← Book details Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 123

Sashe 39

Noorul Huda Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jesus acted like we muslims do, he fall with his face to the ground, but never dance, clap, or beat drum as an act of worship, did he?" Ya tambaya yana kallonta, ya girgixa kai yana murmushi yace "He never, let me add a prove to this, Matthew 26:29 read thus 'Going a little further, he fell with his face to the ground and prayed......" Murmushi yayi yace "you see, ba ace he clapped his hands, beat drum or danced ba, even till date the Coptic Christians still pray the way Jesus PBUH did, the jews in the holy land still pray the same way also!" mikewa tayi ta bar masa wajen ta koma kan katifar dakin tayi kwanciyarta hade da lumshe ido, murmushi yyi ya mike ya fice waje.

Mami ce xaune parlor ta rafka uban tagumi, Hajiya Mariya ma na xaune gefen yayartata, sai Yakumbo dake tsaye kekam bakin nan uwa an taka teba a kan titi ta jefa ma Mami harara yayi sau ashirin a wajen, manyan 'ya yanta maza duk biyun na parlorn, sai Abba dake tsaye shima kamar dai the soldier he is, sojoji ne har biyu tsaye bakin kofa, ya juya ya kuma kallon Mami strictly yace "For the last time ki gaya min inda Aliyu yake...." buda baki tayi cike da bacin rai tace "Kai kana matsayin mahaifinsa baka san inda yake ba sae ni, ta ina xan san inda Aliyu ya tafi, haba a dinga adalci mana" a fusace yakumbo tace "Yo idan bai tambaye ki Aliyu ba uwar wa xae tambaya?? ba boyayyen abu bane kowa yasan bakin ku daya da d'an iskan, ni ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba kinsan inda Aliyu yake...." Sae kuma ta fashe da kuka tace "Tur!!

Mu dai duk xuri'ar mu daga farkonta har ixuwa yanxu bbu crista, ko tu6a66e, ban dai san a naku yanda abun yake ba...." Mariya tace "Mu ma haka, hasalima iyayen mu da kakannin mu duk malamai ne..." Yakumbo ta jefa mata wani matsiyacin kallo tace "keee kar ki min fitsara ban sako da ke ba daga tambaya?" Ko kallonta Mariya bata yi ba, Abba ya girgixa kai yana murmushin takaici yace "Hajarah duk abinda Aliyu ya xama kece sanadi, ke ce sila...".

Mikewa Mami tayi tana murmushi tace "Sae yau ka sani kenan, ae tun da na nema masa karatu a Uk na biya, na kama masa gida mai tsada, na xuba masa abubuwan more rayuwa, naki sauraran shawarar kowa ni da 'yan uwana nace ae namiji ne shi ba mace ba, na rufe ido ban ji ban gani na hada masa kaya na kai sa Airport ya tafi can yayi rayuwarsa in a free way, bbu sa wa bbu hanawa shekaru d'aid'ai har takwas, What did you expect Col???" Daga haka ta nufi stairs Hajiya Mariya ta bi bayanta, kasa cewa komai Abba yayi ya bi ta da ido, yakumbo ta tafe hannu tana salati tace "Wato mu matar nan ke gaya ma magana koh?"
*Haske writers asso*
*Noorul Huda*
By Khaleesat Haiydar
31.....

Alhaji Umar ya saci kallon Abba da uwarsa bai dai ce komai ba haka d'an uwansa Alhaji Jibril, juyawa Abba yayi kamar xae tashi ya fice daga parlon, Alhaji jibril ya ce "Toh Allah ya kyauta, Allah ya kawo mafita yasa ya gane abinda yake shirin yi" Yakumbo ta fashe da wani kuka tace "Ae ni Allah ya isa tsakaninmu da Aliyu, wnn abun kunyar da me yayi kama da wani ido xa mu kalli 'yan adawan mu, me ya burgesa game da crista arniya, ni dai ina ganin jarabawa, Aliyu ya cucemu, yaro kamar shaidan, duk artabun da aka dinga yi jiya ace ba a kamasa ba har ya gudu ko ina ya tafi..." A bangaren mumy kuwa tun daga jiya har yau kuka ne ya xamto abincin ta da ruwanta, tayi kukan tayi xage xagen, tayi iface ifacen, banda bata hakuri bbu abinda yan uwa da abokan arxiki suke, har cewa tayi da ta sani tun daren shekaranjiya ta kashe samantha tasan ba ita a duniyar ne kawai da ace ta bi musulmi sun gudu, gidan nasu cike yake da members din Church dinsu, mata da maxa, pastors har daga kaduna da Abuja sae da suka xo, masu addu'a nayi, masu xirga xirga da Abban samantha xuwa gidansu Abuturrab nayi, da ace Dad din Abuturrab ba babban soldier bane da ya shiga uku don ba abu me kyau bane xae biyo bayan irin sintirin da suke fiye da su ashirin har da matasa, daga karshe tsawa yayi masu yace "Su je duk inda xa su su nemi Aliyu su kashe sa ya basu go ahead, kada wanda ya kara d'aga masa hankali tunda basa ganin kokarinsa, bbu yanda suka iya ga gida cike da sojoji, haka suka juya sumui sumui suka fita.

