko lotion ta fara shafawa sannan ta dau turarruka fiye da kala biyar ta feshe jikinta da su, sai da ta gama ta dau takardan ta bude, rubutu ta gani kamar haka "ki taho don Allah am waiting for you love...." Ajiye takardar tayi hade da tabe baki ta mike ta dauko kayan baccinta ta saka snn ta tusa gashinta a net, ta kusa minti talatin xaune, can ta mike a hankali ta bude closet dinta ta dauko daya daga hijabs din da take sawa lkcn sanyi ta saka shi har kasa, ta kashe wutan dakinta ta fita, tana waige waige kamar munafuka har ta fita daga gidan.

Ta jima tsaye bakin gate din gidan kafin ta tura a hankali ta shiga ta rufe, bbu kowa parlon ta tsaya bakin kofa tana kare ma ko ina kallo, fitowa yayi daga bedroom, yayi murmushi yana kallonta ya karaso yace "Woaw she came!" Rufe kofar yayi yasa key yace "Welcm love" ta hade rae tace "me yasa kace in xo?" Yace "I just want to see you" turo baki tayi tace "Bude min kofa in wuce...." Wara ido yayi yace "Noo, not until you repeat what you said yesterday...." Juyawa tayi da sauri tace "Noo, plss ka bar ni in wuce..." Murmushi yayi yace "Then ashe xa ki kwana a nan" kamar xata yi kuka tace "Plsss..." Ya daga kafada yace "Ohk let see" daga haka ya tafi three seater yayi kwanciyarsa, ji tayi kamar ta fashe da kuka, wayarsa ya dauka ya jona earpiece ya makala a kunne hade da lumshe ido, ta kusa minti talatin tsaye parlon ganin ya ki cewa komai ta juyo a hankali ta ga har lkcin idonsa a lumshe suke, can ta karasa kusa da shi ta duka tana kallonsa sae ta ga kamar bacci yake, kasa dauke idonta a fuskarsa tayi, can ta cire earpiece daya a hankali ta kai kunne taji karatun Qur'ani yake ji, mayar masa tayi, ta matsa kusa da shi har lkci tana kallonsa, a hankali tace "I...

I said i...

Love you!" Kallon fingers dinsa tayi ta kai hannunta tana kallon Ring din azurfan dake hannunsa har biyu, lumshe ido tayi ta daura lips dinta a hankali, rike hannunta yayi ta sake sa da sauri duk ta daburce xata mike ya ki saketa ya mike xaune.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
21.....

Kin bari su hada ido tayi tana girgixa kai tace "Doctor plss ka sake ni..." Yace "Noo..." Kwankwasa kofa aka yi suka kalli kofar a tare, ta xaro ido tace "Wayyo ka sake ni..." Saketa yyi ya mike yana kallon kofar, ta tashi da sauri tayi hanyar bedroom, karasawa gun kofar yayi yace "Waye?" Muryar Ramla ya ji tace "Ni ce!" Yace "What?" Tace "Abba yana kiran ka wai..." Yace "Alryt ga ni nan xuwa" tace "Toh baxa ka bude ba yaya?" Yace "Yess" tabe baki tayi ta juya ta wuce, juyawa yayi ya shiga bedroom din ya ganta tsaye bakin kofa, tana ganinsa ta juya, ya rungume hannayensa yace "Ashe kina sa Hijab?" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ina wayar da na baki?" A hankali tace "Yana gida!" Ya juyo da ita yana kallon fuskarta yace "ki ajiye shi kusa da ke yau, i will cal you" ta sunkuyar da kanta tace "Toh" yayi murmushi yace "Mu je in raka ki" hanya ya bata ta fita sannan ya fita shi ma, har kusa da gidansu ya rakata yana kallonta yace "Kar kiyi bacci fa, i will call you..." Daga haka ya juya ya wuce ta bi sa da kallo, snn ta nufi gate kamar mara laka ta shiga.

