← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 123

Sashe 106

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Noor da dakin Abuturrab da Anty Maryam bayan tafiyar Ummi, Mami kuma na yi ma yara wanka, Anty Maryam tace "Kin san me Samha" girgixa kai tayi tace "Anty Noor xaki ce min ynxu" Anty Maryam tace "Noor kuma?" Ta gyada kai tace "Um haka su Umma ke kirana" Anty Maryam tace "Sbda me?" Murmushi tayi tace "Sbda am now a muslim" Anty Maryam ta buda ido tace "Kai daughter" tace "Wllh Anty" shiru Anty Maryam tayi tana kallonta can a hankali tace "Toh a wani dalilin kika yrda kika yi converting, in ji ba don Aliyu ba, ba kuma don yaran ki ba?" Girgixa kai Noor tayi tace "A'a, ai lkcn ban haife su ba, har ynxu kuma bbu wanda yasan nayi converting banda su Umma da kika gani daxu" Anty Maryam tace "To su suka ce kiyi converting din?" Tace "A'a i have my reasons" Anty Maryam tace "Toh ko xa ki iya gaya min reasons din" tana son sanin dalilin conversion din nata ne don bata son ya kasance don wani tayi hakan, Noor ta d'an yi murmushi nan ta shiga ba ma Aunt din tata dalilanta na komawa musulunci kmr yanda ta fadi ma Umma, banda Murmushi bbu abinda Anty Maryam take, can ta rungumeta tace "That's it daughter, gwara da kika fahimce hakan da kanki, Muslims are always their brother's keeper, infact ba ma brothers dinsu kadai ba, har wanda addininsu ya sha bam bam in most cases, am happy for you dear, Allah ubangiji ya sa Abbanki ma ya gano hakan da wuri daughter" a hankali Noor tace "Hadda Ummata" murmushi Anty Maryam tayi ta shafa kanta a xuciyarta kuwa cewa tayi da kamar wuya, a fili kuwa tace "Toh Allah ubangiji yasa hakan, na kira Abbanki nace you re back with ur babies, he was very happy, yace anjima da daddare kila ya shigo" Noor da ta ji wani mugun dadi har ranta tace "Anty da gaske xai xo?" Anty Maryam tace "Yace kila" ta girgixa kai tace "Noo plss ya xo don Allah ina son in gansa" Anty Maryam tace "Toh xai xo idan Allah ya yrda, one more thing daughter" Noor ta kalleta tana jiran jin me xata ce, Anty Maryam ta dafata tana kallonta tace "Ke bafulatana ce gaba da baya, a al'adar fulani kuma an san mu da kunya da kauda kai, mijin ki ma bafulatani ne gabansa da baya, kar kuma ki mance gidan surkan ki kike yanxu daughter, abinda nake so da ke bana son ki sake taba yaran nn sai an daukesu an baki su, ko kuma anyi insisting ki dauke su, na lura shegen son yara ke gare ki, kuma ban yi mamaki da yanda kika fito da hakan baro baro ba don haka mamarki ma take" ita dai Noor kallonta kawai take, ta ci gaba tace "Duk kukan da xa su yi idan ba gun ki suke ba bbu ruwanki kin ji daughter, kar a dinga ganin rashin kunyar ki" Sunkuyar da kai tayi cikin sanyin murya tace "Toh" Anty Maryam tayi murmushi ta ja hancinta tace "Yauwa maman biyu" murmushi ita ma tayi ta boye fuskarta jikinta.

