← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 123

Sashe 112

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari da sassafe Ummi ta gama shirinta ta sa fatima ma ta shirya ta dau jaka tana kallon Mami tace "Toh Hajiya xa mu koma garin mu sae mun yi waya, Allah ya raya Ahmad da Abbakar" Mami tayi murmushi tace "Irin wnn sammako haka, ko duk maganar jiya ce" Ummi tace "Haba ko daya, ina son isa da wuri ne don inje clinic" Mami ta mike tace "Toh shknn Hajiya, mun gode kwarai Allah ya kara dankon xumunci" Ummi tace "Ameen" Naman suna me yawa Mami ta tula mata da drinks sai snacks tace ta kai ma su Rabi'a, A parlor Ummi tasa aka kira mata Abuturrab, ya sakko ganinta yace "Mami har xaku wuce da safe haka" tace "Eh ina son mu isa da wuri ne, sai ka turo babban mota a kwashe maku kayan ku na can ko boy" ya d'an shafa kai yace "Toh Mami, bari in kirata ku yi sallama" tace "A'a bar ta kace mata mun tafi kawai," a hankali yace "Toh ina xuwa Mami" daga haka ya tafi daki ya dauko makullin motarsa don ta taho masa da motar tasa daga can gombe, tare da Hajiya Mariya suka tafi kai su park, ya ba Fatima dubu ashirin taki karba, dole Hajiya Mariya ta tilastata ta karba tace ta gode, yana kallon Ummi yace "Nagode Mamina sai mun xo kawo maki xiyara in sha Allah, ki gayar min da kanwata khadija" tace "Toh ina xuba ido boy, ga dai Samha nan amana, idan ka ci amana kuma kai ma kasan sauran Aliyu, Allah raya maka boys dinka a tafarkin islam" cikin sanyin murya yace "Ameen Mami" tace "One more thing Aliyu, you re educated, you knw what's right from wrong...

This is all i have to tell you ka xama me aiki da hankalin ka" daga haka ta shiga mota ta ce "Toh Hajiya Mariya sai mun yi waya, Allahu ya bar xumuncin mu" basu tafi ba sai da suka ga motar ya tashi snn suka dau hanyar gida, Abuturrab na driving ya kalli Hajiya Mariya da har lkcn bata da walwala yace "Mum wani abu ya faru ne, ur mood isn't encouraging" sai a snn ta kallesa tace "Tunda wnn fitinannar Uwar taka ta xo meye ma baxai faru ba, mata bata da aiki sai hada fitina, kaga xan kira Alhaji, (wato mijinta knn) in nema maka alfarma ya baka gidansa daya dake hotoro ku koma can da xama a yau Aliyu....

Yayar babanka ba da alkhairi ta xo ba gaskiya, naga kuma kamar Mami na neman biye mata ne" Abuturrab ya d'an yi shiru, sai can yace "Cewa take sai na kara aure koh?" Hajiya Mariya tace "Ta gaya maka kenan?" Gyada kai yyi yace "Eh, ta fadi hakan gaban Samha ma" Hajiya Mariya ta girgixa kai tace "Muna komawa gida ynxu ku fara shiri, dama Col ba son xamanka yake a gidan ba naga alama, ku koma hotoro kawai, but before then xaka bar su a gidana su yi arba'in" yace "Mum to gidana fa?" Tace "Aa bn san col ya san inda kake ma" Bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, yana biye da ita a baya suka shiga parlor, xaunawa yyi a parlorn ya gaida Anty Maryam ta amsa, ya jawo Ihsan yace "Anty amma xaki bar mana ihsan koh" dariya kawai tayi tace "Lallai kam, xuwa anjima xa mu wuce" yace "Da wuri haka Anty" tace "Shekaranjiya na xo ai" yace "Toh Allah kai mu Anty" tace "Ameen" ya mike yana murmushi yace "Da gaske fa Anty xa ki bar min ihsaan" murmushi kawai tayi ya nufi stairs, bedroom dinsa ya shiga, ganin Noor bata dakin ya fito ya shiga dakin Maminsa, Yakumbo ya tarar tana ma Abubakar wanka, Mami na xaune rike da Ahmad, Ya xauna gefen gado yace "Ina kwana Umma" tace "Lafiya lau, sai yanxu?" kallon Mami yyi ita ma ya gaida ta, Ta amsa tace "Har sun wuce" Yace "Eh sun wuce" mikewa yyi ya fita daga dakin ya koma nasa, xama yyi yana tunanin maganganun Hajiya Mariya, can ya sauke ajiyar xuciya ya mike ya shiga bathroom don yin wanka, ko da ya fito daga wanka, xaune ya tadda Noor a can karshen gado a shirye cikin riga da skirt, ga breakfast da aka ajiye mata kan rug, ya ajiye karamar towel din hannunsa ya karasa kusa da ita yace "My wife" bata ce komai ba ya kalli abincin dake kasa yace "Toh sauka ki yi breakfast mana dear" nan ma tayi shiru, ya dago kanta yana kallon kwayar idonta yace "Tell me, wani abu ya faru ne" hawaye ya gani cikin idon, cikin Sanyin murya yace "Wife...." Still bata ce komai ba, a hankali yace "Ni bn san meyasa closeness din mu ya ja baya ba Samha, we were nt like this before, it's getting worst now, baki son amsa ni idan na maki magana, you derive pleasure ignoring me always....