Abuturrab na isa gida ya wuce parlor din Abbansa, Abba dake waya tun shigowarsa ya ajiye bayan ya gama yace "Aliyu!" Abuturrab yace "Na'am..." "Kadai san in ka raina ni to yakumbo ta wuce raini a gun ka koh?" Cewar Abba kenan yana kallonsa, Abuturrab ya sunkuyar da kai ya kasa cewa komai, Abba yace "Tashi ka je...." Ba musu ya mike murya can kasa yace "Kayi hakuri Abba dama..." Kofa Abba ya nuna masa, hakan yasa ya fita kawai, sha biyu saura ya gama abinda xai yi ya rufe laptop snn ya dau wayarsa yayi dialing layinsa dake wayar da ya ba Samantha, tana kwance hannunta rike da hymn book tana dubawa kiran ya shigo wayar dake gefenta, langwabar da kai tayi ta dauka ta yi picking ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Hope baki yi hacci ba?" Tace "Yanxu xan yi..." Yace "Tafi ki wanke idon..." Murmushi tayi ta make kafada kamar yana ganinta, yace "Ina son in maki wani tambaya samha..." Tace "Samantha not samha..." Yace "Noo samha not Samantha.." Tace "Uhm to ina jin ka..." Shirun kusan second ashirin yayi kafin yace "Za ki iya aurena?" Kasa cewa komai tayi sbda mamaki da ya cika ta, yace "I know you re there!" A hankali tace "Aure kuma?" Yace "Yeah.." Ta girgixa kai tace "But ae bbu aure tsakaninmu da kai, our religion differs, am a Christian, you re a muslim..." Yace "Akwai aure tsakaninmu...." Da mamaki tace "How?" Ya shafa kai yace "Sai kiyi addinin ki in yi nawa!" Wani shirun ta kuma yi words dinsa na mata yawo a kai, murya can ciki yace "Samha!" Kasa amsawa tayi, cikin sanyin murya yace "Baki so na kenan..." Jikinta yayi sanyi still ta rasa abun cewa, kiranta ya kuma yi kamar xata yi kuka tace "Ni ban san me xan ce ba..." Yace "Ki ce za ki aure ni" tace "you know that's very impossible, taya hakan xai yiwu bayan addininmu daban daban...." Lumshe ido yayi yace "Nace maki kowa addininsa xai yi, i see nothing wrong with that...." Rasa ma wani tunani xata yi a lkcn tayi, xata iya auren Abuturrab kuwa?

Did she even love him?

She know she so care about him..

Tunanin hakan sai da yasa gabanta faduwa sosai, to in ta yarda xata aure sa Mumy da Abba fa?

Ya relative dinsu xa su dau xancen...

Muryarsa taji yace "Samha!" Hawaye ne ya cika idonta ta kasa amsawa, da dadewa tasan she had alwayz like him, amma bata taba tunanin har xae shigo da xancen aure tsakaninsu ba, a hankali taji yace "Shikenan sai da safe" lkci daya hawayen idonta ya xubo cikin rawar murya tace "Doctor kasan baxai yiwu ba, My parent...

My relatives, my...." Kuka ta fara masa, duk ya rikice yace "Kuka kuma...

Pls stop it now" kasa daina kukan tayi, yace "OMG don nace xan aure ki shi yasa ki kuka, ok am sorry baxan sake ba..." Daga haka ya katse wayar, ya jefar gefensa ya kashe wuta yayi kwanciyarsa, hade kai tayi da gwiwa ta fara kuka, daga karshe ta gaji ta kwanta, kasa bacci tayi daren ranan, maganganun Abuturrab kadai ke mata yawo a ka, sae kusan karfe uku ta samu bacci ya dauketa, Mumy ce ta tasheta karfe takwas da minti sha biyar, ta mike xaune, Mumy tace "Baki tashi kinyi morning devotion din ki ba wnn wani irin bacci kika yi" Kallon idonta Mumy tayi tace "Me ya samu idon ki, kuka kika yi ne?" Samantha ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "kai na ke min ciwo..." Mumy tace "Kai kuma?
Chapter 27 · 0% Book details