Abuturrab na xaune tsakar gida suna labari hira da Abba bayan la'asar, Alto bata kuma cewa a ta da Samantha tayi sllh ba a tunaninta bata da tsarki ne, Binta na xaune tana sirfa gero sai dai duk motsin da idonta xae yi a kan Abuturrab yake sauka, yana lura da irin kallon da take masa, sae abun ya basa dariya ya dai ci gaba da hirarsa da Alto, Samantha ce ta fito ta nufi bandaki da sauri ta fara amai tun kan ta isa, mikewa Abuturrab yayi haka Alto da Hansae dake wanke wanke suka dings cewa subhanallahi, Abuturrab ya d'agota a rikice yace "Meya faru?" Ta fashe masa da kuka tana rike da cikinta tace "Ciwo yake min" Hansae ta kawo ruwa a buta tace "Ikon Allah to bara in jika ma sa6ara" Abuturrab ya karbi ruwan ya wanke mata fuskarta snn ta shiga da ita ciki.

Kwanciya tayi ya xauna gefenta yace "It's ur period right?" Juyawa tayi bata ce komai ba, ya mike ya fita, Tsaye ya ga Hansai har ta jika maganin da tace, yayi murmushi yace "Ae baxa ta sha ba Baaba, bbu gun sayar da magani nan ne?" Alto yace "Kai da tafiya sosai, Binta ta raka ka gun da xaka samu babur ka hau, sae kayi kamar xaka shiga Gombe...." Abuturrab ya durkusa yace "ohh daga kauyen nan sae gombe?" Alto yace "A'a akwai kauyuka har uku a gaba..." Abuturrab ya mike yace "Toh shknn bari in je..." Tuni Binta ta dauraye hannunta tace "Mu tafi..." Ya kalleta yace "Ae na gane hanya yanxu, da kin yi xaman ki" Tace "Yo ae baka san inda xaka samu babur ba" Hansae tace "Gaskiya ne, bari ta rakaka gun sai ta juyo" toh kawai yace suka fita gidan, tun da suka fita Binta ke xuba bai kalleta ba bare ya tanka ta ba, tafiyarsa kawai yake, har suka isa inda babur uku suke sbda masu fita kauyen, duk machine din sun rube, Binta tace "Bako ne daga birni wae wajen kauyen nan xaku fitar da shi xae siya magani" Bata rufe baki ba ko wanne ya dinga cewa ya hau, na gabansa ya hau mutumin ya tada machine din, ya d'an kalleta yace "Sae na dawo" daga haka yace ma mai machine din su tafi.

Sae kusan karfe shidda Abuturrab ya dawo rike da leda, Alto dake kade shanayensa a waje yace "Ka dawo?" Abuturrab yace "Ehh na dawo Baffa sannu da aiki" Alto yace "Ka dai samo maganin koh?" Kai Abuturrab ya gyada masa yace "Na samo" daga haka ya shiga, Binta kadae ce tsakar gida tana kwasan tuwo, ta washe baki tace "Har ka dawo Aliyu?" Kallonta yayi don sae da tasa Mami ta fado masa, ta fi kowa kiransa da Aliyu, yace "Na dawo!

Bbu kowa dakin?" Tace "Ehh ita kadai ce" ya duka ya shiga Bukkar, xaune ya ganta ta hade kai da gwiwa, ya karasa a sanyaye ya ajiye ledan hannunsa ya d'agota yace "Samha!" Ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja, cikin sanyin murya yace "Kuka kike?" Sauke idonta tayi ya kamo hannunta yace "Am making you suffer koh, i know you re not use to all this Samha....

But for the sake of my love endure it for just a while..." Ta fashe da kuka tace "Am not complaining" gefenta ya dawo ya xauna ya jawota jikinsa yace "Bance kina complain ba, but you re not use to this such of life..." Bata ce komai ba yace "Kin fara period din ne?" Ta girgixa masa kai, yace "But it's on it way koh?" Shiru tayi bata ce komai ba, ya dago kanta yace "Shareni ma kika yi" kwace kanta tayi tace "How did you know?" Yayi murmushi ya daura kansa a kafadanta yace "I know because i am a doctor...." Tayi masa wani kallo ta gefen ido tace "Ko dai sa ido, kawai don ka ga na yi amai?" Kamar xata yi kuka ta kare maganar, dariya yayi ya kai bakinsa kunnenta yace "Ni din, toh shknn in ma ya xo ya fara wahalar min da ke ko kallonku baxan yi ba, ya gama wujijjiga ki ya xuba abinsa ya wuce" murmushi tayi ta boye fuskarta a jikinsa, lkci daya Binta ta fado dakin, da sauri ya saketa ita ma ta ja baya, Binta na ganin haka ita ma da sauri ta fita, Ya kalli Samantha yaga ta wani hade rai, bai ce komai ba ya dau ledan da ya kawo ya bude, pad leda biyu sae inner wears da allurori da drugs, perfume, Toothpaste, brush soap da sponge sai gown har biyu da veil ya xube mata su gabanta, ta dauke kai bata ce komai ba, Ya bude daya ledan ya fiddo ledojin kaji biyu ya ajiye mata daya ya ajiye dayan a gefe, sae kuma Bread biyu da Blue band daya da ya siyo da kayan tea sae table water babba, mikewa yayi ya dau ledan kaza da daya bread din ya fita don kai ma su Binta.
Chapter 39 · 0% Book details