I don't just knw what came over you" mikewa yyi ya dau towel dinsa ya koma can daya side din ya xauna, can ya tashi ya fara shiryawa har ya gama bata dago kanta ba, kofa ya nufa ya fita daga dakin, kuka ta fara a hankali, tayi me isarta snn ta sakko kasa, dai dai shigowar Yakumbo, ta kwantar da yaron hannunta tace "Ynxu 'yar nn barin abincin kika yi ya sandare" girgixa kai kawai Noor tayi, tace "Toh maza ki gama ki basu abinci su ma don yunwa suke ji" a hankali tace "Toh" yakumbo ta fita, Hajiya Mariya ce ta shigo da Sadeeq ta kwantar da shi gefen d'an uwansa tana kallon Noor tace "Idan kin gama sai ki yi breastfeeding dinsu kin ji Daughter" Noor tace "Toh" ita ma ta fita dakin, Tea kawai ta hada ta sha don ji tayi baxata iya cin komai ba, can ta mike ta koma kan gadon ta kwanta gefen yaron tana kallonsu.

Karfe sha biyu saura Anty Maryam ta wuce, Col da kansa ya bata 20k kudin mota, Mami kuma ta ba Ihsaan atamfa guda Uku cikin wanda twins suka samu na suna, Hajiya Mariya da Abuturrab ne suka kai ta park, tun da suka bar gidan Noor ke kuka a daki, ta rasa dalilin kukan nata.

Abuturrab na dawowa Ilham ta tare sa a parlor wai Abba na kiransa, ya d'an yi jim yana kallon Hajiya Mariya dake kallon ilham ita ma, can tace "Yakumbo na parlorn ne?" Ilham tace "Eh tana ciki" tsaki Hajiya Mariya tayi ta wuce sama, Abuturrab ya nufi parlon Abbansa, a hankali ya tura kofar ya shiga da sallama, xaunawa yyi kasa yana kallon Col yace "Ga ni Abba" Col ya kallesa yace "Na gan ka" D'an murmushi yyi ya sunkuyar da kai, Yakumbo tace "Atoh, ba wani abu bane dama batu ne da xai xame maka alkhairi nn gaba, kaga dai ni Fatima baxan so abinda xai cutar da kai ba Ali, kai ba ma hka ba, ni ta wa ennan yara biyu nake baxan so su halaka ba, haka kurum rana tsaka ka dau kirista wacce ba muharramar ka ba ka lula duniya da ita, kayi ta ba Ahmad wahalan neman ka, ni ma kasa nayi ta shiga da fita ina neman a karkato min da hankalinka ka dawo gida, to ni duk wnn bai wani dame ni ba, abinda yafi damuna shi ne Hajarah da Mariya sun san komai suka dinga munafurtar mu ashe su suka xuga ka kayi abinda kayi ma, kuma sun san inda kke, to ba wnn ba ma, babban tashin hankalin shine ynda ka kai yarinya masallaci aka daura maku aure kaje kana rayuwa da ita hankali kwance ga ka tatattcen mara ji koh? to dai wllh kullum kayi ta addu'a Allah ya yafe maka mahaifin ka ya yafe maka ni ma in yafe maka, idan ba haka ba wllh tarihi sai ya maimaita kansa, kana ji kana gani yar ka mace xata bi kato su gudu da sunan so, to don Allah wa ka cuta idan ba mu ba?" Sai a snn Abuturrab ya dago yana kallonta, Tace "Atoh, ba xancen ka harareni bane gaskiya ce na fada, ba haka kayi ma yar mutane ba, to kaji tsoron Allah kar kai ma ayi ma yar ka, kaga ko mu ma mun shiga uku ba kai kadai ba, to ni duk ba ma wnn ba, wai sai gashi da ka tashi dawowa sai ka dawo mana da yan biyu, wai kirista ta haife su, to ynxu abun tambaya a nn Aliyu shine, waye xae ba yaran nn tarbiya irin ta koyarwar islama?" Bbu yabo bbu fallasa yace "Uwarsu!" Yakumbo tace "Yau naga abinda ya ishe ni bai ishi Allah ba, wace uwar ta su?
Chapter 112 · 0% Book details