← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 123

Sashe 59

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko kafin su isa titi har Anty Maryam ta hau machine, Abuturrab ya bi bayansu, gidan bbu wani nisa, Anty Maryam bata kulasa da shi ba ma ta shige gidan, bbu wata wata tasa ma Samha dake ta juye juye har lkcn Hijab snn ta ja ta suka bar gidan, sosai tayi mamakin ganin Abuturrab, shi dai sadeeq d'an kallo ya xama, Abuturrab ya gaisheta yace "Anty in tafi da ita kawai, let me get her drugs" tana kalle kalle tace "Ina xa ku tafi?" Yace "Ba nisa xa mu yi ba, beside it's nt safe here kinga mum ta gan ni" sake Samha tayi a sanyaye, ya kama hannunta ya bude mata bayan mota ta shiga, Sadeeq ma ya shiga motar daga haka suka bar gun Anty Maryam na kallonsu, daga jiya xuwa yau har ta rame tsabar tension, ko minti uku basu yi da barin wajen ba Machine din Anty Amina da Rachael suka iso gun, xuciyarta ya dinga bugawa har Rachael ta sakko fuskar nn nata shabe shabe da hawaye, ta shako Anty Maryam tace "Maryam yaron da ya dauke Rebecca na gani kofar gidan ki, wato kina da masaniyar inda 'ya ta take kika bari ina ta gantalewa a duniya ko, ashe ke munafuka ce Maryam dama addininku har da munafurci yake koya maku...." Anty Maryam tace "Wani magana kika haka sister, waye kika gani kofar gidana, ce maki yyi wajena ya xo?" Rachael ta fashe da kuka sosai tace "Me nayi maku xaku raba ni da ya ta, idan bae san ki ba me xai xo yi kofar gidan ki" Anty Maryam tace "Yau naga ikon Allah, sister ki yrda ni ko sanin kamaninsa bnyi ba, idan ba dai ko ranan ya fara xuwa ba ko kuma ita tayi masa kwatancen nn....

Ni bn san irinsa ba, taya xan hada kai gun cutar da 'yar d'an uwana Sister, i know nothing about him" Rachael ta dinga rusa kuka tana cewa "Toh kuwa idan ba gizo yyi min ba ni dai na gansa a kofar gida da mota...

Kila da gasken ita tayi masa kwatancen nn din" Anty Amina dai tunda suka sauka ta shige gida ta bar su tsaye, sai gata ta fito da mamaki tace "Maryam bn ganta ba kuma?" Anty Maryam tace "Machine na sa ya kai ta gida, dama yarinyar kawata ce ta xo xata kwana can gidana kuma ina da baki shi yasa na kawo maki ita nan" Ko sanin abinda suke cewa Rachael bata yi ba sai rusa kuka take tana tsine ma Abuturrab, Anty Maryam ta kamo hannunta tace "Kiyi hakuri sister in har dai shine ya xo kofar gidana to wataran xae sake dawowa kilan don ya gan ki ne shi yasa ya koma" da kyar ta ja ta suka bar gun don komawa gida, a xuciyarta kuwa gode ma Allah take da Abuturrab ya wuce da ita.

Lodge din da ya sauka Abuturrab ya nufa, Sadeeq yace "Haba she's in pain mu tafi asibiti mana guy?" Abuturrab yace "She'll be alryt idan Allah ya yrda....." Suna isa hotel din Abuturrab yasa ta fito suka shiga yana rike da hannunta, Sadeeq na biye da su a baya, kwanciya yasa tayi kan gado, Abuturrab ya kalli Sadeeq yace "Mu je in siyo mata magani frnd" Sadeeq yace "Damn it, kai likita ne da xaka ce xaka siyo mata magani kaga yarinya is in pain why baxa a je asibiti ba?" Abuturrab yace "Yea am a doctor i knw what to get her, you don't wrry" mikewa Sadeeq yyi sai kuma yace "Haka to xa a bar ta ita kadai??" Rasa abun cewa Abuturrab yyi, lkci daya yaji wani iri har cikin ransa, can ya dake yace "Ohk ohk, u stay...." Daga haka ya fice ba don hakan da yace ya kai har xuciyarsa ba.

Sadeeq mai shegen tausayi nn ya xauna ya dinga mata sannu, ko kadan bai son ganin mace bata da lfya, ko cikakken minti goma Abuturrab bai yi ba ya dawo, Sadeeq na tambayarsa har ya dawo bai tanka sa ba ya ajiye ledan hannunsa ya durkusa kusa da ita yana kallonta, can ya kalli Sadeeq ya ciro kudi ya mika masa yace "Plss abinci xaka d'an samo mana ta ci kafin in bata magani" mikewa yyi yace "Ohk, am with cash" daga haka ya fita, kafin ya dawo har Abuturrab yasa ta kintsa yayi mata allurorin da xai yi mata, ko da ya shigo bacci take.