Bayan Magrib Noor na xaune dakin ta sa pepper soup din da wata k'awar Mami ta kawo mata gaba ta kasa ci sbda yajin da yyi mata yawa, Hajiya Mariya ma na dakin da Mami suna jera uban kayan twins dake xube kasa kamar baxa su girma ba don kayan da Hajiya Mariya ta siyo masu tare da Abuturrab ma yawan su ba a cewa komai, ta kashe ma Col yafi dubu dari biyu duk a kayan yara, shi dai bai ce mata komai ba ta ajiye atm ta kara gaba, lkci lkci Noor kan kalli yaran da suke kwance kan gado sai motsi suke da ta kallesu kuma maganganun da Anty Maryam tayi mata sai ya fado mata, hakan yasa har suka fara kuka bata yi yunkurin daukarsu ba, sai Hajiya Mariya ce tace "Jariran nn sun cika son hannu naga alama" daga haka ta nufe su, Anty Maryam ce ta shigo dakin da sallama tayi masu sannu da aiki, tana kallon Noor tace "Har ynxu baki gama ba, to rufe ki xi ku gaisa da Abbanki" mikewa tayi da sauri tace "Abbana" Bayi ta shiga da sauri ta wanke hannunta ta fito, ta nufi kofa, Mami da Hajiya Mariya suka bi ta da kallo cike da tausayinta, Anty Maryam kam murmushi tayi ta juya ta bi bayanta, Noor na sauka kasa taga Abbanta xaune parlorn, da Abuturrab da Col, ae bata san lkcn da ta taho da gudu ba ta fada jikinsa tace "Abbana!" murmushi yyi yana kallonta yace "Samantha...." Rungumesa tayi hawaye ya cika idonta tace "I missed you Abbana, i missed you" har lkcn yana murmushi yace "I missed you more daughter" hawaye na sakko mata tace "Abba Mumy fah?" Yace "She is home" tana goge hawayen da yaki tsaya mata tace "I wish i can see her" Abuturrab dai sai kallonsu yake, yaji wani iri har cikin ransa, Col ma dai kallonsu yake shi ma, Hajiya Mariya ce ta shigo parlon rike da Hussain, Ramla kuma na rike da Hassan suka nufo su, yana ganin haka ya janyeta jikinsa, Hajiya Mariya ta mika masa yaron tana murmushi ya karbesa, Ramla ta mika masa dayan ma, kallon yaran kawai yake, can yyi murmushi ya kalli Noor yace "Are you sure babies din ki ne wnn daughter" turo baki tayi tace "Nawa ne fa Abba" ya girgixa kai yace "A'a ba naki bane" tace "Abba wllh nawa ne" yace "Noo" kamar xata yi kuka tace "Da gaske Abba nawa ne" ya ja hancinta yace "You are nt saying the truth" kamar xata yi kuka tace "Am nt lying, they re my babies" yace "Hw will i believe they re urs, gashi ba su yi kama da ke ba?" juyawa Hajiya Mariya kar dariya ya subuce mata, Abuturrab ya sunkuyar da kansa yana murmushi, Hawaye har ya fara cika idonta ta kalli Abuturrab, Col ya d'an yi murmushi shi ma, kuka ta fara yi ta rufe kanta jikin Abbanta, Anty Maryam dai sai kallon ikon Allah take, Hajiya Mariya tace "Ki bar daddy daughter, yaran ki sun yi kama da ke kin ji" Murmushi kawai Abban nata ke yi ya kai bakinsa kunnenta yace "Yea, sun yi kama dake My daughter, they are beautiful just as you, i love them just as i love you...." A hankali ta dago kanta tana d'an murmushi tace "Thanks Abbana," yace "Yea my Samantha" turo baki tayi tace "Abba am nt Samantha any longer" ya d'an bude ido yace "Who are you then?" Lumshe ido tayi tace "Noor..." Yace "Ohh really?

Noorul Islam?" Daga Abuturrab har Abbansa kallonsu kawai suke, ta girgixa kai tace "Rather, *Noorul Huda*" Gyada kai Abbanta ya dinga yi yace "Light of Guidance you mean" ta wara ido ta rungumesa tace "Yes Abba, i want to be just as my grandpa" Murmushi ya dinga yi yace "All the best daughter" Noor ji tayi kamar kada Abbanta ya tafi duk da ya kusa minti talatin a gidan, ana kiran isha yace xai wuce, Dad din Abuturrab ya rakasa suka fita.

Abuturrab sai kallonta yake ganin ynda take hawaye, ta galla masa harara ta mike ta bar parlorn tana share hawayenta, mikewa yyi ya bi bayanta bedroom din Mami xata shiga ya jawota xuwa nasa bedroom din ya rufe kofa ta fashe da kuka, rungumeta yyi yace "Ae tun da kina nan kullum xai dinga xuwa fa wife" lamo tayi jikinsa tana sheshsheka, ya lumshe ido yace "Yaushe kika dawo Noor wife, you re getting me confused" bata ce komai ba, ya ja ta xuwa gefen gado ya xaunar da ita yace "Kin ji dear" tace "Ba ruwan ka" shiru yyi yana kallonta, can ya d'an yi murmushi yana kallon dogon hancinta yace "Ohk" hannu ya kai hancin nata yace "Ta nn kadai twins suka maki kara, ba don kuma nima nawa bashi da kyau ba....

Amma bakinsu, idonsu, fuskarsu, infact komai nasu nawa ne" yana magana ne yana mata wani irin kallo, ta tabe baki irin kan ka ake ji din nan, dariya yyi ya rungumeta yana kiss din wuyarta yace "There is always reason for everything baby" lumshe ido tayi bata ce komai ba.
Chapter 106 · 0% Book details