Sadeeq ya ajiye abincin hannunsa yace "How is she now?" Abuturrab yace "She's fine" Wayar Sadeeq ne yyi ring, ya fiddo ya ga sabon number ke kiransa, kallon Abuturrab yyi, Abuturrab dake kallonsa shi ma yace "Who?" Sadeeq ya daga kafada xai daga Abuturrab ya taso da sauri ya karbi wayar yana kallon screen, wani mugun faduwa gabansa yyi ganin number Abbansa ne, ya koma ya xauna yace "It's my dad's number" Sadeeq ya xaro ido yace "Haba dai, shud i pick?" Jin Abuturrab bai ce komai ba ya daga kiran ya sa hands free, daga daya side din Abban Abuturrab yace "Abbakar?" Sadeeq ya gyara xama yace "Na'am ina kwana?" Bai amsa gaisuwarsa ba yace "Ka gane me magana kuwa?" Sadeeq yace "A'a ban gane ba" Abba yace "Haba?" Sadeeq ya d'an sosa kai yace "Lah kamar muryar Abban kano!

Sae yanxu na gane" Abba yace "Ina Aliyu, ba shi nasan kuna tare" Abuturrab ya girgiza masa kai da sauri alamar yace baya nn, Sadeeq yace "Abba tun daxu muka rabu yace min sokoto xai je, Abba wllh ban san shine Aliyu ba, i wouldn't have done what i did, i never knew him coincidentally muka hadu a mota daga Enugu xuwa nn kaduna da shi har muka yi exchanging number, Wai ashe...." Katse sa Abba yayi yace "Good, you tell him that ni nace ka gaya masa har ya bar duniya kada ya sake ya bari mu hadu, either by mistake or not, in har ya bari hakan ya faru sai dai wani ba shi ba" Sadeeq dake ta sosa kai yace "Bai kai ga haka ba Abba kayi....." Abba yace "Kai ma idan ka shigo hannuna sai na lahira ya fi ka jin ddi, makaryacin banxaa" katse wayar sadeeq yyi yana yar dariya, Abuturrab kam murmushi yyi, Sadeeq yace "Ai mun saba jin irin haka tun muna yan kanana ko frnd" Aliyu ya daga kafada yace "Sure!" Mikewa Sadeeq yayi yace "Muje daga waje ka ban lbrin how all this happened...

I don't want us to disturb her tunda tana bacci" mikewa Abuturrab yyi suka fita.

A haraban hotel din suka xauna, dai dai lkcn da wayar Abuturrab ya fara ring ya kura ma number ido kafin ya daga ya kai kunne, muryar mijin Anty Maryam yaji yana cewa "Aliyu kar ka shigo unguwar mu yau, ka jira har sai na kira ka kafin ka xo" a hankali Abuturrab yace "Toh" nan da nan ya gano da matsala knn.

Lbrin yanda suka hadu da Samha ya shiga basa tun daga farko, Sadeeq ya xaro ido yana kallonsa jin ba ma musulma bace, Abuturrab dai ya rasa gane me yasa xuciyarsa ya kasa samun nutsuwa sai faduwa gabansa yake, bada lbrin kawai yake amma hankalinsa bai gun, Sadeeq ya lura da hakan yace "Any problem?" Abuturrab ya shafa kansa yace "Am just tired frnd" ko rufe baki bai yi ba wayarsa ya dau ring, da sauri ya daga hade da sallama ganin number Hajiya Mariya, bata amsa sallamar ba tace "Aliyu me kaje yi kaduna kuma?

Kana ina yanxu haka?

Where r you now" bai kai ga bata amsa ba yaji an bude gate din hotel din, duk suka kalli direction din da Sadeeq mota ce guda na soldiers, mikewa suka yi da sauri a tare kmr hadin baki suka kalli junansu, lkci daya duk suka nufi cikin hotel din da sauri, Sadeeq yace "Damn it, damn it.... anyi tracing dinmu" Daki suka shige Abuturrab dake ta furta innalillahi a xuciyarsa ya nufi window da sauri yana lekawa ko akwai wani hanya da xa su bi su fita, Ganin bai ga alamar hanya ba ya koma ya xauna gefen gado ya rike kai yana kiran Allah a xuciyarsa, y is all this happening to him, me yasa abubuwa ke wargaje masa haka, me yasa har ynxu aurensa da Samha yaki yiwuwa, Maminsa ce ta fado masa jikinsa yayi sanyi sosai, may be that's the reason, Sadeeq yace "Haba kar ka karaya soon Aliyu, we will get the hell outta here, ba wanda ya isa ya kamani am nt ready for that now....

I will get a way for us" Wayarsa ya ciro da sauri ya bude ya cire sim ya jefa aljihu yace "Damn this..." don yasan duk ynda aka yi ta haka ma aka yi tracing din nasu, kofa ya bude da sauri ya fita Abuturrab ya bi sa da ido, yea hakkin mahaifiya.
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By khaleesat Haiydar
54......
Chapter 59 · 0% Book details